Ruwan Sama Ya Lalata Gidaje Sama Da 240 A Kebbi
Published: 11th, April 2025 GMT
Sama da gidaje dari biyu da arba’in ne aka lalata a daren Talatar da ta gabata, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe sa’o’i ana yi a unguwar Garin Kestu Atuwo dake karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi.
Da yake jajantawa wadanda abin ya shafa, Gwamna Nasir Idris ya shawarci gidajen da abin ya shafa da su dauki lamarin a matsayin wani kaddara daga Allah Ta’ala.
Shugaban karamar hukumar Shanga, Alhaji Audu Dan Audu, ya wakilce shi, ya ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a daren ranar Talata ya lalata gidaje da dukiyoyi na miliyoyin Naira, ya kuma yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki ganin yadda ba a yi asarar rayuka ba.
Ya kuma yi kira gare su da su yi hakuri domin nan bada jimawa gwamnatin jihar za ta mika musu tallafi da suka hada da kayayyakin gini.
Abdullahi Tukur
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar ‘Yan Sanda A Jihar Zamfara Ta Gargadi Direbobi Game Da Rufe Lambar Mota
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Zamfara ta gargaɗi direbobi da sauran jama’a game da rufe lambobin motoci, musamman a cikin garin Gusau, babban birnin jihar.
Gargaɗin ya biyo bayan ƙaruwa da ake samu na rahotanni da kuma lura da direbobi da ke tafiya da lambobin motoci a rufe, wanda rundunar ta bayyana a matsayin karya dokokin hanya da ke kawo barazana ga tsaro da zaman lafiya.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, rundunar ta bayyana cewa wannan dabi’a tana nuna ƙoƙarin kaucewa binciken jami’an tsaro tare da yiwuwar taimaka wa aikata laifuka.
Sanarwar ta ƙara da cewa, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya jaddada cewa rundunar ba za ta sake lamuntar irin wannan aiki ba.
Ya bayyana cewa an umarci jami’an rundunar da su fara aiwatar da tsauraran matakan doka, inda ya ƙara da cewa kowace mota da aka samu ta rufe lambar mota za a kama ta tare da gurfanar da mai motar a gaban doka.
CP Maikaba ya kuma shawarci jama’a da direbobi a fadin jihar Zamfara da su bi dokokin hanya tare da yin haɗin kai da ‘yan sanda wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Ya tabbatar wa jama’a da cewa rundunar ‘yan sandan za ta ci gaba da jajircewa wajen kiyaye doka da oda, tare da ƙarfafa al’umma da su rika ba da rahoton duk wani abin da suke zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Daga Aminu Dalhatu