Fafaroma Francis ya Rasu
Published: 21st, April 2025 GMT
Fadar Vatican ta sanar da mutuwar shugaban majami’ar katolika na duniya, Fafaroma Francis yana da shekaru 88 a duniya.
A shekarar 2023 ne cocin ya zaɓi Fafaroman, wanda asalin sunansa shi ne Cardinal Jorge Mario Bergoglio a matsayin wanda zai jagorance ta, bayan saukar Fafaroma Benedict XVI daga kan muƙamin.
Da safiyar Litinin ne ɗaya daga cikin jagororin cocin ya sanar cikin jimami game da rasuwar ta Fafaroma Fraincis, inda ya ce: “Ya ku ƴan’uwana, cikin alhini, ina sanar da ku game da rasuwar Babanmu a addini, Francis.
Da misalin ƙarfe 7:35 na wannan safiya (Agogon Vatican), Bishop ɗin Roma, Francis ya koma ga mahalicci. Ya sadaukar da rayuwarsa baki ɗaya wajen bauta wa ubangiji da kuma coci.”
“Ya koya mana bin littafi mai tsarki sau da ƙafa, da karsashi da kuma soyayya a fadin duniya, musamman ga wadanda ke cikin talauci da kuma wadanda aka tauye.”
“Cikin godiya mai tarin yawa kan matsayinsa na manzo daga Yesu, mun miƙa ruhin Fafaroma Francis gare ka, kasancewarka mai matuƙar rahama maras iyaka.”
Marigayi Fafaroma Francis ya yi ƙoƙarin kawo sauye-sauye masu dama ga mabiya ɗariƙar katolika, amma ya fi samun goyon baya daga masu ra’ayin mazan jiya.
Shi ne Fafaroma na farko daga nahiyar Amurka, kuma na farko daga ɓarin duniya na kudu.
Ba a taɓa samun wani fafaroma daga wata nahiya ba bayan Turai, tun bayan mutuwar Fafaroma Gregory III wanda aka haifa a Syria a shekarar 741.
Magabacinsa, Fafaroma Benedict XVI shi ne fafaroma na farko da ya yi ritaya daga kan muƙamin don ƙashin kansa a tsawon shekaru 600.
BBC/Hausa
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Fafaroma Rasuwa Fafaroma Francis
এছাড়াও পড়ুন:
An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu
ShareTweetSendShare MASU ALAKA