Aminiya:
2025-09-17@23:21:27 GMT

Gaskiyar abin da ake faɗa kan ’yan fim — Samira Sani

Published: 25th, March 2025 GMT

Samira Sani ‘yar asalin garin Kano ne da ta shigo Masana’anrtar Kannywood a 2022.

A tattaunarta da Aminiya, ta ba da tarihinta da kuma yadda ta daɗe tana mu’amala da ‘yan Kannywood kafin ta fara fitowa a fim:

Za mu so ki gabatar da kanki?

Suna na Samira Sani, jaruma a Masanartar Fim ta Kannywood.

Mene ne tarihinki a takaice?

To ni ‘yar asalin garin Kano ne.

An haife ni a garin Dakatsalle da ke Karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano.

Na yi makarantun firamare da sakandare duk a Dakatsalle, bayan na gama sakandare sai aka yi min aure, daga baya Allah Ya kawo ni cikin birnin Kano.

Ke nan kin taɓa yin aure?

Eh na taɓa yin aure, kuma ina da ‘ya’ya uku.

Ta yaya kika samu kanki a Kannywood?

Ta sanadiyyar wata ƙawata, wacce take ‘yar fim ce, tana gayyata ta, muna zuwa wurin daukar fim, a hankali a hankali, ‘yan Kannywood suka san ni, ni ma na san mutane.

A wace shekara kika shiga Kannywood?

Na shiga ne a shekara 2022, shekaru uku ke nan, amma ban fara fitowa a fim ba sai a shekarar 2023.

Me ya ba ki sha’awa kika shiga Kannywood?

A da gaskiya ba na sha’awar Kannywood.

Saboda me?

Saboda yadda ake zagin ‘yan fim, ana cewa ‘yan iska ne, to sakamakon na shiga cikinsu, na ga irin yadda suke da mu’amala mai kyau, suna son junansu, domin idan na je ana daukar fim, za ka ga ana wasa da dariya, har sai ka ji ba ka son rabuwa da su.

To a haka sai na fuskanci abin da ake faɗa a kan ‘yan fim ba gaskiya ba ne, wasu ne suke masa kallo a baibai.

To daga nan sai na ji ina sha’awar abin, to sai na fahimtar da iyayena da ‘yan’uwana, To a haka na shiga Kannywood, inda na fara a hannun Darakta Mujahid M. Soja.

To ke nan sai da kika fara mu’amala da ‘yan Kannywood sannan kika fara fim da su haka ne?

Kwarai kuwa, sai da na fara mu’amala da su sannan na shiga Kannywood, saboda a gaskiya a da ina dari-dari da shiga fim, ina gudun kar a ce mini ‘yar iska to amma da na yi mu’amala da su, sai na fahimce su, kuma na ga abin da ake yi a waje ba a yin sa a fim.

Domin ina mu’amala da ‘yan fim ina yi da wadanda ba ‘yan fim ba, shekara biyu ina mu’amala da ‘yan fim sannan na fara.

To da wane fim kika fara?

Na fara da wata waƙa ce mai suna Ladidi mai Koko da Sosai, wacce muka yi da dan Yarbawa da Kamal Aboki (marigayi) da Adam Dorayi.

A ɓangaren fim kuwa na fara da fim din ‘Yar Tiktok na Darakta Mujahid M. Soja.

Ya zuwa yanzu finafinai nawa ne kika yi?

Za su kai 8 zuwa 9, wadanda suka haɗa da: ‘Yan Tiktok da Soyayya Daya da Buri da Niniya da Umarni da kuma Jikokin Mai gari da sauransu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: kannywood Samira Sani shiga Kannywood a Kannywood

এছাড়াও পড়ুন:

Jigilar Mai: Me Ya Haddasa Rikicin Dangote Da Ƙungiyar NUPENG?

Duk da cewar an yi yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu, rikici ya sake ɓarkewa bayan NUPENG ta ce Dangote bai cika alƙawari ba.

Amma matatar ta musanta zargin, inda ta bayyana cewa ma’aikatanta na da damar shiga ƙungiya idan sun so, amma ba dole ba ne.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa
  • Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano
  • Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo
  • An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • Jigilar Mai: Me Ya Haddasa Rikicin Dangote Da Ƙungiyar NUPENG?
  • An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara