Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (2): Kyawawan Dabi’u Ke Fayyace Tsoron Allah A Musulunci
Published: 11th, April 2025 GMT
-Mun lura da ilimomin harkokin zamaninmu a cikin Alkur’ani
Cikin godiyar Allah, muna mika ziyara ga Shehu Isma’ila Umar Almadda (Mai Diwani) da kuma ban gajiya da gabatar da Tafsirin Alkur’ani mai girma na Azumin Ramadan na bana. Allah ya kai mu na badi albarkar Annabi (SAW) da Shehu (RTA).
Ya Shehi, a Tafsirinka na rana ta bakwai mun ji yadda ka yi bayani na ilimomin kiyaye hadurran hanya da ke kunshe a cikin aya ta 63 ta Suratul Furkan (Sura ta 25), “Wa Ibadur Rahman…”.
Mun kara fahimtar cewa, ayar tana nusarwa a kan tafiya cikin tsari walau sufuri ne na titin mota, ko na jirgin sama ko na ruwa ko jirgin kasa, da dukkan alamomin da ake sakawa na gane hanya da kiyaye aukuwar hadurra na ganganci da sauran ilimomin da suka kunshi dokokin hanya, duka suna nan a karkashin fahimtar ayar. Allah ya saka da alkhairi.
Game da sunan Allah na “Arrahmanu” kuwa, ya kara nuna mana cewa ya kunshi kowane ilimi. Kuma duk masana na sunan na “Arrahmanu” su ne suke zama kwararru na kowane fanni da ke tafiya a kan kasa cikin ilimi da kwarewa. Wallahi, wannan yana nuna mana cewa, mu al’umma musamman ta musulmi mu dage da neman ilimi na kowane fanni saboda inganta rayuwa da aiki da ilimin wajen nuna sanin ya kamata.
Daga misalan da ka kawo na batun hanya, na fahimci cewa, idan alamar hanya ta jar danja ta tsayar da direba shi kuma ya ki tsayawa, ya nuna jahilci ko rashin aiki da ilimin, wanda hakan ne yake sa jami’an da abin ya shafa suke hukunta direbobi masu karya dokokin hanya. Su kuma jami’an, yadda suke fara tambayar mai laifin a game da shin yana da lasisin tuki domin tantance cewa, shi a cikin “Ibadur Rahman” yake ko kuma jahili ne. Idan jahili ne hukuncinsa daban, idan kuma wanda ya san abin ne, watau yana daga cikin “Ibadur Rahman”, har yana da lasisi to hukuncinsa ma yakan fi tsanani, duka ya fahimtar da mu cewa muna da komai a cikin Alkur’ani.
Allah ya saka maka da alheri bisa yadda kuma ka karfafa gwiwar masu mulki har ma da magidanta a kan koyar da duk wadanda suke karkashinsu ilimi, domin tabbas jahilci tamkar mutuwa yake. Idan an ba mutane ilimi shi ne zai zama an raya su, haka nan idan an bar su da jahilci to kuma babu makawa an kashe su.
Muna godiya ya Shehi, Allah ya kara lafiya da nisan kwana.
-Tabbas Ya Kamata Mu Zurfafa Bincikenmu A Cikin Alkur’ani Domin Samun Ci Gaba
Assalamu alaikum. Ya Sayyadi barkanmu da kammala watan Azumin Ramadan, Allah ya amsa ibadunmu ya sa muna cikin ‘yantattun da aka ‘yantar, amin. Hakika bayanin da ka yi a kan yadda ya kamata mu al’ummar musulmi mu kara zurfafa bincike a cikin Alkur’ani domin samar da ci gaban zamani da ake gani a ko ina cikin duniya babban lamari ne mai matukar muhimmanci da ya kamata kasashenmu na musulmi mu mayar da hankali a kai.
Musamman ma, mu kasashen Afirka da muka zama koma baya idan aka kwatanta da sauran yankuna na duniya, ya kamata mu su sake nazarin wayewar zamani da ke kunshe cikin Alkur’ani, wanda hakan zai sanya mu iya yin kafada-da-kafada da manyan kasashen duniya irin su Amurka da China ta fannin ci gaban zamani.
Duk wanda ya san tarihi da kuma ilimi, ya san cewa duk bayanan da wadannan kasashen da suka ci gaba suke takama da su da kundayen da suka mallaka na bayanan ilimi muna nan da su a cikin Alkur’ani, abin da ya kamata a yi shi ne mu fadada bincike na fahimtar zamani a cikin Alkur’ani wanda hakan zai bai wa mu Afirka damar yin kirkire-kirkire da gudanar da sabbin ayyuka na ci gaban zamani.
Yana da kyau yadda muke da yawan mahaddata a Nijeriya, ya zama kasar ta zamo kan gaba wajen zama abar koyi a fannin kawo ci gaban zamani a Afirka da kuma inganta rayuwar ‘yan Afirka. Muna da yakinin cewa, in dai an sa hakan a gaba, tabbas nan da shekaru masu zuwa za mu iya cimma duk burin da muke so mu ga mun cimmawa.
Kuma har ila yau, mun ji dadi a kan kiran da ka yi na a sake nazarin wasu abubuwa na shari’a da ba su da asali a ainihin nassin da Allah ya saukar, domin tabbas abubuwan da Allah ya haramta da hukuncinsa (Muharramatu) kuma ya kulle su da hukunce-hukunce (Muhkamatu) babu wanda ya isa ya kara ko ya rage, kuma Allah bai bar su a dunkule ba, ya yi bayaninsu dalla-dalla.
Yadda aka fara shigo da abubuwa cikin addinin nan tun daga zamanin Sahabbai ya rikita abubuwa da yawa. Wannan ba rashin kunya ba ne ko kadan, muna girmama dukkan Sahabbai wallahi, kuma a cikinsu ne wasu suka tsawatar a kan shigo da abubuwa cikin addinin. Ga misalin Hadisin Ka’abu bin Malik, lokacin da wasu matasa suka ziyarce shi, suka yi masa kirarin girmamawa, suka bukaci ya yi musu hira daga cikin rayuwarsa tare da Annabi (SAW), wanda ya ce, musu “in kun ji na yi shiru ku ma ku yi shiru, yadda kaina ya yi fari (furfura) haka kwakwalwata ta yi, kuma abubuwa ne na yadda muka yi rayuwa da Rasulullahi (SAW). Bari na fada muku duk sai da aka canja su face Sallah (kadai), ita ma ga ta nan kun fara canzawa”. Duk wannan ya nuna cewa, ya kamata mu dawo kan turba ta asali.
Allah ya saka da alkhairi, ya Sayyadi. Wallahi muna godiya sosai, domin mun kuma karu da bayanai a kan abubuwan da Shari’a ke kewayawa a kansu na batun da ya shafi daukar kudi daga nan zuwa nan kamar rabon gado; da tsara Iyali da yadda za a yi aure da rabuwarsa da yadda za a yi tarayya a cikin dangi; da ukuba da hukunci a tsakanin abokan hulda. Haka nan, sauran harkoki irin su kokarin tabbatar da zaman lafiya wanda ya kunshi yadda ake shirya yaki, da sulhu, da zaman lumana; da batun riba da ke bayani a kan tsarin yadda za a gudanar da kasuwanci, sai kuma abubuwan da suka shafi dabi’o’i na ‘yan’adam.
Hakika duk sauran abubuwan da ba wadannan ba, Shari’a ta bar mutane su yi hukunci da abin da ke zamaninsu, na daga kundin tsarin mulki da ake shimfidawa don maslahar al’umma wajen habaka tattalin arziki da raya kasa.
Allah ya kara ilimi da fahimta a cikin wannan addini mai fadi da Manzon Rahama, Annabi (SAW) ya zo mana da shi domin tseratar da al’umma duka sai dai wanda ya ki. Mun gode.
Sako daga Malam Miftahu Adam Zariya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Manzon Allah SAW Ramadan
এছাড়াও পড়ুন:
Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan Almujtaba (a) 110
110- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan. Da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu.
///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan lamami na biyu daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (s) diyar manzon All..(s).
Idan kuna tare da mu, masu sauraro a cikin shirimmu da ya gabata, mun yi cikekken bayani dangane da rayuwar Abdullahi dan Abi sarkh, wanda ya Khalifa Uthman ya sanya wali ko gwamna a kan mutanen kasar Masar, da kuma yadda suka kai kararsa wajen Khalifa, amma Khalifa ya rubuta wasiya ya ja kunnensa, sannan ya bukaci ya sauya halayensa, amma ba wai kawai ya ki sauya halayensa ba sai dai ya kashe wanda ya kai kararsa gaban Khaliga.
A nan su mutanen kasar Masar suka fusata suka tura mutane 700 zuwa madina inda suka nemi shawarar wasu daga cikin sahbban manzon All..(s), daga ciki har da Aliyu dan Abitalib (s) wanda ya shiga wajen Khalifa ya yayi masa magana, kuma ya amince ya sauya masu gwamnansu, sai yace su zabi wanda suke so, sai suka zabi Muhammad dan Abubakar.
Mun kuma bayyana yadda aka haifeshi a hajjin bankwana, kuma yana dan watanni 3 a duniya manzon All..(s) ya kauracewa duniyar, sannan baya rasuwar Khalifa a Abubakar, yana mai yuwa dan shekara 3-4 mahaifiyarsa ta gama idda sai Amirulmuminina (a) ya aureta.
Don haka Muhammad dan Abubakar yana dan shekara kimani 26 a duniya khalifa Uthman ya sanyashi gwamnar Madina, amma abin mamaki shi ne sun isa wani gari ana kiransa Hums a kan hanyar masar sai suka gamu da wani bawan Uthman dauke da wasika daga wajensa zuwa wajen Abdullahi dan Abi sarkh, inda a ciki ya bukaci ya kashesu gaba daya har tare da sabon Gwamnan. Amma sun lura cewa rubutun hannun Marwan dan Hakam ne.
Daga nan sai suka kama wrsh bawan Uthman da kuma wasikar da suka samu a wajensa suka shiga madina. Suka nunawa Amirulmuminina wasikar, ya karbeta ya shiga wajen Uthman, sannan ya nuna masa wasikar ya kuma tambayeshi ko shi ne ya rubuta? Sai yace a’a, sai ya tambaye shi wa kake tuhuma, sai ye babu wanda yake tuhuma.
A nan ce sai ya koma gida ya kama gidansa ya kulle, don ya san cewa fitina zata auku.
Don haka mutanen masar sun yiwa gidan Khalifa a Madina Kawanya, babu wanda ya taimaka masa cikin dimban sahabban manzon All..(s), sun barshi da yan tawaye wadanda suka yiwa gidansa kawanya suka hana shigar ruwa da abinci cikin gidan.
Kafin mu dawo kan wannan, bari mu dubi yadda Khalifa Uthman ya wanye da Abdullahi dan Masaud daya daga cikin manya-manyan sahabban manzon All..(s), wanda kuma manzon All..(s) da kansa ya yabe shi so sai. Ance shi ne mutum wanda yafi kama da manzon All..(s) a shiriyarsa sa da shirunsa. Kuma manzon All.. (s) yana fada dangane da shi, (wanda yake farinciki ya karanta Al-kur’ani a asalinsa da kuma danyensa kamar yadda aka sauko da shi, to yayi karatu da irin karatun dan Mas’udu).
Sannan wasu mutane sun yabe shi a gaban Amirulmuminina (a) sai yace : {Ni ma zan fada dangane da shi kamar yadda suka fada, yana daga cikin wadanda suka fi kowa iya karatun Kur’ani, ya halatta abinda ya halatta,ya kuma haramta abinda ya haramta, malami ne a sanin addini, ya san sunnar manzon All..(s) , yana daga cikin wadanda wannan ayar ta sauka tana yabonsu,
{Waɗanda suka karɓa kira zuwa ga Allah da ManzonSa, daga bãyan cuta ta sãme su. Akwai wata lãda mai girma ga waɗanda suka kyautata yi daga gare su, kuma suka yi taƙawa.} Ali Imrani aya ta 172. Har ila yau yana daga cikin wadanda wannan ayar ta sauka.
{Kuma kada ka kõri waɗanda suke kiran Ubangijinsu sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa, babu wani abu daga hisãbinsu a kanka, kuma babu wani abu daga hisãbinka a kansu, har ka kõre su ka kasance daga azzãlumai.} Al-Anam 52.
Lalle Abdullahi dan masaud yana daga cikin manya manyan musulmi a zamanin manzon All..(s) a wajen shiriya, da kyawawan ayyuka,da kamun kai, don rikonsa da addini ne ya sa Khalifa Umar ya turashi zuwa Kufa tare da Ammar dan Yasir, sannan ya rubutawa mutanen kufa wasika inda a cikinta yake fada masu, (Lalle ya tura Ammar dan Yasir gareku a matsayin shugaba, da kuma Abdullahi dan Masa’ud Malami kuma mataimaki, suna daga cikin zababbun daga cikin sahabban manzon All..(s), suna daga cikin wadanda suka je yakin Badar, ku yi koyi da su, ku yi biyayya a garesu, ku ji maganganunsu, da zancensu, hakiki na zabi Abdullah gareku a kan kaina).
Don haka Abdullahi dan masa’ud ya zauna a kufa a tsawon khalifan Umar dan Khaddabi, wato shekari kimani 10, yana karantar da mutane addini, yana sanar da su littafin All..T, yana sanar da su ilmin addinin musulunci, yana nuna masu hanya madaidaiciya, tare da wannan ya kasance ma’ajin kudaden gwamnati a kufa.
A lokacinda Al-amura suka koma ga khalifa Uthman, sannan ya aika Walid dan Uqbah a matsayin wali a Kufa ! sai sabani ya shiga tsakaninsa da shi, kamar yadda muka yi magana a kan Walida an Uqbah a baya, wanda ya tilasta masa ajiye aikinsa na ma’ajin baitul Malin musulmi a Kufa.
