Abubuwan da suka sa Fafaroma Francis ya yi fice a duniya
Published: 21st, April 2025 GMT
Da safiyar wannan Litin fadar Vatican ta sanar cewa da misalin ƙarfe 7.35 Agogon Vatican Fafaroma Francis, wanda sunansa na asali Cardinal Jorge Mario Bergoglio, ya rasu a yayin da al’ummar Kirista na duniya ke bikin Ista.
Ya mutu ne washegari da ya fito bainar jama’a a Dandalin St Peter’s, domin taya Kiristoci murnar zagayowar ranar Ista.
Fafaroma Francis ya yi fama da doguwar jinya, inda a watan da ya gabata ne aka sallame daga asibiti bayan ya shafe makonni biyar can sakamakon cutar sanyin haƙarƙari mai tsanani.
Ga wasu abubuwa da Fafaroman ya yi fice a kansu:
1. Nuna adawa a fili ga wasu manufofin Donald Trump.Ya yi Allah wadai da yunƙurin Trump a mulkinsa na farko na gina katanga tsakanin Amurka da ƙasar Mexico, inda ya ce hakan ba ɗabi’ar Kiristoci ba ce.
Ya kuma yi Allah wadai da shirin maida baƙi ƙasashensu, da gwamnatin Trump ke ƙoƙarin yi a mulkinsa na biyu.
2. Sumbatar ƙafafuwan fursunoni.Fafaroma Francis ya wanke tafin ƙafafuwan wasu fursunonin gidan yarin Rome, tare da sunbata, abun da ya ja hankalin duniya.
3. Kira a magance matsalar sauyin yanayi.Fafaroma Francis ya zargi manyan ƙasashen duniya da ƙin ɗaukar matakan kare muhalli da sauyin yanayi, inda a 2023 ya ce wasu matsalolin ba za su taɓa gyaruwa ba.
4. Jawo masu ɗabi’ar auren jinsi a jiki.Duk da kakkausan suka da ya sha, wasu na ganin yana da ƙoƙarin jawo masu raunin imani a jiki, ciki kuwa har da yarda da ya yi ake sanya albarka ga auren jinsi.
5. Shi ne Fafaroma na 266, kuma na farko daga nahiyar Arewa da Kudancin Amurka.Asalin iyayensa ’yan Italiya ne, da suka yi ƙaura zuwa ƙasar Argentina. An haife shi a Buenos Aires, ranar 17 ga watan Disamba, 1936.
6. Kakkausar suka ga kamfanonin ƙera makamai.Ya yi kira ga ƙasashen duniya da su rungumi masalaha wajen magance rigingimu, gudun kada rikice-rikice su haifar da Yaƙin Duniya na 3.
7. Alaƙanta kwararar ’yan ci-rani zuwa Turai, da tauye ci-gaban ƙananan ƙasashe.Ziyararsa ta farko, Francis ya je tsibirin Lampedusa, yankin da ’yan ci-rani suke bi wajen shiga nahiyar Turai, inda ya ɗora laifi kan yadda ake tauye ci-gaban ƙananan ƙasashen duniya.
8. Yana son ƙwallon ƙafa da kuma waƙe-waƙe.Francis shi ne Fafaroma da yafi mu’amala da matasa, wajen sauraron su, da kuma ƙaunarsa da ƙwallon ƙafa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fafaroma Fafaroma Francis Fafaroma Francis ya
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Amurka Trump Ya Bukaci Gurfanar Da Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama A gaban Kuliya
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi tsohon shugaban kasar Barack Obama da cin amanar kasa tare da yin kira da a yi masa shari’a
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi magabacinsa, Barack Obama da cin amanar kasa, inda ya bukaci a gurfanar da shi a gaban kuliya kan wani rahoton sirri da ya nuna cewa; Jami’an gwamnatin Obama sun murguda bayanai game da katsalandan din Rasha a zaben Amurka na shekara ta 2016.
Kalaman na Trump sun zo ne yayin wani taron manema labarai a ofishin Oval, wanda shugaban kasar Philippines Ferdinand Marcos ya halarta. Yana cewa:”Bisa ga abin da ya karanta…tsohon shugaba Obama ne ya fara wannan badakalar,” ya kara da cewa Obama shi ne “shugaba” na abin da ya bayyana a matsayin “gungun maciya amana.”
An karfafa wadannan zarge-zarge ne bayan da Daraktar hukumar leken asirin kasar Tulsi Gabbard ta aike da masu gabatar da kara ga ma’aikatar shari’a dangane da wani rahoto da aka fitar a ranar Juma’ar da ta gabata da ke tabbatar da cewa jami’an gwamnatin Obama na da hannu wajen kirkirar bayanan sirri da nufin share fagen juyin mulki na tsawon shekara daya kan shugaba Trump.