Sojoji sun ceto mutum 84 da ’yan bindiga suka sace a Katsina
Published: 21st, March 2025 GMT
Dakarun Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 84 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Kankara a Jihar Katsina.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa sojojin runduna ta 17 tare da tallafin jiragen yaƙi sun kai farmaki maɓoyar ’yan ta’adda da ke yankin Sanusi Dutsin-Ma da tsaunukan Pauwa.
Ya ce a yayin farmakin dakarun sun kashe wasu daga cikin ’yan bindiga sannan suka kuɓutar da waɗanda aka sace.
Daga cikin mutanen da aka ceto, akwai maza bakwai, mata 23, da yara 54.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta yaba wa sojojin bisa ƙoƙarinsu, kuma tuni aka samar da abinci da kulawa ga mutanen da aka kuɓutar, kafin a mayar da su ga iyalansu.
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Katsina ba za ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba, domin tana da niyyar ci gaba da yaƙi da su har sai an daƙile matsalar garkuwa da mutane a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga dakaru Garkuwa Kwamishina yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Har Yanzu Ba A Ga Mutum 160 Bayan Ambaliyar Texas
Gwamnan jihar Texas ta Amurka ya ce sama da mutane 160 ne har yanzu ba a gano ba sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a ranar Juma’ar da ta gabata.
Greg Abbott ya ce wannan adadi na lardin Kerr ne kaɗai, ɗaya daga cikin wuraren da lamarin ya fi muni.
Hukumomi dai sun bayar da rahoton mutuwar fiye da mutum 100.
Masu aikin ceto na aiki a sannu a ƙoƙarin kawar da tarkacen da ruwan ya janyo domin gano ko akwai mutanen da ke maƙale a ƙarƙashinsu musamman a yankin gaɓar kogin Guadalupe.
A jihar New Mexico da ke makwabtaka da Texas, ruwa ya tafi da wani gida inda wani uba ke zaune da ‘ya’yansa biyu a yankin Ruidoso, kuma har anzu ana kan nemansu