Gaza: Sojojin HKI Sun Sake Kai Wa Asibitin “Ma’amadani Hari
Published: 13th, April 2025 GMT
Jiragen yakin HKI sun harba makamai masu linzami guda biyu akan ginin asibitin Ma’amadani dake Gaza. Harin ya yi sanadiyyar rushewar wasu bangarori da su ka hada dakunan yin gwaje-gwaje da kantin sayar da magani.
Saboda hare-haren na Isra’ila a wannan asibitin, da akwai gwamman marasa lafiya da suke kwance a kasa a waje, yayin da wasu kuma suke kwance wajen asibiti.
Kungiyar Hamas ta bayyana harin da sojojin HKI su ka kai wa asibitin da cewa wani sabon laifi ne na dabbanci da ‘yan sahayoniyar suka tafka a Gaza.
Haka nan kuma Kungiyar ta Hamas ta zargi Amurka da cewa ita ce take bai wa HKI haske akan tafka laifukan da take yi a Falasdinu.
Bugu da kari kungiyar ta Hamas ta kuma yi mamaki akan yadda kungiyoyin kasa da kasa da su ka hada da MDD suke yin shiru akan laifukan da ake tafkawa da ba su da tamka a wannan zamanin, akan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da cutar da marasa lafiya da korarsu daga asibiti zuwa kan tituna.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Falasdinawa 40 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’oi 24 A Gaza
A yau Laraba sa jijjifin Safiya an sami shahidai 3 a Gaza da hakan ya kara yawan shahidai zuwa 40 a cikin sa’o’i 24.
Bugu da kari, baya ga shahidan da suke faduwa a kowace rana, ana fama da matsananciyar yunwa a cikin yankin, bayan karewar kayan abincin HKI ta sake komawa yaki kwanaki 44 da su ka gabata.
A cikin sansanin ‘yan hijira na “Nusairat” mutane 3 sun yi shahada da su ka hada da karamar yarinya sanadiyyar harin da sojojin na HKI su ka kai wa yankin.
A gabashin birnin Khan-Yunus ma dai wasu Falasdinawa sun yi shahada.
Daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun wuce 52,000,wadanda su ka jikkata kuma sun haura 100,000.