Gobara ta kashe ɗan shekara 7 a sansanin ’yan gudun hijira
Published: 21st, March 2025 GMT
Wata gobara da ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Munna Albadawi da ke ƙaramar hukumar Jere a Jihar Borno, ta lalata wasu gidaje 10 tare da salwantar da rayuwar yaro mai shekara 7 mai suna Abubakar Gargar.
A cewar shugaban sansanin, Babangida Mahmud gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:00 asubahin safiyar ranar 20 ga watan Maris, 2025, inda gobarar ta laƙume kayayyakin abinci da tufafi da dai sauran kayayyaki.
Wanda kawo yanzu ba a tantance adadin asarar da ta haifar ba baya ga salwantar rai guda.
Hukumar kashe gobara ta Jihar Borno tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro sun yi nasarar shawo kan gobarar da ƙyar da jibin goshi bayan da ta yi ɓarna mai yawan gaske.
Tuni dai aka yi wa marigayin jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya shimfiɗa.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar (SEMA) da sauran hukumomin jin ƙai sun baza jami’ansu a sansanonin don daidaita lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan gudun hijira Gobara a Maiduguri Munna Albadawi
এছাড়াও পড়ুন:
Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka
Har kullum, Sin za ta ci gaba da martaba ka’idojin kare hakkokin kamfanoninta. Duba da cewa manhajar TikTok ta shafe tsawon shekaru tana aiki a Amurka, ta kuma samar da dumbin ayyukan yi ga tarin Amurkawa, tare da bayar da gudummawa ga tattalin arzikin kasar, ya kamata gwamnatin kasar ta baiwa manhajar damar cin gajiya daidai da sauran makamantanta dake kasar. Kamar dai ko da yaushe, burin Sin shi ne wanzar da daidaito da cimma moriyar bai daya tare da Amurka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp