Takht Ravanji: Iran Ba Za Ta Taba Yin Tattaunawa Akan Dakatar Da Tace Sanadarin Uranium Ba
Published: 28th, April 2025 GMT
Mataimakin ministan harkokin waje mai kula da bangaren siyasa, ya bayyana cewa; Ko kadan ba a bijiro da batun dakatar da tace sanadarin uranium a Iran ba, ko kuma batun makamanta masu linzami.
Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya tabbatar da cewa, wadannan abubuwan biyu wato dakatar da ci gaba da tace sanadarin uranium da kuma makamai masu linzami, jan layi ne da jamhuriyar musulunci ta Iran ba za ta bari a ketara su ba ba kuma za ta bari a bude tattaunawa akansu ba.
Kwamitin da yake kula da tsaron kasa da kuma siyasar waje a majalisar shawarar musulunci ta Iran a karkashin jagorancin dan majalisar Ibrahim Ridhazi ya yi taro a ranar Lahadin da ta gabata, inda aka gayyaci mataimakin ministan harkokin wajen domin jin ta bakinsa akan abubuwan da suke faruwa a tattaunawar da ake yi ba kai tsaye ba da Amurka.
Ridha’i ya fada wa ‘yan jarida cewa Takht Ravanji ya kammadar da rahoto akan yadda tattaunawar take gudana a tsakanin Amurka da Iran da kasar Oman take shiga Tsakani.
Haka nan kuma ya ce; Tace sanadarin Uranium a cikin gida wani jan layi ne da ba za a tsallake shi ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Pezeshkian: Tunanin Kawo Karshen Shirin Nukiliyar Iran Ya Yi Kama Da Tabuwa
Shugaba Masoud Pezeshkian ya yi watsi da hankoron Amurka na tunzura kawayenta, musamman gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, na yunkurin kawo karshen shirin nukiliyar Iran.
Shugaban an Iran ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Aljazeera na kasar Qatar a wannan Talata, inda ya bayyana cewa, za a ci gaba da inganta sinadarin Uranium a kasar Iran nan gaba bisa tsarin dokokin kasa da kasa.
Wannan yunkuri yasa an ga bangarorin biyu na Amurka da Isra’ila suna matsa lamba a kan sauran bangarori na duniya, tare da bayyana Shirin na Iran a matsayin mai matukar hadari ga duniya, da nufin samun goyon bayan kasashen duniya kan bakaken manufofisu a kan kasar ta Iran.
Dangane da zargin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan Shirin Iran da kuma neman samoma kansa hujjoji na kaiwa Iran hari, da kuma bayyana cewa harin Amurka ya kawo karshen Shirin Iran na nukiliya, Pezeshkian ya ce, “Da’awar cewa shirinmu na nukiliya ya kawo karshe, batu ne na yaudara.”
“Ilimin nukiliya yana a cikin kwakwalen masananmu ne na kimiyyarmu, ba a cikin wurarenmu ba.” In ji Pezeshkian.
Haka nan kuma shugaban na Iran ya sake nanata matakin kin amincewa da zargin kasarsa da hakoron kera makaman kare dangi, da kuma kara jaddada matsayin kasar na ci gaba da daukar matakan da take yi wajen kara inganta shirinta na makamashin nukiliya domin ayyukan farar hula.
Pezeshkian ya kuma sake nanata shirye-shiryen Iran na yin shawarwarin da ba su ginu a kan haramtawa Iran hakkinta na inganta na tace sanadarin Uranium ba, amma ya ce “duk wata tattaunawa da za a yi a nan gaba dole ne ta dogara a kan batutuwa na masu tabbatar da hakkokin Iran.