Rundunar PLA Ta Kaddamar Da Atisaye A Yankunan Tsakiya Da Kudancin Zirin Taiwan
Published: 3rd, April 2025 GMT
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.এছাড়াও পড়ুন:
Shugabannin Kudancin Kaduna za su karrama Janar Christopher Musa
Majalisar Shugabannin Kudancin Kaduna (SKLC) ta kammala shirye-shirye domin gudanar da gagarumar tarbar ga tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya).
Za a yi bikin ne domin tunawa da kyakkyawar rawar da majalisar ta ce ya taka a aikin soja da kuma hidimarsa ga kasa.
An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aureAn shirya gudanar da bikin ne a ranar Asabar, 22 ga watan Nuwamba, 2025, a Babban Filin Wasan na garin Kafanchan, cibiyar kasuwancin Kudancin Kaduna.
A yayin taron majalisar karo na 19 da aka gudanar a Kafanchan, Shugaban SKLC, Ishaya Dare Akau, ya ce za a ba Janar Musa lambar yabo mafi girma ta majalisar wato GCSK.
Akau, ya ce wannan karramawar tana nuni da yadda Janar Musa ya wakilci Kudancin Kaduna, Jihar Kaduna, da Najeriya baki daya cikin kwarewa da cancanta, inda ya bayyana shi a matsayin jakada nagari.
A yayin taron, majalisar ta kuma kaddamar da kwamitin kula da harkokin kudi na Bikin Gargajiya na Shekara-shekara na Kudancin Kaduna (SKFEST), inda aka nada Shugaban Hukumar Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS), Comrade Jerry Adams, a matsayin shugaban kwamitin.
Manyan jami’an gwamnati da dama sun halarci taron karkashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Henry Danjuma Magaji, tare da Mai ba Gwamna shawara kan harkokin siyasa, Hon. Ado Dogo Audu.
Sun yi wa majalisar bayani kan muhimman shirye-shiryen gwamnati, ciki har da amincewar da gwamnatin tarayya ta bayar na farfado da aikin gina hanyar Jere–Kagarko–Jaba–Kwoi–Kafanchan, wadda Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya taimaka wajen ganin tabbatuwarsa.