An Fitar Da “Takardar Ci Gaban Sha’anin Hakkin Dan Adam A Xizang A Sabon Zamani”
Published: 29th, March 2025 GMT
A yammacin yau Juma’a ne ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai a birnin Lhasa na jihar Xizang wato Tibet, inda aka fitar da “Takardar bayanin ci gaban sha’anin kare hakkin dan Adam a Tibet a sabon zamani”.
Takardar ta yi nuni da cewa, a ko da yaushe, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar suna mai da hankali kan ayyukan da suka shafi Xizang, kuma suna ci gaba da kyautatawa da raya tsarin mulkin Xizang, da daukar matakai masu inganci don raya tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama’a, da kawo alheri ga jama’a, da inganta hadin kai da ci gaban kabilu, da kuma kare hakkin dan Adam na dukkan kabilun jihar Xizang.
Ta kara da cewa, a halin yanzu, jihar Xizang ta samu kwanciyar hankali a bangaren siyasa, da hadin kan kabilu, da bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’umma, lamarin da ya haifar da wani abin al’ajabi na kare hakkin dan Adam a tudun dusar kankara.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar Sin ya gudanar da taron manema labarai da misalin karfe 10 na safiyar yau Litinin, inda kakakin hukumar kididdiga ta kasar, kuma babban masanin tattalin arziki, kana daraktan sashen kididdigar tattalin arziki na kasar, Fu Linghui ya yi karin haske kan ayyukan tattalin arzikin kasar cikin watan Agustan bana, tare da amsa tambayoyin manema labarai.
A cewar bayanan da aka gabatar a yayin taron, ayyukan tattalin arzikin kasar a watan Agusta sun samu ci gaba ba tare da tangarda ba. Kuma hakan ya bayyana ne ta hanyoyi daban-daban kamar haka: masana’antu sun habaka cikin sauri, masana’antar kera kayayyakin aiki da masana’antar fasaha sun samu ci gaba mai kyau. Kana ayyukan bayar da hidima su ma sun bunkasa cikin sauri. Baya ga haka, an samu ci gaba mai kyau a bangaren bayar da hidimomi na zamani. Harkokin kasuwanci sun samu ci gaba cikin natsuwa, inda harkokin sayar da kayayyaki ga masu sayayya suka kara habaka. Har ila yau, kadarorin jari sun ci gaba da karuwa, jarin masana’antu ya habaka cikin sauri, harkokin fice da shigen kayayyaki sun ci gaba da girma, tsarin kasuwanci ya ci gaba da ingantuwa, kana yanayin samar da guraben aikin yi, ya kasance kan wani mataki mai daidaito. Sai dai kuma saboda yanayin da ake ciki, adadin marasa aikin yi a birane ya karu, ma’aunin Core CPI ya ci gaba da hauhawa, kana faduwar farashin kayayyakin masana’antu ya ragu.
Bayanan sun kara da cewa, akwai bukatar lura da cewa, ana fuskantar yanayin rashin tabbas a waje, kuma tattalin arzikin kasar Sin yana fuskantar kalubale da hadari da yawa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp