Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia
Published: 22nd, March 2025 GMT
A ranar Juma’a aka rantsar da sabuwar shugabar ƙasar Namibia, Netumbo Nandi-Ndaitwah domin jagorantar ƙasar wadda aka ruwaito na fuskantar ƙalubale na rashin aikin yi da talauci.
Kasancewar Netumbo Nandi-Ndaitwah mace ta biyu da aka taɓa zaɓa a matsayin shugabar ƙasa a nahiyar Afirka, kuma ta farko a Namibia na iya fuskantar ƙalubale.
“Idan komai ya tafi daidai, wannan zai zama kyakkyawan misali,” kamar yadda Netumbo Nandi Ndaitwah ta shaida wa shirin Podcast na BBC Africa. “Amma idan wani abu ya faru, kamar yadda zai iya faruwa ga kowace gwamnati ko da a ƙarƙashin namiji ne, akwai waɗanda za su ce: ‘saboda ni mace ce!'”
Sabuwar shugabar, mai shekara 72 a duniya ta lashe zaɓen qasar ne a watan Nuwamba inda ta lashe kashi 58% na ƙuri’un da aka kaɗa.
Nandi-Ndaitwah ta kasance daɗaɗɗiyar ƴar jam’iyyar South West Africa People’s Organisation (Swapo) – wadda take kan mulki tun lokacin da ƙasar ta samu ƴancin kai a shekarar 1990, bayan kwashe tsawon lokaci tana fafutukar ƙwatar kanta daga Afirka ta Kudu mai fama da mulkin wariya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Netumbo Nandi Ndaitwah Nandi Ndaitwah
এছাড়াও পড়ুন:
Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka
Wasu lauyoyi biyu a Najeriya sun gargaɗi Gwamnatin Tarayya da ta yi taka-tsantsan wajen yin hulɗa da ƙasar Amurka, inda suka ce maganganun Amurka a kan Najeriya abun ruɗarwa ne
Babban lauyan nan, Cuf Okoi Obono-Obla, wanda tsohon mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara ne, ya zargi Amurka da son raba kan ’yan Najeriya da sunan kare Kiristoci.
Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a NijeriyaYa ce iƙirarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya ƙarya ne face nufin tayar da hankali da kawo rikici.
“Najeriya ba ta taɓa zama barazana ga zaman lafiyar duniya ba,” in ji Obono-Obla.
“Idan Amurka, inda ake yawan harbe mutane a coci-coci, ba ta gayyaci sojojin ƙetare su shigo musu ba, to kamata ya yi ta bar Najeriya ta magance nata matsalolin.”
Ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙurin Amurka na yin katsa-landan cikin harkokin Najeriya zai zama take doka da tauye ikon ƙasa.
Shi ma Barista Leonard Anyogo, kuma shugaban ƙungiyar ‘Good Governance Advocacy International’, ya shawarci Najeriya da ta bi hanyoyin diflomasiyya wajen mayar wa Amurka martani ba da faɗa ba.
“Ya kamata mu tattauna, ba mu yi fada ba,” in ji Anyogo.
“Najeriya ta nemi haɗin kai da Amurka a fannin tsaro da diflomasiyya domin kare muradunta.”