NAJERIYA A YAU: Yadda Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Zai Shafi Rayuwar ’Yan Najeriya
Published: 11th, April 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A Najeriya ana tafka muhawara a kan yadda farashin ɗanyen man fetur yake ƙara faduwa a kasuwannin duniya.
Wannan lamari dai ya haddasa damuwa a zukatan wasu ’yan ƙasar, kama daga masana tattalin arziki zuwa jami’an gwamnati, kasancewar ɗanyen mai ne mafi muhimmanci a cikin hanyoyin samun kuɗaɗen shigar ƙasar.
Sai dai tambayar da wasu ’yan kasar suke yi ita ce: shin yaya wannan faɗuwar ta farashin ɗanyen mai za ta shafi rayuwar talaka?
NAJERIYA A YAU: Tasirin ’Yan Uwantaka Ga Rayuwar Al’umma DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne kan yadda faɗuwar farashin ɗanyen man fetur zai shafi ɗan Najeriya.
Domin sauke shirin, latsa nan: https://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16955648-yadda-fa-uwar-farashin-anyen-mai-zai-shafi-rayuwar-yan-najeriya.mp3?download=true
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ɗanyen mai faɗuwar farashi Najeriya Rayuwar Talaka
এছাড়াও পড়ুন:
Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce zai yi matuƙar wuya a samu shugaban da zai saita Najeriya, idan har Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka.
Shehu Sani, ya bayyana haka ne yayin hira a gidan talabijin na TVC, inda ya bayyana cewa Tinubu na da damar daidaita makomar Najeriya.
Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a fashewar tanka a Neja Waɗanda ke son rusa Kano ba za su yi nasara ba — Sanusi IIHar ila yau, ya ce nasarar Tinubu ko gazawarsa, za ta taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomar siyasar ƙasar nan.
“Idan Shugaba Bola Tinubu ya gaza, bana ganin abubuwa za su zo wa shugaban ƙasan da zai zo da sauƙi,” in ji shi.
Tsohon ɗan majalisar ya shawarci shugaban ƙasar da ya zaɓi mutane ƙwararru da za su taimaka masa wajen cika muradun ’yan Najeriya maimakon bai wa masu yi masa biyayya muƙamai.
Ya ce Tinubu ya kamata ya maimaita ire-iren tsarin da ya aiwatar a Jihar Legas, inda ya naɗa ƙwararru da suka taimaka masa wajen samar wa jihar ci gaba.
Shehu Sani, ya kuma soki yadda siyasar Najeriya ta koma mai cike da rashin jituwa.
Ya ce abun baƙin ciki ne yadda masu mulki da ’yan adawa ke yi wa juna kallon abokan gaba maimakon abokan samar da ci gaba.
Ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya ɗauki matakai da suka ƙunshi sauye-sauye, ko da kuwa wasu ba za su ji daɗin hakan ba, inda ya jaddada cewa kowace ƙasa da ta ci gaba ne ta hanyar sadaukarwa.
“Babu wata ƙasa da ta zama babba cikin sauƙi. Ƙasashe kamar China, Singapore, da Indonesia sun yi sadaukarwa kafin su cimma muradunsu,” in ji shi.