Aminiya:
2025-04-30@19:19:30 GMT

Finafinan Kannywood da suke tashe da kuma manyan marubutansu

Published: 6th, April 2025 GMT

Wani nazarin finafinan Kannywood da BBC Hausa ta gabatar ya nuna cewa, Masana’antar Kannywood tana ta samun sauye-sauye, musamman a bangaren shirya fim da kasuwancinsa, inda daga CD aka koma sinima, yanzu aka koma YouTube, sannan ake ta hankoron shiga manhajojin duniya ka’in da na’in.

A wannan shekarar, kamar kowace shekara, masu shirya finafinan Kannywood sun taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa da fitar da finafinai masu kyau, wadanda suka kayatar da masu kallo.

Yadda Kanawa suka huce takaicin rashin Hawan Sallah Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya (2)

Tun bayan komawa dora finafinai a YouTube, yanzu za a iya cewa harkokin Kannywood sun fara komawa yadda suke a baya, bayan a baya masana’antar ta fara durkushewa.

Nazarin ya yi tankaɗe da rairaye, sannan ya zakulo wasu finafinai da suke tashe. Sai dai kusan finafinan duka masu dogon zango ne, wanda hakan ke nuna yadda masana’antar ta sauya da kuma hanyar da ta dosa domin dorewarta.

Da farko da aka fara finafinai masu zango, an yi tunanin kananan masu shirya fim ne kawai suka yi, su ɗora a YouTube, har ma wasu suke ganin ba su da inganci.

Amma yanzu an wayi gari manyan furodusoshin Kannywood sun shiga ana damawa da su.

Daga cikin finafinan da aka zakulo, akwai wadanda an dade da fara yin su, amma har yanzu suna jan hankalin mutane. Ga yadda jerin finafinan ya kasance:

Labarina

Labarina fim ne mai dogon zango na fitaccen darakta, Malam Aminu Saira, wanda sunansa ya riga ya yi amo, ta yadda ba ya bukatar gabatarwa ga dukkan masu kallon finafinan Hausa.

Fim ne mai tsari shigen labarin ‘Dare dubu da daya’, inda daga wannan labarin za a shiga wani labarin daban, wanda a cewar daraktan, hakan zai sa fim din ya dade ba tare da ya salance ba saboda ba labari daya ba ne.

A shekarar 2020 aka fara fim din da labarin Sumayya wato Nafisa Abdullahi, wadda daga baya ta rikide ta koma Fati Washa, inda a karshen zango na bakwai aka dakata da labarin Sumayya, aka tafi hutu.

Amma yanzu labarin ya koma na Alhaji Mainasara wato Sadik Sani Sadik, wanda aka fara daga zango na takwas, kuma yanzu haka ana zango na 11.

Labari ne kan yadda Alhaji Mainasara ya batar da kama, ya fito a matsayin talaka domin samun soyayya ta gaskiya bayan wahalar da ya sha a farko, inda ya hadu da Jamila wato Amina Uba Hassan, ya nuna mata kauna.

Daga bisani ya tura mata direbansa da sunan yana da arziki, ita kuma ta amince da shi, maimakon Mainasara.

Ana cikin haka ita kuma kawarta, Maryam wato Fatima Hussaini ta amince za ta aure shi a haka.

Bayan aure komai ya fito fili. Amma daga baya matsala ta sa Maryam ba za ta haihu da shi ba, ta sa shi auren Dakta Asiya wato Diamond Zahra.

Fim din ya fitar da jarumai mata wadanda yanzu ake yi da su a masana’antar irin su Firdausi Yahaya da Fatima Hussaini da Amina Uba Hassan da sauransu.

Yawancin fitowar fim makomako na samu masu kallo sama da miliyan 1.

Manyan Mata

Fim din Manyan Mata shi ma ba a shekarar 2024 aka fara ba, amma yana ci gaba da jan masu kallo.

Fim ne da ya tara manyan jarumai masu yawan gaske, wanda za a iya cewa ba a saba ganin hakan ba.

Furodusa Abdul Amart Maikwashewa ne ya shirya, kuma ya dauki nauyi, sannan Sadik N. Mafia ya fara bayar da umarni, daga baya Ali Gumzak ya ci gaba.

A fim din an nuna yadda wasu mata suke shan wahala a gidajen miji da ’yan gudun hijira da sauran mata talakawa da yadda wasu suke amfani da damar da suke da ita wajen cin zarafinsu.

Sannan a gefe guda kuma, akwai mata biyu wato Laila (Hadiza Gabon) da Nadiya wato Aisha Tsamiya, wadda aka maye da Rabiatu Kafur da suke kokarin kwato ’yancin mata da kungiyarsu ta ‘Manyan Mata’, tare da kokarin nuna amfanin ilimin ’ya’ya mata.

Yanzu dai kallo ya koma sama, bayan rikici ya barke a tsakaninsu. Kusan duk wani babban jarumi a Kannywood yana cikin fim din, har da waɗanda aka daɗe ba a ji duriyarsu ba.

Yawancin fitowar fim ɗin a mako-mako yana samun masu kallo kusan 500,000.

Gidan Sarauta

Gidan Sarauta na cikin finafinai masu dogon zango na furodusa Abubakar Bashir Maishadda, wanda yake jan hankalin masu kallo.

An fara fitar da fim din ne a ranar 5 Nuwamban 2023 kuma jarumi Umar M. Shareef da jaruma Mommee Gombe ne suke jan fim din tare da taimakon Garzali Miko da Aisha Najamu.

Ali Nuhu da Hadizan Saima da Yakubu Mohammad da Rabiu Rikadawa da Abale duk suna cikin fim din.

An gina fim din ne a kan Umar M. Shareef, wanda ya fito a yarima mai jiran gado, ya fada soyayya da ‘yar talaka, Bintu (Momme Gombe), amma bai bayyana ba, daga kaninsa ya riga shi aurenta.

Amma sai aka gane akwai wani abu a tsakaninsu, wanda hakan ya sa kanin ya sake ta, shi kuma ya aura.

Wannan ya sa aka yi fushi da shi, aka ba shi zabin ko dai Bintu ko sarauta, inda ya zabi matarsa, ya hakura da sarautar.

Daga bisani shi ma Garzali ya hango yarinyar Tafida, wato Badariyya (Firdausi Yahaya), inda ya fada kogin kauna, amma yana tsoron shiga halin da yayansa yake ciki.

Ali Nuhu ne ya ba da umarnin a fim din, wanda dukkan jaruman suka dage wajen fitar da labarin fes.

Garwashi

Garwashi fim ne da aka fara fitarwa a ranar 12 ga watan Agustan 2024 a YouTube. An shirya fim ɗin ne a kan ƙalubalen da matan da mazajansu suka rasu suke fuskanta daga wurin ’yan’uwa da mutanen gari.

Jarumar shirin, Asma’u wato Firdausi Yahaya tana shan fama daga dangin mijinta da ’yan’uwanta da ma wuraren da take aiki.

Fitacciyar marubuciya Fauziyya D. Suleiman ce ta tsara labarin, sannan fitaccen darakta Yaseen Auwal ya ba da umarni.

Fim din ya dauki hankalin masu kallo sosai cikin kankanin lokaci, musamman ganin yadda jarumar take shan wahala.

Allura Cikin Ruwa

Fim ne da aka shirya kan Na’ima wato Rukky Ali, wadda marainiya ce, da aka tsinta bayan an harbe mahaifiyarta.

Daga baya maza irin su Maina wato Yakubu Mohammad, wanda take wa kallon kanin mahaifi da Alhaji Hadi wato Sani Danja da Dakta Hashim wato Adam A. Zango da Sadik wato Isa Ferozhkan, wanda suka daɗe suna soyayya, duk suka nuna sha’awar aurenta.

Daga baya an gano ashe tana da tarin dukiya da aka rasu aka bar mata. Saboda soyayyarta ce Maina ya fallasa cewa, Tijjani Faraga ba mahaifinta ba ne, don haka ya ce babu laifi don ya aure ta.

Kamfanin 2Effects ne ya ɗauki nauyin shirin, sannan Yakubu Mohammed ne ya ba da umarni.

Fitattun marubutan finafinan Kannywood da suke tashe

A harkar finafinan Hausa na Masana’anatr Kannywood, an fi mayar da hankali kan ‘yan fim din da suke fitowa, musamman ma wadanda suke jagorantar finafinan, inda akan manta da wadanda suke bayan fage.

A harkar, akwai masu ruwa da tsaki da dama da suke bayar da gudunmuwa wajen daukar fim, tun daga marubuta da masu fitilla da masu sauti da masu daukar bidiyo da tsara dandali da zirgazirga da sauransu.

A cikin wadanda suke aiki a bayan fage, an fi sanin furodusa da darakta, amma ba a cika ambaton sunan marubuta ba, wadanda kuma alkaliminsu ne yake saita fim, sannan idan ya samu aiki mai kyau, masu kallo su yaba.

