Fira Ministan Indiya Ya Bayyana Cewa: Iran Tana Kokari A Fagen Inganta Zaman Lafiya A Yanki Da Duniya Baki Daya
Published: 27th, April 2025 GMT
Fira ministan Indiya ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana kokari da zage dantse wajen taimakawa a fagen inganta zaman lafiyar yanki da na duniya baki daya
Fira ministan Indiya Narendra Modi ya yaba da rawar da Iran ta taka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, yana mai cewa: Gwamnatin Indiya tana goyon bayan kokarin Iran na karfafa zaman lafiya a yankin da ma duniya baki daya, yana mai jaddada bukatar warware takaddama ta hanyar diflomasiyya, ciki har da na Iran da Amurka.
Har ila yau fira ministan na Indiya ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da abin da ya faru a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke lardin Hormozgan a kudancin kasar Iran, ya kuma bayyana cewa kasarsa a shirye take ta ba da duk wani taimako ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Modi ya bayyana kyakkyawar fatansa na lafiya da burinsa ga shugaban kasar Iran da jagoran juyin juya halin Musulunci da kuma ci gaba da wadata ga al’ummar Iran masu girma.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Da Tawagarsa Sun Isa Kasar Brazil Don Halartar Taron BRICS Karo Na 17
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya tafi kasar Brazil don halartar taron BRICS karo na 17
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya sanar da isar ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a birnin Rio de Janeiro domin halartar taron kasashe mambobi a kungiyar BRICS karo na 17.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Baqa’i ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Tawagar kasar Iran karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi za ta halarci taron kasashen BRICS.
Baqa’i ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa: “Sun isa birnin Rio de Janeiro na Brazil, domin halartar taron kasashen BRICS karo na 17.”