Aminiya:
2025-09-17@21:47:42 GMT

An fara shigar da kayan agaji a Gaza

Published: 29th, July 2025 GMT

An fara shigar da kayyakin agaji zuwa Zirin Gaza wadanda galibi ta sararin samaniya aka rika jefawa da jirage daga kasashen Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Arshiyan Kohen, kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila ya ce, za a dakatar da farmakin soji na tsawon sa’o’i 10 a kowace rana a wasu sassan Gaza tare da ba da damar samun sabbin hanyoyin ba da agaji.

DW ya ruwaito cewa ana ci gaba danka kayayyakin tallafin a hannun kungiyoyin agaji na kasa da kasa da suke ci gaba da ayyukan rarrabasu.

Tinubu ya bai wa ’yan ƙwallon Nijeriya mata kyautar kuɗi da gida da lambar yabo An kashe ’yan ta’adda 45 a Neja

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteress ya siffanta wannan matakin da mai sanyaya zuciya bayan damuwa da bala’in da mazauna Gaza suka tsinci kansu a ciki, yana mai fatar gaggauta shigar da kayayyakin agajin da kuma dorewarsa.

A yayin taron tattaunawa kan matsalolin da suke shafar ayyukan samar da abinci a Afrika ne Guterres ya faɗi  cewa yunwa ba za ta taɓa zama makamin da za a yi amfani da ita wajen yaƙi a duniya ba.

Babban jami’in bayar da agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya, Tom Fletcher ya yi maraba da matakin, yana mai cewa yanzu haka yana tuntubar kungiyoyi wadanda za su yi duk mai yiwuwa don isa ga mutane da dama da ke fama da yunwa a wannan lokaci.

Tuni dai kungiyoyin agaji suka gabatar da wasu korafe-korafe tun ba a yi nisa ba, don yi wa tufkar hanci muddin ana son kwalliya ta biya kudin sabulu a ayyukan agajin da aka fara bayan fiye da watanni uku da dakatar da su.

Ahmad Nadir, na kungiyar lafiya ta duniya WHO, ya ce tsame hannun Isra’ila daga batun karba da rabon kayan agaji ne kadai zai bai wa kwarraru kan ayyukan agaji damar gudanar da ayyukan da za a samu nasara.

A bayan nan ne Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP ta ce kashi uku na al’ummar Gaza ba su ci abinci na kwanaki ba, kuma mutane 470,000 suna cikin yanayi na juriyar tsananin yunwa wanda tuni ya kai ga mutuwar wasu.

Isra’ila dai na ci gaba da fuskantar suka daga kasashen duniya, kan amfani da yunwa a matsayin makamin yaki kan al’ummar Falasdinu, lamarin da gwamnatin kasar ta ki amincewa da shi.

Akwai yunwa ta gaske a Gaza —Trump

Ko a wannan ɗin Litinin Shugaban Amurka Donald Trump ya ce “akwai yunwa ta gaske” a Gaza.

Shugaban na Amurka ya faɗi hakan ne bayan Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nace kan cewa babu yunwa a yankin.

Da aka tambaye shi ko ya yarda da abin da Netanyahu ya fada cewar “ƙarya ce tsagwaronta” idan aka ce Isra’ila na ta’azzara yunwa a Gaza, shugaban na Amurka ya ce: “Ban sani ba…amma yaran nan da ka gan su, suna cikin yunwa…wannan yunwa ce ta gaske.”

Kalaman Trump na zuwa ne bayan shugaban hukumar kai agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce ana buƙatar abinci mai “ɗimbin yawa” domin magance halin yunwa da yankin ke ciki.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yunwa Majalisar Dinkin Duniya

এছাড়াও পড়ুন:

Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa

Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce fiye da sojojin kasar 20,000 ne suka ji rauni tun farkon yakin da aka fara a Gaza a watan Oktoba 2023, inda fiye da rabinsu ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa, ciki har da ciwon damuwa.

A cewar sashen bayar da shawarwari na ma’aikatar, kusan kashi 56 cikin 100 na wadanda suka ji rauni sun kamu da wasu matsalolin lafiyar kwakwalwa, wanda ke nuna irin tasirin matsalar kwakwalwa da wannan rikici ke haifarwa.

Ma’aikatar ta kara da cewa kusan kashi 45 cikin 100 na wadanda suka ji rauni suna fama da raunuka a jiki, yayin da kashi 20 cikin 100 na sojojin ke fama da matsalolin kwakwalwa da na jiki a lokaci guda.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki September 14, 2025 An Zabi Issa Tchiroma A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A Kamaru September 14, 2025 Kasar Iran Ta Yi Fatali Da Zarge-Zargen Da Kungiyar G7 Da Kawayenta Suka Yi Kanta September 14, 2025 Iran Ta Bayyana Shirinta Na Halartar Taron Shekara-Shekara Na Hukumar Makamashin Nukiliya September 14, 2025 Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Bayyana Rashin Halarta Tawagarta A Kada Kuri’a Kan Batun Falasdinu   September 14, 2025 Tsananin Masifar Da Falasdinawa Ke Ciki A Gaza Saboda Hare-Haren Gwamnatin Mamayar Isra’ila September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa  Kisan Kiyashi A Gaza
  • Hamas Ta Karyata Gwamnatin Mamayar Isra’ila Kan Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta
  • Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila
  • Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza
  • Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza
  • Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa