Nigeria: Wani Bom Da Ya Tashi A Maiduguri Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 7
Published: 13th, April 2025 GMT
Rahotanni da suke fitowa daga Nigeria sun ce, a kalla mutane 7 su ka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama su ka jikkata sanadiyyar fashewar wasu abubuwa masu karfi akan hanyar Damboa-Zuwa Maiduguri.
Rahotannin sun ce abubuwan su fashe ne dai a lokacin da wasu ayarin motoci da suke wucewa ta hanyar tare da rakiyar sojoji a jiya Asabar da hakan ya haddasa asarar rayuka da kuma jikka.
Hanyar Damboa zuwa Maiduguri tana zuwa kananan hukumomi da dama a kudancin Jahar ta Borno, a lokaci daya kuma yanki ne da ya yi kaurin suna a matsayin matsugunin ‘yan Bokoharam.
An dade da rufe hanyar saboda matsalar tsaro, amma gwamnatin Babagana zulum ta sake bude ta, da kuma dawo da zirga-zirgar ababen hawa zuwa Damboa,Chibok da kuma wasu kananan hukumomi da suke a kudancin Jahar.
Ana barin matafiya su bi ta hanyar ne sai biyu a mako daya, bayan sojoji sun yi sintiri da kuma tabbatar da cewa ba a dasa abubuwan fashewa ba. Kusan shekaru biyu kenan ana yin haka. Tuni dai aka dauki wadanda su ka jikkata da ba a tantance adadinsu ba zuwa asibitin cikin Maiduguri domin yi musu magani.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
HKI: Sojoji 62 Ne Su Ka Halaka A Gaza A Cikin Wannan Shekara Ta 2025
Jaridar HKI ta “Haaretz'” ta buga labarin da yake cewa: A cikin wannan shekarar ta 2025, sojojinsu da su ka halaka sun kai 62.
A cikin watannin bayan nan an sami karuwar sojojin mamayar da ‘yan gwgawarmaya suke kashewa a Gaza.
Yankin Khan Yunus dake Arewacin Gaza da HKI take riya cewa ta nike shi, sannan kuma ta kori Falasdinawa daga cikinsa, yana daga cikin wuraren da aka yi wa sojojin mamayar kwanton bauna.
Bugu da kari, har yanzu ‘yan gwgawarmayar suna ci gaba da harba makamai masu linzami daga Gaza zuwa matsugunan ‘yan share wuri zauna da suke kusa da Gaza.
A jiya ma dakarun “Sarayal-Quds” na kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da harba makamai masu linzami zuwa matsugunan da suke da Gaza.
Jaridar ta “Haaratz’ ta kuma ce, Fira ministan na HKI bai yi wa iyalan ko daya daga cikin iyalan sojojin da aka kashe a Gaza ta’aziyya ba, balle ya gana da su.
Jaridar ta kuma ce, hotunan da ake nunawa na Netanyahu yana ganawa da iyalan sojoji tsoho ne ba sabo ba ne.