Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta yi ƙarfi — Muftwang
Published: 3rd, April 2025 GMT
Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, ya yi gargaɗin cewa Najeriya ta yi kuskure a baya wajen barin Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ’yan bindiga har suka yi ƙarfi.
Ya jaddada cewa babu wata ƙungiya da ya kamata ta mallaki makamai ko ta samu ƙarfin guiwar ƙalubalantar hukumomin tsaro.
NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16mDa yake jawabi a Abuja yayin ƙaddamar da jiragen yaƙi marasa matuki da bama-baman da aka ƙera a Najeriya, wanda kamfanin Briech UAS ya samar, Mutfwang ya buƙaci haɗin gwiwa da kamfanonin fasahar tsaro na cikin gida.
“Dole ne mu tabbatar da cewa babu wata ƙungiya da ke iya ƙalubalantar hukumomin tsaronmu,” in ji Mutfwang.
“Najeriya ba za ta sake yin kuskuren barin ‘yan ta’adda su sake yin irin wannan ƙarfi ba.”
Ya yaba wa sojoji kan ƙoƙarinsu na inganta tsaro a Jihar Filato: “Saboda amfani da fasaha da ƙoƙarin jami’an tsaro, Filato ta fara dawo da sunanta a matsayin waje mai zaman lafiya da yawon buɗe ido.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda Boki Haram Muftwang
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa irin wannan magana ta Trump cin mutunci ce ga ’yancin Najeriya.
Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan AmurkaDon haka malamin ya yi kira da a ɗauki matakin diflomasiyya cikin gaggawa.
“Trump ya yi barazana ga ƙasa mai cin gashin kanta da harin soja, wannan girmamawa ne ga ƙasarmu,” in ji Gumi.
Sheikh Gumi, ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kira Jakadan Amurka domin neman bayani da kuma a janye wannan barazanar, inda ya yi gargaɗin cewa idan ba a yi haka ba, to Najeriya ta yanke hulɗa da Amurka.
“Shugaba Tinubu ya kamata ya kira Jakadan Amurka idan ba su janye barazanar ba, to mu yanke hulɗa da wannan gwamnati mara mutunci,” in ji shi.
Gumi, ya kuma jaddada cewa Najeriya tana da damar bunƙasa tattalin arziƙinta ba tare da dogaro da Amurka ba.
“Akwai hanyoyi da dama da za mu iya faɗaɗa tattalin arziƙinmu da ƙarfafa haɗin kan soji ba tare da dogaro da su ba,” in ji Gumi.