Wannan ya sa muka rairayo wasu marubuta da alkalumansu suka rubuta finafinai wadanda suka yi shuhura, duk da cewa akwai zaratan marubuta da a ’yan kwanakin nan ba su yi wani aiki babba ba.

Yakubu M. Kumo

Yakubu M. Kumo, marubuci ne wanda a yanzu alkaminsa ke tashe a rubuce-rubucen finafinan Masana’antar Kannywood.

Daga cikin fitattun finafinan da ya rubuta akwai Labarina da Manyan Mata da Jamilun Jiddan da Gidan Sarauta da sauransu.

Ya dade yana rubuta finafinai masu inganci wadanda mutane suka yaba.

Fauziyya D. Suleiman

Fauziyya marubuciya ce da ta dade tana rubuta fitattun finafinai masu kayatarwa, tun daga kananan har zuwa masu dogon zango.

Daga cikin fitattun finafinan da ta rubuta akwai Dadin Kowa da take cikin marubutan fim din, wanda zuwa yanzu an kai shekara 10 ana yi.

A cikin finafinan da ta rubuta suke tashe, sun hada da fim din da yake tashe a yanzu wato Garwashi, kuma tana cikin masu shiryawa.

Mujahid Koguna

Mujahid Koguna da Yakubu Mohammad ne suka hadu wajen rubuta fim din Allura cikin ruwa na 2Effects kuma ya rubuta fim din Fansa.

Abdulkarim Papalaje

Abdulkarim Papalaje yana cikin sanannun marubuta kuma tsohon marubucin finafinan Hausa ne mai basira da yarubuta finafinai da dama da suka hada da Adamsy da Madubin Dubawa duka na Ali Nuhu da Ni da Matata da Oga Abuja da sauransu.

Nazir Adam Salihi

Nazir Adam Salihi shi ma sanannen marubuci ne da ya rubuta Gidan Badamasi.

Wasu marubutan da suka shahara sun hada da Jamil Nafseen da Nabila Rabi’u Zango da ya rubuta fim ɗin Umarni na furodusa Nazir Ɗanhajiya, waɗanda ana yabawa da su.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Allura cikin ruwa Fauziyya D Suleiman Garwashi Labarina Manyan Mata finafinan Kannywood da sauransu Manyan Mata

এছাড়াও পড়ুন:

Kissoshin Rayuwa: Imam Al-Hassan 114

114-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissiso da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan, ko kum littafin mathnawi na maulana Jalaluddeen rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///… Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-hassan limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), kuma da na farko ga Fatimah(s) diyar manzon All..(s), sannan jikansa na farko.

A cikin shirimmu da ya gabata, mun yi maganar yadda Khalifa Uthman ya wanye da Ammar dan Yasir ( R), mun ji yadda Ammar ya tashi da shi da iyayensa suka fara karban musulunci a Makka, da kuma yadda suka yi shahada a hannun Abu Jahal, sannan yadda Ammar ya kubuta daga sahrrinsa bayan ya fadi abinda suke so, ba da sonsa ba. Amma alkur’ani ya sauka yana tabbatar masa da Imani.

Sannan munji yadda manzon All…(s) yake himmantuwa da al-amarin Ammar don Yasir ba don iyayensa su ne shahidar na farko a makka ko a musulunci ba, sai har da cewa yana da Ikhlasi da kuma tsoron All… don haka manzon All..(s) yana girmama Ammar dan yasir ne saboda tsoron All…da kusancinsa da shi. Saboda a hadisan da aka karbo daga gareshi (s) dangane da Ammar suna maganane a kansa, kamar . Inda yake cewa. All..kayi fushi da wanda yayi fushi da Ammar. Sannan manzon All..yayi masu alkawali da shiga aljanna tun suna Makka, inda yake cewa: Ya ku yan gidan yasir kuyi hakuri laillai makomarku aljanna ce.

Sannan munji yadda ya narke a cikin son Aliyu dan Abitalib (a) bayan wafatin manzon All… Da kuma yadda Khalifa Uthman ya sa aka dakeshi har ya suma, har sau biyu.

A cikin shirimmu nay au zamu yi magana kan yadda aka yi wa Imam Alhassan (a), dangane da wai yana son Khalifa Uthman, kuma yana bakin ciki da kissansa, wanda Taha Hussain ya kawo a cikin littafinsa –Fitnatul Kubra.

Wasu malaman tarihi sun ruwaito hadisan kariya sun jinginawa Imam Alhassan dan Aliyu dan Abitalib (a) dangane da Khalifa Uthman, sun riya cewa Imam Alhassan (a), yana daga cikin masoyan khalifa Uthman, kuma yana sonshi har cikin zuciyarsa. A cikin rayuwarsa da kuma bayan kashe shi.

Dr Taha Hussain yana daga cikin wadanda suka tafi a kan wannan ra’ayin, inda yake fada cikin littafinsa Ftnatul Kubra, yana cewa” Hassan (a) bai gushe ba yana son Uthman, ya kasance masoyin Uthman ne da gaske, sai dai bai zare takobi don neman fansar jininsa ba, don bayan ganin hakan hakkinsa ne, wasu lokutan yakan wuce gona da sonsa Uthman har sai da a fadawa babansa (Imam Ali) abinsa dai dace ba. Kamar yadda, masu ruwaye sun ruwato daga Ali (a) ya wuce dansa Imam Hassan (a) yana alwala, sai ya ce masa, ka kyautata alwala, sai ya bashi wannan amsar mai daci, inda wai yana ce masa (hakika kun kashe wani mutum a jiya yana kyautata alwala). Sannan Aliyu (a) bai kara wani abu ba sai wannan Kalmar, (hakika All..ya tsawaita sonka ga Uthman).

Sai dai idan muka dubi wannan ruwayar wanda Taha Hussain ya kawo shi don karfafa ra’ayinsa, hakaka Balaziri ya ruwaitoshi, dada Mada’in, a cikin littafinsa ‘Al-ansabul Al-ashraaf JZ 5 sh 81, Shi wannan Mada’ini an sanshi da kin iyalan gidan manzon All..(a) , wato nasibi ne, sannan an sanshi da kirkiro hadisai na yabo da goyon baya ga banu umayya, yana jinginawa manzon All..(s).

Kuma manufarsa da kirkiro wannan hadisin ita ce tsarakaka banu Umayya, ta jikan manzon All..(s) mai tsari Imam Hassan (a). Don ya nuna cewa salihan bayi kamar Jikan manzon All..(s) yana son Uthman. Banda raunin sanadin wannan hadisin, ga wasu karin abin lura a cikinsa.

01- Idan har da gaskiya ne, Imam Ali (a) ya na son yi wa dansa gyara a alwalarsa, to me yasa Imam Hassan (a) zai fada masa wannan kalmomi masu daci?, Sannan A lokacinda aka kashe Khalifa Uthman, Imam Hassan (a) yana dan shekara 32 a duniya bai iya alwala ba? Imam Hassan (a) ya tashi a gaban manzon All..(s) yana dan shekara 7 a duniya, kakansa manzon All..(s) ya kaura daga wannan duniya, amma bai koyawa jikansa na farko, alwala ba?

Sai ya yana dan shekara fiye da 30 ne babazansa zai koya masa al-walah, ? ko way a san wannan ba haka yake ba.

Sannan ina hadisin nan da aka bayyana cewa Imam Hassan da Hussain (a) suka ga wani dattijo bai iya alwala ba, sai tunda su yara ne a lokacin sai suka yi dubara ta kyautata masa al-walansa, inda dayansu yayi alwala irin na dattijo sai dayan kuma yayi alwala mai kyau, sai dattajan ya gano cewa da shi ake nufi sai ya gyara alwalansa. ?

Wanda ya nuna cewa Imam AlHassan da Alhussain (a) suna koyawa mutane alwala tun kakansu manzon All..(s) ya na da ransa a duniya.

02-Sun ce Imam Alhassan (a) yana daga cikin masu kare khalifa Uthman a lokacinda yan tawaye suka yiwa gidansa kofar rago, kuma yana haka tare da Umurnin babansa Imam Ali(a) ne, to ta yaya a wannan hadisin Imam Hassan yana zargin babansa da kashe Uthman? .

Al-hali mun san cewa Imam Hassan yana tare da mahaifinsa, a yakin Jamal da kuma yakin siffin, a lokacinda yayi wadanda suke tuhumarsa da kashe Khalifa Uthman, suna cewa suna yakarsa ne don daukar fansar jinin Uthman. Imam Alhassan da Alhussain duk suna tare da mahaifinsu a wadannan wurare suna goyon bayansa, kuma basa tuhumarsa da kashe Khalifa Uthman.

Wannan ya tabbatar mana cewa, Mada’ini ya kirkiro wannan hadinsin ne tare da manufar da muka bayyana.

03-Ayyukan Uthman ne suka kasheshi, ya dorawa mutanen Masar da Kufa danginsa suka yi ta kashe su da kuma zaluntarsu, sun kawo kokari a Madina ya ki amsa korafe-korafensu, a lokacinda ya amsa kiran mutanen masar, daga baya ya warware.

