Amurka Ta Daba Wa Kanta Wuka Bisa Karin Harajin Da Ta Yi
Published: 3rd, April 2025 GMT
Sanin kowa ne, ciniki mai inganci na bukatar kasuwa mai ‘yanci, da takarar da ake yi cikin daidaito, gami da manufa mai dorewa. Idan kasar Amurka ta ki samar da wadannan abubuwa, to, babu wani abun da za a yi, in ban da mai da kasar saniyar ware, da kara tabbatar da hadin kai tare da sauran abokan hulda.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Araqchi: Iran Zata Mayar Da Martanin Da Ba Zai Yiwu A Boye Ba Kan Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kanta
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Idan aka maimaita ta’asar kai hari kan Iran, za ta mayar da martani ta hanyar da ba za a iya boyewa ba
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya mayar da martani kan barazanar da jami’an Amurka suka yi a baya-bayan nan, inda ya ce idan aka sake kai hari kan Iran, za ta mayar da martani mai tsauri wanda ba zai yiwu a iya boye ba.
Araghchi ya kara da cewa a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin din nan cewa: Iran, kasar da ke da al’adun gargajiyar da ta shafe shekaru dubu bakwai na wayewar kai, ba za ta taba mika kai ga barazana da tsoratarwa ba. Iraniyawa ba su taba mika kai ga kasashen waje ba kuma ba su bukatar komai sai girmamawa.
Ya ci gaba da cewa: “Iran ta san hakikanin abin da aka yi mata da kuma abin da makiya suka fuskanta a lokacin farmakin da ‘yan sahayoniyya da Amurka suka yi a baya-bayan nan, ciki har da yawan munanan hare-haren da ta kai a matsayin daukan fansa wadanda ake ci gaba da boyewa. Don haka idan makiya suka sake kuskuren kai hari kan Iran, babu shakka zasu fuskanci martani mai gauni da ba zai yiwu a iya boyewa ba.