Gharibabadi : inganta sinadarin uranium jan layi ne a tattaunawar Iran da Amurka
Published: 21st, April 2025 GMT
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa tace uranium din ta tamakar jan layi ne a tattaunawar dake wakana tsakaninta da Amurka.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar ne Kazem Gharibabadi ya bayyana hakan, inda ya ce hakkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne inganta sinadarin Uranium, yana mai jaddada cewa, wannan batu a matsayin jan layi a tattaunawar da Amurka.
Mista Gharibabadi ya bayyana haka ne a yayin taron kwamitin majalisar dokoki kan tsaron kasar da manufofin ketare, inda ya yi wa ‘yan majalisar bayani kan shawarwari zagaye na biyu tsakanin Tehran da Washington, wanda ya gudana a Rome, babban birnin kasar Italiya.
Jami’in na iran ya kara da cewa tawagar kasar ta jaddada matsayinta na cewa Iran ba ta neman kera makaman kare dangi, inda ya bayyana cewa ayyukan nukiliyar Iran na zaman lafiya ne gaba daya.
Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya kuma jaddada cewa, daya daga cikin manyan makasudin shawarwarin shi ne cimma nasarar dage takunkumin da aka sanya wa iran gaba daya da suka hada da na majalisar dokokin Amurka da kuma umarnin zartarwar takunkuman matsin lamba da shugaba Donald Trump ya sanya wa hannu.
Kawo yanzu AMurka da Iran sun gudanar da shawarwari har guda biyu ka batun shirin nukiliyar kasar ta Iran, kuma dukkan bagarorin sun bayyana tattaunawar da mai kyakyawan fata.
A ranar Asabar mai zuwa bagarorin zasu sake ganawa a karo na uku, bayan wacce sukayi a Oman da kuma Italiya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a tattaunawar
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Yi Kiran Cewa; Ina Masu Fafatukar Kare Hakkin Dan Adam Suke A Bala’in Gaza?
Shugaban kasar Iran ya yi kiran cewa: Ina masu fafutukar kare hakkin bil’adama suke a bala’in Gaza?
Shugaban kasar Iran Dr. Masoud Pezeshkian ya jaddada muhimmancin sauya salon tafiyar da gwamnati da kuma karfafa alaka da kasashen da ke makwabtaka da ita, yana mai cewa masu takama da kare hakkin bil’adama suna nuna fuska biyu a aikinsu, inda suka yi shiru kan munanan laifukan da ake yi wa al’ummar Gaza.
A safiyar yau ne shugaba Pezeshkian ya isa ma’aikatar harkokin wajen kasar, inda ya gana da mataimakan ministoci da daraktocin ma’aikatar.
A lokacin da yake jawabi a taron, shugaban ya ce, “Tun da yake dan majalisar shawarar Musulunci bai canza ba, har yanzu shi mutum daya ne, dole ne al’umma su kasance masu jajircewa da kwarewa tare da ci gaba da yin aiki tukuru, sun mika ragamar mulki ga ministoci da gwamnonin larduna, wasu kura-kurai dole ne a gyara su, me yasa gwamna ba zai iya yin abin da shi yake yi ba?”
Pezeshkian ya kara da cewa, “Idan aka bi tsarin manufofin – wato manyan tsare-tsare, kuma aka ba da iko ga wadanda ke cikin wannan fanni, aikin zai ci gaba. Idan kuskure ya faru, dole ne a gyara shi. Daga nan ne yanayin kasar zai inganta.” Dole ne kuma gwamnoni su mika mulki ga shugabannin kananan hukumomi.