Maduro Ya Bayyana Sakataren Harkokin Wajen Amurka Da Cewa Wawa Ne
Published: 29th, March 2025 GMT
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da yake ziyarar aiki a kasar Guyana da cewa, sakarai ne.
A yayin ziyarar da sakataren na harkokin wajen Amurka ya kai zuwa kasar Guyana mai makwabtaka da Venezuela, ya ce, Amurka za ta mayar da martani mai karfi akan Venezuela idan har ta kai wa Guyanan hari.
Rubio ya kara da cewa; Idan haka ta faru, to kuwa Venezuela za ta gwammace kida da karatu a wannan rana.
Amurkan dai ta kulla yarjejeniyar tsaro da kasar ta Guyana a yayin ziyarar da Rubio ya kai.
Shi kuwa shugaban kasar ta Venezuela da yake mayar da martani ya ce; Marco Rubio wawa, ya zo yana yi wa kasar Venezuela barazana daga kasar Guyana, sannan ya kara da cewa; Venezuela ta fi karfin a yi mata barazana, domin ita kasa ce ta ‘yanci.”
Alaka a tsakanin Venezuela ta Amurka ta sake tabarbarewa tun bayan da shugaba Donald Trump ya hau karagar mulki, bayan da ya kara kakaba mata takunkumai, da kuma batun mayar da ‘yan hijirar kasar daga Amurka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
Gwamnatin Amurka ƙarƙashin Donald Trump ta sake sanya Najeriya cikin jerin “Ƙasashe Masu Matsala ta Musamman” saboda zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.
Wannan zargi ya biyo bayan jawabin da Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya yi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a kwanan baya.
Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDPA lokacin taron Shettima ya bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin abin tausayawa, inda ya hi kira da a tabbatar da zaman lafiya ta hanyar kafa ƙasashe biyu masu zaman kansu.
Bayan jawabin nasa, wasu ƙungiyoyi suka fara yaɗa labarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya, duk da cewa mutane da dama sun ƙaryata jita-jitar.
A ranar Juma’a, Trump ya wallafa wani rubutu a shafinsa na X, cewa Kiristoci na fuskantar barazana a Najeriya.
Ya yi iƙirarin cewar masu tsattsauran ra’ayi suna yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya .
Ya umarci ɗan Majalisar Amurka, Riley Moore da shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar, Tom Cole, su binciki lamarin, sannan su gabatar masa da rahoto.
Shugaban ya ƙara da cewa ƙasarsa ba za ta zuba ido yayin da irin wannan “ta’addanci” ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashe ba.
Ya lashi takobin cewar Amurka za ta ci gaba da kare Kiristoci a duniya baki ɗaya.
Bayan wannan furuci, wasu sun zargi Trump da amfani da matsalar tsaron Najeriya don samun goyon bayan siyasa.
Har yanzu Gwamnatin Najeriya ba ta yi martani a kan lamarin ba, amma jami’an gwamnati a baya sun bayyana cewa rikice-rikicen da ake fama da su a ƙasar suna da nasaba da ayyukan ta’addanci, fashi, da rikicin ƙabilanci, ba addini ba.
Kalmar “Ƙasa Mai Matsala Ta Musamman” na nufin ƙasashen da Amurka ke ganin suna take haƙƙin ’yancin addini, kuma hakan na iya sa wa ta ƙaƙaba wa Najeriya takunkumai.
Idan ba a manta Najeriya ta fara shiga jerin irin waɗanda ƙasashe tun a shekarar 2020.