2025-07-05@06:23:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 108

«da aka naɗa»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya miƙa wa Majalisar Dokokin jihar sunayen zaɓaