Aminiya:
2025-09-17@20:30:19 GMT

Ban taɓa nadamar shiga Kannywood ba — Kabiru Nakwango

Published: 14th, September 2025 GMT

Kabiru Abubakar Aliyu, wanda aka fi sani da Nakwango, ɗaya ne daga cikin jiga-jigan da aka kafa masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood da su.

A cikin wannan tattaunawar, ya bayyana cewa bai taɓa yin da-na-sanin shigarsa sana’ar ba, sannan ya bayyana dalilin da yanzu ba a cika ganin sa sosai a fina-finai ba, da ma yadda ya ce fim ɗin Hausa ya taɓa zama silar sasanta wasu ma’aurata da aurensu yake tangal-tangal.

Tun yaushe ka shiga harkokin fim ɗin Hausa?

Ai harkar fim ɗin Hausa daga baya ta fito, a da wasan kwaikwayo ake yi. Na fara wasan kwaikwayo na rediyo wajen 1970, lokacin ina ƙarami. A lokacin rikoda ta fito. To a sannan na fito a matsayin mace a wasan, saboda a sannan muryata ba ta fashe kamar yanzu ba. Daga nan sai sha’awar abin ta daɗa shiga raina, tun da dama ina kallon iyayenmu a harkar a lokacin irin su Ƙasimu Yero da su Usman Baba Pategi (Samanja), da yake su sun daɗe suna yi kuma abin yana ba ni sha’awa.

Kamar fim ɗin Hausa irin na Kannywood fa, yaushe ka fara shi?

An fara fim ɗin Hausa irin na yanzu ne a wajen 1994/1995. To a lokacin mu tuni ma mun yi nisa a harkokin wasan kwaiwayo, duk da ba mu ce za mu shigo fim ɗin ba. Amma aƙalla tun kafin a fara fim irin na yanzu, mun yi fina-finai za su kai aƙalla bakwai.

A lokacin ba wai zuwa muka yi makaranta aka koya mana yadda za a yi ba, kyamara kawai za a kafa mana, a lokacin irin JVC kyamara ɗin nan, har yanzu ina da ita, wacce take zuwa batiri daban, kanta ma daban. To a haka tun wannan lokacin mun yi fina-finai da dama.

Ko za mu iya sanin wasu daga cikin su?

A lokacin akwai fina-finai irin su ‘Jambaɗe’, ‘Jan artabu’, sai ‘Ta inda kuka yake zuwa…’, da sauransu.

Lokacin da kuke wasan kwaikwayo na rediyo, wace rawa ka fi takawa a cikinsu?

Na fito a mace, wacce ake kira Matar Malam. Ka san ita matar malam duk abin da Malam ya zo da shi, shi za a yi. Ko dai ta bi shi ko kuma ta kangare. Daga baya kuma sai na fito a ɗalibi, daga nan kuma ba a daɗe ana yi ba sai muka shiga ‘stage drama’.

Za ka iya tuna fim ɗin da ka fara fitowa a ciki?

Na fara fitowa a wani fim na Hamisu Iyantama da ake kira ‘Ƙilu ta ja bau’. Ba zan iya tuna shekarar ba. Amma kafin na fito a wannan, na shirya fim nawa na kaina mai suna ‘So ne ko ƙauna’. Shi ne fim na farko na Hausa da ya fara fita a sinima ta farko a Kano, wato Wapa Sinima. Daga baya muka kai shi sinimar Eldorado. Su ne fina-finan farko na Hausa da aka fara a ƙarƙashin kamfaninmu da ake kira da Dabo Films.

Shin ko ka kiyaye shekarar da aka yi shi?

Eh, shi a 1995 aka yi shi.

Akwai waɗanda suke yi wa ’yan fim na yanzu kallon masu ƙarancin tarbiyya. Ya kake ji a matsayinka na ɗaya daga cikinsu?

Bahaushe yana cewa mutunci riga ne, kowa ka gani shi yake sa wa kansa. Babu a inda babu mutanen kirki ko fitsararru. Duk harkar duniya akwai baragurbi. Shugabanni, malamai, ’yan acaɓa, kowacce harka. Shi wannan kallon da mutane suke yi wa ’yan fim, magana ta gaskiya ba kowa suke yi wa ba.

Wanda ya yarda a ce da shi mutumin kawai, za a faɗa masa, haka ma wanda ya yarda a faɗa masa mutumin kirki, shi ma haka za a faɗa masa.

A kwanakin nan, ana ganin bidiyoyinka kana karantarwa. Kwanan nan ka fara ko dama tun tuni kana yi?

Ni malamin makaranta ne, ban kuma ma san lokacin da na fara ba. Aikin mahaifina ne noma da karantarwa, a haka ya haife ni na gan shi yana yi, kuma na koya na iya. Duk abin da ka gan ni ina yi ba su ba, kawai kewayawa na yi na dawo kansu. Amma kuma ni ba malami ba ne babba kamar yadda wasu suke kallo na.

Shin har yanzu kana harkar fim ɗin ko ka daina?

Fim, dalilai da yawa sun sa na dakatar da yawan yin shi, amma ban ce na daina ba. Idan aka zo da fim irin nawa, wanda zai yi kira ga hanyar Allah, kuma ya yi kama da maganar Allah, to zan yi. Amma idan na ga fim ba na Hausawa ba ne, kawai fim ne da aka rubuta shi da yaren Hausa ba zan yi ba.

To ke nan kana ganin irin waɗancan fina-finan da ke isar da saƙon sun yi ƙaranci ke nan?

Idan ka kalli fina-finan da ake yi yanzu, mafiya yawa da yaren Hausa ake yin su, amma ba fim ɗin Hausa ba ne, ni kuma wakilin Hausawa ne.

To mene ne bambancinsu?

Yawwa. Za a ɗauko al’ada. Alal misali, idan Bature zai yi maka fim, zai ɗauko rayuwarsa da al’adarsa da ƙarfin ƙasarsa, sannan ya yi farfaganda domin jan hankalin mutanen duniya ƙarfinsa da muhibbarsa, don ka ji tsoron sa. Kai kuma Bahaushe idan ka ta shi za ka nuna waye kai, yaya ka taso, da me ka girma? Ko rubutun wasiƙa za ka yi, me zai hana ka rubuta da ajami? Hakan zai zama wani abin bajinta, saboda Turawan sun zo sun same ka kana da karatu da rubutu da tsarin shari’a da na mulki.

To amma yanzu sai a zo a yi fim da salon Turawa. A yi fim a ɗauki bindiga ana hare-harbe. Wannan ba al’adar Bahaushe ba ce, kuma a Nijeriya ma ba mu san wannan ba. Fim ake yi kawai da yaren Hausa, amma ba na Hausawa ba. Ko ɗakin shari’a za ka nuna a fim, ya kamata ya zama irin na Bahaushe da siffar shigar alƙali ya kamata ya nuna al’adar Bahaushe tun da ko a kotu ba a haɗa maza da mata wajen zama. Amma ba haka muke yi ba yanzu.

Sannan hatta kalaman da za a yi amfani da su a fim, ya kamata su zama a ingantacciyar Hausa, amma yanzu sai ka ga ana Ingausa ko kuma ka ji mutum ya zunduma ashar a fim. Wannan ba daidai ba ne saboda Bahaushe bai san wannan ba.

Amma ban raina musu ba, suna matuƙar ƙoƙari. Kuma tun farko an sami tangarɗa da aka bar abin a hannun matasa ba a shige ta ba. Attajirai, shugabanni, malamai duk ba su shige ta ba. Kaɗan daga cikin malamai ne ma ba sa aibata ’yan fim. Idan matsala ta zo dubawa ake yi ana da maganinta, ko kuma idan an kawar da ita wacce ta fi ta za ta shigo Kana tunanin nan gaba akwai wanda zai iya hana sana’ar fim? Ko gwamnatin jiha ko ta tarayya?

Sana’a ce da matasa suka ƙirƙire ta daga babu, har ta kai inda take a yau. Ina daga cikin waɗanda suka fara fim ɗin Hausa na yanzu, (ba wasan kwaikwayo ba).

Duk da waɗannan tarin matsalolin da ka yi bayani, waɗanne hanyoyin kake ganin za a bi domin inganta fim ɗin Hausa?

To Allah Ya sawwaƙe. Hanyoyin suna da yawa, amma dole sai an nemi dai masu sana’ar domin a nuna musu ga abin da ake da buƙata, ba wai a wofantar da su ba. Gwamnati ta yarda za ta shiga ciki ta shige musu gaba, ta nuna musu yadda za su girmama Nijeriya su nuna ɗayantakar ƙasar, saɓanin yadda ake nunawa yanzu cewa akwai Hababba da Haƙarami. Akwai ƙabilu ƙasƙantattu akwai shafaffu da mai. To sai an gyara an nuna musu. Duk matsalolin siyasa da na diflomasiyya, duk abin da kake so ɗan fim zai iya gyara shi.

An taɓa wasu ma’aurata, miji da matansa biyu, har yana shawarar sakin su, amma ta sanadin kallon fim suka shirya kansu, mai rubuta fim ɗin ma bai san su ba, kawai ya kalli abin da ke faruwa ya yi fim. Har nan gidana mijin ya zo tare da matan nasa tun daga Sakkwato. Ban san su ba, kuma ba fim ɗina ba ne, amma saboda rawar da na taka har fim ɗin ya yi tasiri a rayuwarsu suka zo don nuna godiya.

’Yan fim suna zuba kuɗinsu, ka ga kuwa dole su yi tunanin yadda kuɗaɗensu za su dawo. Amma wanne irin tallafi gwamnati ta saka a ciki, ba wai kullum wani ya shiga gidan rediyo ya ce duk ’yan fim ’yan iska ba ne.

Ko kana da wani da-na-sani a harkar fim gaba ɗayanta tun lokacin da ka fara ta?

Alhamdulillahi ban taɓa yin da-na-sani ba. Ni dai ban san abin da na yi na da-na-sani ba, sai dai idan wani ya hango. Amma ni dangane da iyayena, ko surukaina ko ’ya’yana ko abokan karatuna ko malamaina, ba ni da matsala kuma ban taɓa abin da zan yi da-na-sani a ciki ba. Hasali ma nakan haɗu da mutanen da ke girmama ni a sanadiyyar fim ɗin.

Akwai abin da ba za ka iya mantawa da shi ba a harkar na daɗi ko akasin haka?

Gaskiya suna da yawa. Na daɗin daga ciki akwai ranar da na yi tafiya daga Kano zan je Gombe, sai mota ta lalace min a hanya, ni kuma kuɗin hannuna a lokacin ba za ma su ishe ni wunin ranar ba, ballantana na gyara motar. To fuskata da ake gani a fim ta sa aka tarbe ni aka kira bakanike ya gyara min motar aka sallame shi, sannan ni ma aka ba ni kuɗin da suka ishe ni har na dawo gida na yi uzururrukana da su na aƙalla kwana 10, duk arziƙin fim.

Na kuma taɓa sauka a wani gari cikin dare, ina neman wanda zan je wajensa, saboda lokacin babu wayar salula, ina ta tambayar mutumin ba a gano shi ba, ga shi wajen ƙarfe ɗaya na dare. Na shiga wata unguwa sai kawai wani mutum ya buɗe ƙofa ya ce Malam Kabiru ne? Ai kuwa sai ya ce da matarsa na shigo na kwana a gidansa sai da safe na nemi wajen da zan je. Komai akwai a ɗakin.

Har yanzu kuma muna zumunci da mutumin. Kwana biyar na yi niyyar yi a garin a lokacin, amma daga ƙarshe sai da na yi kwana 13, saboda karamcin da aka nuna min. Har littafi sai da mutumin ya sa muna darasi da shi.

Kazalika, a lokuta da dama matata ta sha zuwa asibiti amma a ce ba sai ta bi layi ba, cikin ƙanƙanin lokaci za a yi mata komai, wannan duk arziƙin fim ne. Ina kuma da makaranta, amma tun daga wurare masu nisa wasu suke kawo ’ya’yansu, saboda kawai sun ji an ce tawa ce kuma suna gani na a fim. Sannan mutane na girmama ni duk inda na shiga, duk da cewa wani girman ma ban cancance shi ba.

Sannan a ɓangaren rashin daɗi kuwa, an taɓa kama ni saboda na tsaya wa wani mutum a kotu, amma ya gudu. Zan kwana a caji ofis amma wani ya zo ya fitar da ni cikin daren, sai da ya je har wajen alƙali ya nemi izini. Masinjan kotun ne yake ba da labari wani ya ji ya yi ta faɗi tashi sai da ya je har wajen alƙali ya ba da umarni aka sake ni, ban kwana a ofis ɗin ba. To ka ga wannan abu ne mara daɗi da ba zan manta da shi ba.

Ko akwai wanda yake sha’awar harkar fim a zuri’arka?

Eh, akwai ɗana da ya nuna sha’awa amma bai yi nisa ba ya bari. Yanzu haka kuma akwai wanda ya ce yana sha’awar tace fim, sai na haɗa shi da masu yi, yanzu haka kuma har ya goge a tace fim din.

To kana fatan nan gaba ya zama magajinka ke nan a masana’antar?

A’a, ba zai iya ba.

Me ya sa?

Shi fim da taka rawa a cikinsa a jikin mutum yake. Sai dai ya yi shuhura a wani abin daban, amma ba irin nawa ba. Kowa da yadda Allah Ya yi shi. Akwai waɗanda suka fi ni ilimin addini a Kannywood, amma sai a ce a kira ni. Akwai kuma waɗanda sun fi ni ƙwarewa a harkar, amma saboda wasu dalilai, sai a ce a kira ni.

Kowa da yadda Allah Ya yi shi. Misali irin su Ibrahim Mandawari, gogagge ne a fim, da shi aka fara Kannywood, amma abin da zai yi ba zan iya yi ba, shi ma abin da zan yi ba zai iya ba, saboda kowa da irin baiwarsa.

Ko kana da saƙo ga ’yan uwanka ’yan fim?

Babban saƙona gare su shi ne su ji tsoron Allah kan duk abin da suke yi, sannan su yi ƙoƙari wajen tallar addininsu da al’adunsu sannan su riƙa yafiya a junansu.

Ga sauran jama’a kuma, ya kamata su riƙa kyautata zato, su daina gaggawar yanke wa wasu hukunci. Kowa na iya yin kuskure, kuma za a iya gyara masa ta hanyar da ta dace, amma ba ta kafafen yaɗa labarai ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kabiru Nakwango kannywood kwaikwayo wasan kwaikwayo a Kannywood

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu

Sojoji biyu sun ji rauni bayan wani harin kwanton baya da ’yan bindiga suka kai kan ayarin motocin Kwamandan kwamandan Rundunar Sojoji ta 382 Ƙaramar Hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ruwan Godiya, kan hanyar Sheme–Kankara, lokacin da tawagar Operation Fansan Yamma (OPFY) ke wucewa.

Ganau sun ce sojojin na kan hanyar ziyartar sansanonin sojoji a yankunan Faskari da Mabai da Ɗan Ali lokacin da aka kai musu hari.

Sai dai sun yi nasarar tunkarar ’yan bindigar har suka kuvuta, kodayake sojoji biyu sun samu raunuka na harbi kuma aka kai su asibitin sojoji domin jinya.

An kai wa sojojin harin ne a rana ɗaya da shugabannin al’ummar Faskari suka zauna da wakilan ’yan bindiga domin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS

Hakan ya sanya Faskari zama ƙaramar hukuma ta baya-bayan nan da ta shiga irin wannan sulhu bayan ƙananan hukumomin Ɗanmusa da Jibia, Batsari da Ƙanƙara, Kurfi da Musawa.

Yarjejeniyar na neman kawo ƙarshen tashin-tashina, garkuwa da mutane da kuma ƙaura da ake fama da su a jihar.

Amma akwai shakku kan ɗorewar ta, domin wasu daga cikin shugabannin ’yan bindigar sun bayyana cewa sulhun ya shafi ƙananan hukumomin da suka shiga yarjejeniyar kawai, lamarin da ya janyo tsoron cewa sauran wuraren da ba su rattaba hannu ba, suna iya ci gaba da fuskantar hare-hare.

Wasu mazauna Ruwan Godiya sun ce ayyukan ’yan bindiga na ƙara ta’azzara a sassan Katsina duk da yarjejeniyar sulhun da aka ƙulla da wasu daga cikin shugabanninsu.

Masana sun bayyana cewa hakan ya nuna raunin irin waɗannan tsare-tsare na sulhu, tare da tabbatar da buƙatar ƙarin sa-ido a yankunan da ke fuskantar barazana.

Sulhun Faskari da ’yan bindiga

Ƙaramar Hukumar Faskari ta zama ta baya-bayan nan a Jihar Katsina da ta shiga yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga, domin kawo ƙarshen kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma ƙaura da ake fama da su a yankin.

Kamar sauran sulhunan da aka kulla a ƙananan hukumomi guda shida, sharuddan yarjejeniyar sun ba wa ’yan bindiga damar shiga garuruwa da kasuwanni da asibitoci.

Haka kuma, za su sako duk wanda aka yi garkuwa da shi ba tare da sharaɗin ba. A sakamakon haka, al’umma za su iya komawa gona da kasuwanni cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar farmaki ba.

Yarjejeniyar ta biyo bayan taron al’umma da aka yi a Faskari, inda fitaccen shugaban ’yan bindiga, Ado Aliero, wanda ake nema ruwa a jallo, ya tabbatar wa manoma tsaronsu.

“Daga yau kowa ya koma gona cikin kwanciyar hankali; ba abin da zai faru a Faskari baki ɗaya,” in ji Aliero cikin wani bidiyo da Aminiya ta gani.

Aliero ya ɗora laifin rushewar yarjejeniyar da aka yi a baya kan cafke ɗansa, yana mai cewa ya bi duk hanyoyin lumana, amma abin ya gagara, kafin ya koma tayar da hankali.

A wani bidiyo daban kuma, wani ɗan bindiga da aka gani sanye da rigar harsashi ya zargi hukumomi da nuna wariya da rashin adalci, yana mai cewa sulhu na gaskiya zai tabbata ne kawai idan aka yi adalci ga kowa.

Sai dai duk da rahotannin da ke cewa jami’an gwamnati da na tsaro sun halarci taron, gwamnatin Jihar Katsina ta nesanta kanta daga wannan yarjejeniyar.

Akwai masu kawo cikas — Gwamna Raɗɗa

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya ce duk da irin ƙalubalen tsaro da ake fuskanta, gwamnatinsa na samun ci-gaba, sai dai akwai masu ƙoƙarin kawo cikas.
Ya bayyana haka ne a wani taron shawarwari da aka gudanar a Katsina ranar Lahadi, wanda ya tattaro manyan masu ruwa da tsaki ciki har da sarakunan gargajiya da shugabannin siyasa da shugabannin tsaro da masana, ’yan kasuwa da shugabannin addini.
Gwamnan ya ce tsaro ne ginshiƙin ajandar ci-gabansa tare da ilimi da noma da kiwon lafiya da kuma tallafa wa ƙanana da matsakaitan ’yan kasuwa.
Ya sanar da cewa gwamnati za ta gina gidaje 152 ga iyalan da aka raba da muhallansu a Jibia, tare da shirya shirin tallafa wa tubabbun ’yan ta’adda da suka domin kada su koma ɓarna.
Haka kuma ya yaba wa jami’an sa-kai da ƙungiyoyin tsaro na gari da suka taimaka wajen dawo da ƙwarin gwiwa a tsakanin jama’a.
Cikin manyan da suka halarci taron akwai tsohon Gwamna Aminu Bello Masari da dattijo Sanata Abu Ibrahim da fitaccen dan kasuwa Alhaji Ɗahiru Mangal da Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, Ministan Gidaje Arc. Ahmed Ɗangiwa, da kuma Hadiza Bala Usman mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsare-tsare.
Sauran sun hada da tsohon Daraktan DSS Alhaji Lawal Daura, tsohon Daraktan NIA Ambasada Ahmed Rufai, tsohon Shugaban Kamfanin na NNPC Injiniya Abubakar Yar’adua da Babban Alƙalin jihar Alhaji Musa Ɗanladi, da kuma manyan hafsoshin soja da dama da suka yi ritaya.
Hakazalika, an samu halartar manyan jami’ai, malamai daga jami’o’i da ƙungiyoyin ƙwadago da ƙungiyoyin farar hula da ’yan kasuwa da sauran shugabanni daga sassa daban-daban na jihar.
Gwamna Radda ya jaddada cewa zai ci gaba da karɓar suka da shawarwari daga masu kishin ƙasa, tare da kira ga haɗin kai domin shawo kan matsalolin tsaro da tattalin arziki da jihar ke fama da su.

Abin da mahalarta suka ce

A nasa vangarenm Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Faruk Lawal Joɓe, ya bayyana cewa gwamnatin Raɗɗa ta samar da sama da ayyuka 35,903 a fannoni daban-daban ta karkashin manufar “Gina Makomarka.”

Joɓe ya bayyana ce an samar da ayyukan ne ta hanyar ɗaukar malamai da shugabannin unguwanni da jami’an tsaro na sa da mafarauta da sauransu domin su riƙa taka rawa wajen wanzar da zaman lafiya.

Ya kuma yi ƙarin haske kan aikin Sabunta Birane na Katsina State Urban Renewal da ya lashe Naira biliyan 74.9 wanda ya shafi manyan ayyuka a Daura da Funtua da Katsina.

Ayyukan sun haɗa da gina sabuwar hanyar Eastern Bypass mai tsawon kilomita 24, titi mai hannu biyu a cikin Katsina, gyaran tituna a Daura da Funtua, da kuma kammala wasu muhimman hanyoyin karkara.

A nasa jawabin, Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida, Dakta Nasir Muazu, ya ce gwamnatin Raɗɗa ta ɗauki matakin rashin tattaunawa da ’yan bindiga.

Ya ce abubuwan da ke haifar da ta’addanci sun haɗa da son zuciya da rikice-rikicen albarkatu da sauyin yanayi, da kuma rashin adalci a cikin al’umma.

Ya ƙara da cewa daga 2011 zuwa 2015 matsalar ta tsaya a ƙananan hukumomi biyar, amma ta bazu zuwa 25 a lokacin tsohon Gwamna Aminu Masari bayan shirin afuwa ya faskara.

Kwamishinan ya bayyana cewa hare-haren soji sun lalata maɓoyar ’yan bindiga da dama, sun buɗe manyan hanyoyi, sannan mutum 628 da suka tsira daga hare-hare sun samu kulawar lafiya a bana.

Ya ce yanzu dakarun Community Watch, masu aikin sa-kai da ’yan banga suna mara baya ga jami’an tsaro da ke amfani da jirage marasa matuƙa da makamai da motocin aiki.

Shugaban Ƙungiyar ƙwadago (TUC) na jihar, Muntari Abdu Ruma, ya gargaɗi gwamnati ta yi taka-tsantsan da yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga lura da yarjejeniyar Kankara ta 2016 da ta gagara.

Haka kuma, shugaban ƙungiyoyin farar hula na jihar, Malam Abdulrahman Abdullahi, ya ce akwai buƙatar ƙarin haɗin kai tsakanin jihohin Arewa maso Yamma wajen yaki da ’yan bindiga. Ya yi nuni da cewa ziyarar da dattawan Katsina suka kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bisa jagorancin Gwamna Raɗɗa ta fara haifar da sakamako mai kyau a Ƙanƙara da Faskari, amma dole a ci gaba da ayyuka cikin tsari.

A nasa ɓangaren, Sanata Ibrahim Tsauri na jam’iyyar adawa PDP, ya ce taron ya fi karkata wajen bayyana nasarorin gwamnati fiye da ba wa mahalarta dama su yi sharhi.

Duk da haka ya ce idan aka ci gaba da irin waɗannan taruka, za su iya kawo sauyi ga jihar bayan shekaru 15 na ƙalubale.

An ce mahalarta taron sun yi alkawarin mara wa gwamnati baya wajen shawo kan matsalar samari, musamman shaye-shaye da sauran laifuka.

Sauran muhimman shawarwarin sun haɗa da haɗe hanyoyin sadarwa a wuri guda da nufin samun nasarar wannan abu da aka sanya a gaba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas
  • Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo
  • DSS Ta Maka Sowore, Facebook Da X A Kotu Kan Wallafa Rubutu Game Da Tinubu
  • Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara 
  • Tarihin Ƴan Majalisar Farko Kafin Da Kuma Zamanin Mulkin Mallaka (3)