Samun Kuɗi Ya Fi Samun Ɗaukaka Wahala A Kannywood -Baba Sadiƙ
Published: 3rd, August 2025 GMT
Auwalu Labarina, wanda ke cikin matasa jarumai da tauraruwarsu ke haskawa a Masana’antar Kannywood, ya fito a manyan fina-finai da dama da suka hada da darasi, Kwana Casa’in, Gidan Sarauta da kuma shirin nan na Labarina, ya kuma samu kyautuka da dama da suka danganci wannan sana’a tasa ta fim a lokuta daban-daban.
da yake amsa tambaya a kan me yasa ya fi mayar da hankali wajen ɗora bidiyo, musamman na jarumai mata a Masana’antar Kannywood a shafukansa na sada zumunta, musamman kuma ‘Facebook’? Sai Baba Sadiƙ ya ce; ba komai ba ne ya jawo haka illa tsarin biyan kuɗi (Monetization) da kamfanin ‘Facebook’ ya fito da shi, domin yanzu na zage damtse ina neman kuɗi, ba tare da wasa ba, kafin yanzu ina ɗora bidiyon shawarwarin da za su taimaki al’ummarmu, amma kuma su mutanen da ke kallo sai na ga kamar ba su da ra’ayin ire-iren wadannan abubuwa da nake ɗorawa a shafin nawa.
Bayan daukar tsawon lokaci ina yin wadannan bidiyoyi na shawarwari, sai na yanke shawarar yin watsi da shi na koma ɗora bidiyoyina tare da abokan aikina ƴan fim, musamman idan muka haɗu a lokeshan na daukar fim, daga wannan lokaci ne sai na ga yawan ‘likes’ da ‘comments’ ɗin da mutane suke yi a shafi nawa ya ƙaru sosai, sannan adadin mutanen da ke ziyartar shafin shi ma ya ƙaru, sai kuma ga shi ina samun dalar Amurka fiye da 300 a duk lokacin da na ɗora ire-iren wadannan bidiyoyi nawa a shafin, sai kawai na ci gaba da yin hakan.
daga wancan lokacin da na fara ɗora bidiyoyi nawa tare da jarumai mata ƴan fim da sauran sanannun mata, na kan samu aƙalla Naira Miliyan biyar zuwa 10 a duk wata daga abin da ‘Facebook’ ke biya na, don haka yanzu na gane cewa; talauci ne matsalata a lokacin baya, kuma Alhamdulillahi yanzu na fara samun sauƙin wannan matsala a halin yanzu da hanyoyin samu suka ƙara buɗe min, in ji shi.
daga ƙarshe, Baba Sadiƙ ya ce; kamata ya yi a ce matasa su mayar da hankali wajen abubuwan da za su taimake su a rayuwarsu, ba su tsaya suna faɗin aibin wani ko yaba burgewar wani ba, yanzu matasa da dama su kan ɓata lokacin su wajen aibata wani idan ya yi kuskure, ko kuma yabon wanda bai ma san suna yi ba, ba komai ne ke jawo irin haka ba; illa rashin aiki da mafi yawancin matasa ke fama da shi, a maimakon ka tsaya cewa; Rarara ya sai sabuwar mota ko kuma Hadiza Gabon ta yi ‘Slimming’ gara ka je ka nemi abin da za ka rufa wa kanka asiri, kamar yadda ya shawarci matasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Kannywood
এছাড়াও পড়ুন:
Har yanzu ana fama da cutar kwalara a Najeriya – UNICEF
Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu da aka fi samun ɓullar cutar kwalara a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka.
Darektan Hukumar UNICEF mai kula da yammacin Afirka da Afirka ta tsakiya, Gilles Fagninou ne ya bayyana hakan tare da cewar annobar kwalara ta zama tamfar alaƙaƙai a Najeriya.
Haɗarin tirela ya yi sanadin asarar awaki sama da 100 a Zariya Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya“A cewarsa cutar Kwalara na ci gaba da yaɗuwa a Najeriya, inda ƙasar ke fama da ɓarkewar cutar a ‘yan shekarun nan.”
“Ya zuwa ƙarshen watan Yuni, Najeriya ta samu adadin mutane 3,109 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara da kuma mutuwar mutane 86 a cikin jihohi 34,” in ji Fagninou.
Jami’in na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ƙara da cewa, wannan adadi ya sanya Najeriya ta zama ƙasa ta biyu da cutar ta fi ƙamari a yankin yammacin Afirka da Afirka ta tsakiya kamar yadda aka ambata a baya.
Ya yi nuni da cewa ɓarkewar cutar kwalara a yankin yammaci da Afirka ta Tsakiyar ta haifar da matsala ga yara.
Ya ce, an ƙiyasta kimanin yara 80,000 na fuskantar barazanar kamuwa da cutar kwalara a yammacin Afirka da Afirka ta Tsakiya yayin da aka fara damina a faɗin yankin.
A cewarsa, ruwan sama kamar da bakin kwarya da yawaitar ambaliya da kuma yawan matsugunan su na haifar da haɗarin kamuwa da cutar kwalara da kuma jefa rayuwar yara cikin haɗari.
Ya bayyana cewa cutar kwalara cuta ce mai saurin yaɗuwa ta hanyar abinci ko ruwan da ke gurɓata da ƙwayoyin cuta.