Sai ya zauna a kufa kadan daga bayan ya koma Madina, a lokacinda zai tafi, sai mutanen kufa suka raka shi har bayan gari, don girmama shi da kuma bakin cikin rabuwa da shi. Suna fada masa a lokacinda suke bankwana da shi: All..ya saka maka da Alkhairi, ka sanar da Jahilai, ka karfafa ilmin malamammu, ka koya mana karatun Al-kur’ani, ka koya mana addini, madallah da dan’uwa musulmi irinka, madallah da aboki.
Sai yayin bankwana da su, ya kuma hanyarsa zuwa Madina, a shigo birnin a lokacin Khalifa Uthman yana khudaba a kan membarin manzon All..(s), a lokacinda Khalifa ya hango shi sai yana fadawa mutane yana kuma nuna shi, yana cewa : Ku saurara hakiku mummunan dabba ta zo maku, …..
Shin yakamata a zagi sahabin manzon All..(s) wanda bai aikata wani laifi ba, sai sabanin da ya samu da Walid dan Ukba, Sabon walin kufa wanda ya kha’inci All..da manzonsa kuma Ayar Alkur’ani ta sauka ta kira shi Fasiki, kuma yake satar kudaden musulmi!?.
Sai Ibn Mas’ud ya mayar masa da cewa: Ba haka bane, sai dai ni sahabin manzon All..(s), a ranar Badar da kuma bai’ar ridwan}. A lokacinda suka ji martanin Abdullahi dan Masa’ud sai wasu da dama sun tashi suna kareshi a gaban Uktman, daya daga cikinsu ita ce Aisha matar manzon All..(s) tana cewa : Ya kai Uthman kana fadar haka ga sahabin manzon All…(s)?
Sai Uthman ya bada umurnin aka fitar da Abdullahi dan masa’ud da karfi da kuma wulakanci. Sannan daya daga cikinsu, wanda ake kira Abdullahi dan Zam’ah ya daga shi ya buga da kasa, wasu sun ce wani ne ba shi ba, sannan ya dake shi a kan kirjinsa ya kuma karya masa awazarsa.
A lokacinda Imam Ali (a) ya ga haka, ko kuma ya ji labarin abinda aka yiwa Abdullahi dan Masa’ud ya zabura ya tashi yana daga murya yana cewa {Ya kai Uthman, ta yaya zaka yi haka da sahabin manzon All..(s) don abinda Walid dan Ukba ya fada maka dangane da shi?}.
Sai Uthman yace: Ba don Walid na yi masa haka ba, sai na aiki Zabaidah dan Sult Alkindi zuwa Kufa, sai dan masa’ud ya ce masa: Jinin Uthman ya halatta. Sai Imam Yace: Ya halatta a kan Zubaidah yayi haka ba tare da tabbatar da amincensa ba?
Sai Imam ya dauki dan Masa’ud zuwa gidansa yana jinyarsa. Sai Uthman ya yankewa dan Masa’ud baya zuwa wajensa, sannan ya sa aka dakatar da bashi albashinsa, sai ba’a dabe ba, dan Masaud ya yi rashin lafiyan da ya yi wafati a cikinta.
A lokacinda Uthman ya ji labarin rashin lafiyansa, sai ya zo gidansa, ya zauna kusa da shi, yana ce masa, menene damuwarka? Sai ibn Masa’ud yace: Zunubi na.
Sai yace: Me kakeso, sai yace, rahamar Ubangiji na, sai yace: Ba zan kira makama likita ba? Sai yace: Likitan ne ya sa ni rashin lafiya. Sai yace: In bada Umrni a maka kudadenka?: Sai yace: Ka hanani a lokacinda neka bukatarsa, sai ka bani shi a lokacinda bana bukatarsa? Sai yace: Sai ba barshi ga yayanka! Sai yace: Arzikinsu na hannun All..!
Sai Uthman yace: Ka gafarta mani ya baban Abdurrahman, Sai ibn Ma’ud yace: Ina rokon All.. ya karbammani hakkina daga gareka. Sai Uthman ya tashi ya tafi ya manta da shi.
Sannan a lokacinda ya kusan Mutuwa sai ya yi wasiyya kada Uthman ya sallaci gawarsa, sannan ya bukaci abokinsa Ammar dan yasir yayi mansa sallah idan ya rasu. Sannan bayan rasuwarsa Ammar da sauran salihan bayi suka yi masa sallah sannan suka sanyashi a bakiyah. A lokacinda Khalifa ya ji, ya yi fushi, sai ammar yace masa , wasiyya yayi kada ka yi masa salla.