Turkiya:Fiye Da’Yan Adawa 300,000 Su Ka Yi Zanga-Zanga Nuna Kin Jinin Tayyib Ordugan
Published: 22nd, March 2025 GMT
KAmfanin dillancin labarun “al-Somariyya Newas” ya ambato jagoran ‘yan hamayyar siyasa na kasar Turkiya Uzgor Auzal yana fadin cewa: A daren jiya juma’a adadin wadanda su ka fito Zanga-zangar nuna kin jinin shugaba Rajab Tayyib Urdugan sakamakon sauke da kama ‘yan hamayyar siyasa da ya yi kaga kan mukamansu da su ka hada da magajin garin birnin Istanbul.
Magajin garin Istanbul Imam Uglu ya yi watsi da duk wata tuhuma da aa yi masa ta hannu a cin hanci da rashawa.
Kamfanin dillancin labaran “Reusters” ya nakalto wata majiyar shari’a tana cewa Imam Uglu ya yi watsi da dukkanin thume-tuhumen da aka yi masa masu alaka a cin hanci da rashawa.
Shi dai Imam Uglu zai tsaya takarar shugabancin kasa da Urdugan, kuma ana tsinkayo cewa zai iya lashe zabe.
Jami’ar adawa da Imam Uglu ya fito daga cikinta “ Turkish Republican Party” ta yi Allawadai da kama Imam Uglu, tare da bayyana shi da cewa, bi ta da kulli ne na siyasa kawai.
Bayan kama Imam Uuglu Zanga-zanga ta barke a cikin birane da garuruwa mabanbanta na kasar ta Turkiya tare da yin tir da abinda ya faru.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tallafin matar Tinubu na N1bn ga ’yan gudun hijirar Binuwai ya bar baya da kura
Da alama tallafin da matar Shugaban Kasa, Sanata Remi Tinubu ta ba wadanda hare-haren jihar Binuwai ya raba da muhallansu na Naira biliyan daya ya bar baya da kura.
Kwana daya da bayar da tallafin, ’yan gudun hijirar sun fito suna zanga-zangar yunwa, amma kakakin hukumar bayar da agaji ta jihar (SEMA), Terna Ager, ya ce musu kudin ba na sayen abinci ba ne.
Remi Tinubu ta bai wa waɗanda harin Benuwe ya shafa tallafin Naira biliyan ɗaya Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin TarayyaAminiya ta rawaito yadda Sanata Remi a ranar Talata ta ziyarci jihar inda ta mika wa Gwamnan Jihar, Hyacinth Alia tallafin kudin, a madadin ’yan gudun hijirar.
To sai dai kwana daya bayan hakan, sai wasu daga cikin ’yan gudun hijirar suka fantsama a kan tituna suna zanga-zangar yunwa da zargin masu kula da sansanin da gallaza musu tun da suka tare a can.
Mutanen dai sun tare babbar hanyar Makurdi zuwa Lafiya suna rera wakoki irin su “Gida muke so mu koma,” “Yunwa ta dame mu” da kuma “Matanmu na rasa ’ya’yansu suna yin bari”.
Daya daga cikin matan mai suna Rebecca Awuse, ta shaida wa ’yan jarida cewa, “Yunwa ta ishe mu. Ba mu da abinci, ba muhalli, ba magani sannan ba kulawar lafiya. ’Ya’yanmu na mutuwa da yunwa. Mata da yawa sun yi bari saboda yanayin da suke ciki sannan a kasa muke kwana.
Sai dai da yake mayar da martini, Terna Ager, ya yi zargin cewa akwai wata boyayyar manufar siyasa a zanga-zangar.
A cewarsa, “Babu dalilin da zai sa su yi wannan zanga-zangar sam. Wadanda ke sansanin Yelwata wani lokacin sukan koma sansanin Makurdi an fi samun tallafin abinci a can.
“Tallafin da matar Shugaban Kasa ta bayar na sake tusgunar da su ne ba wain a sayen abinci a raba musu ba ne. Kuma hakan ma yana daukar lokaci.
“Na yi imanin suna zanga-zangar ce saboda suna tunanin za a debi kudin kawai a raba musu, amma ba haka ba ne dalili,” in ji shi.