Aminiya:
2025-08-01@08:14:43 GMT

Dakatar da Gwamnan Ribas zubar da ƙimar Nijeriya ne a idon duniya — Jonathan

Published: 22nd, March 2025 GMT

Tsohon Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ya ce dakatar da Gwamnan Ribas, Similanayi Fubara da aka yi kwanan nan zubar da ƙimar ƙasar ne a idon duniya.

Tsohon shugaban ya ce ba daidai ba ne dakatar da Gwamnan Ribas da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da ’yan majalisar dokokin jihar, wanda Shugaba Bola Tinubu ya yi a makon jiya.

An ayyana zaman makoki na kwana uku bayan kashe mutum 44 a Nijar An yi wa wata karya tiyatar ceton rai

Channels TV ta ruwaito Jonathan yana bayyana haka yayin da yake jawabi a matsayin shugaban taro wanda gidauniyar Haske Satumari ta shirya a ranar Asabar a Abuja.

Jonathan wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa ne, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan matakin na cire zaɓaɓɓun shugabanni da aka yi.

“Wannan matakin da aka ɗauka zai ɓata sunan Nijeriya ne a idon duniya,” in ji shi.

Jonathan ya ce duk da cewar akwai buƙatar ɗaukar matakan da za su magance rikicin siyasar da ya dabaibaye Jihar Ribas na tsawon lokaci, a cewarsa dakatar da waɗanda mutane suka zaɓa a matsayin shugabanninsu bai dace ba.

Ya ƙara da cewa ya san bai kamata a matsayinsa tsohon shugaban ƙasa ya cika maganganu barkatai a game da abubuwan da suke a ƙasar ba, amma “yadda ake kallon Nijeriya yana ta’allaƙa ne a kan matakan ɓangaren zartaswa da majalisa da na shari’a suka ɗauka,” in ji shi.

A farkon makon da muka yi bankwana, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa dokar ta ɓaci a Jihar Ribas, ya kuma dakatar da gwamna da mataimakiyarsa da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Ribas Siminalayi Fubara

এছাড়াও পড়ুন:

Tsohon Ɗan Takarar Mataimakin Gwamnan Kaduna Na PDP Ya Koma ADC

Sai dai ya gode wa PDP bisa damar da ta ba shi ya tsaya takara a 2023, amma yanzu lokaci ya yi ne da zai yi gaba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Kwastan Da Shekara Ɗaya
  •  Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa  Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI
  • Majalisar Kasa Na Duba yiwuwar Dawo Da Gwamnan Jihar Rivers Fabura Kafin Cikar Wa’adin Watanni Shida.
  • Gidauniyar ‘Ya’yan Sarakunan Arewa Sun Marawa Sarkin Musulmi A Matsayin Shugaban Majalisar Sarakuna
  • Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu
  • Shugaban SUBEB Yayi Alkawarin Bayar Da Tallafin Ilimi A Jihar Nasarawa
  • Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar da Manufar Sauyin Yanayi
  • Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano Ya Kammala Rahoton Aikinsa Na Wucin Gadi
  • EU Tace Zata Dakatar Da HKI Daga Cibiyar Bincikenta Saboda Gaza
  • Tsohon Ɗan Takarar Mataimakin Gwamnan Kaduna Na PDP Ya Koma ADC