A nan sai suka ce ko ya sauka daga khalifanci ko kuma su kasheshi, da yaki sauka suka kashe kashe. Imam Ali (a) bai da hannu ko kadan wajen kissan Khalifa Uthman, ta yaya dansa Imam Hassan (a), kamar yadda ya zo a cikin Hadisin Mada’ini,  zai tuhum- babansa da kissan Uthman, kamar yadda wannan hadisin yake cewa,  ya san cewa ba haka ne ba.?  

Amma abinda ya faru kafin kissan Khalifa na uku,  shi ne cewa, Khalifa Uthman ya aikata abubuwan da dama wadanda basu dace ba, har sai ya kai ga ba wani kare shi a cikin sahabban manzon All..(s) a Madina.

Hatta, talha da zubai da Abdurrahman bin Auf, wanda ya dorashi kan khalifancin, kuma  wadanda ya yi masu ni’imoni, masu yawa, sun dawo daga rakiyarsa.

Duk sun dawo suna fushi da shi. Ta yaya wadannan sahabban manzon All..(s) da salihan bayi daga cikinsu wadanda muka ambata a baya, kamar Abuzar, Ammar, Abdullahi dan Mas’ud da Aliyu dan Abi talib da sauransu duk suna aibata shi. Amma sai Imam Hassan (a) ya zama ya na sonsa?. Ba zai yu ba.

Don haka tare da wannan zamu ga cewa, ba kuma wata kima ga wannan Hadisin a sanadinsa da mataninsa. Abin mamaki shi ne, ta yaya Taha Hussain bai yi bincike mai zurfi a cikin wannan hadisin ba har ya zo ya fada cikin wannan tatsuniyar.

Don haka a lokacinda ayyukan Uthman suka zama abin tattaunawa a ko ina a Madina da sauran manya manyan garuruwan musulmi, sai zabubbu cikin sahabban manzon All..suka taro suka yi shawara, suka kuma yanke shawara kan cewa dole ne su sauya shugabancin musulmi. Don haka suka aika wasiku zuwa manya manyan kasashen musulmi suna neman taimakonsu da makamai da kuma sojoji.

Ga Nassin abinda ya zo cikin daya daga cikin wasikun da suka rubuta. Wannan wasikar zuwa ga mutanen Masar.

{Daga muhijiruna na farko, da sauran shura, zuwa ga wadanda suke kasar Masar, daga sahabbai da kuma masu binsu wato (tabi’ina), Bayan haka:

Da ku zo wajemmu, ku kawo dauki ga khalifancin manzon All..(s) kafin ma’abutanta, su kwaceta su kwaceta, to lalle lillafin All.. an sauya shi (ba’a aiki da shi),kuma sunnar manzon All..(s) an sauya ta, kuma hukunce, hukuncen khalifofi biyu an sauyasu, Muna hada All…kan cewa duk wanda ya karabta wannan takardan, daga cikin sahabban manzon All…(s)  da suka saura, da mabiyansu da kyautatawa, face ya taho mana, don ya karbo mana hakkimmu, kuma mu bashi hakkinsa, to ku zo mana idan har kunyi Imani da All..da ranar lahirah, (ku zo ku) ku tsaida gaskiyar bisa tafarki bayyananniya wanda manzonku (s) ya barku a kanta, kuma wacce khalifofi suka barku a kanta, an rinjayemu kan hakkimmu, an mamaye dukiyarmu, kuma an shiga tsakanimmu da al-amarimmu, kuma khalifanci bayan bayan bayan manzon All..(s) ta kasance khalifancin annabi, kuma mai rahama, amma a yau ta zama mulki na zalunci, wato wanda ya sami rinjaye ya ci.. …}.

Wannan kadan Kenan daga wasikar da sahabbai muhajirun suka rubutawa suran sahabban a wasu wurare, kuma Ibn Kutaiba ya kawo ta a cikin littafinsa Al-imama wassiya shafi na 35.

Sannan wadan wasikar ta ambaci abubuwa da dama wadanda suka fadawa daular musulunci da musulmi saboda mulkin Uthman.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 
  • Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC
  •  Manyan Malaman Roman Katolika Sun Fara Taron Zabar Paparoma
  • Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok
  • Sama Da Masu Sayayya Daga Ketare 220,000 Ne Suka Halarci Bikin Baje Kolin Canton Karo Na 137
  • Ƴansanda Sun Kama Ƴan Daba 33 A Kano
  • Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi
  • Al-Shara Ya Ki Abincikewa Da Tsarin Tarayya Wanda Kurdawan Kasar Siriya  Suke Bukata
  • Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 115
  • Kissoshin Rayuwa: Imam Al-Hassan 114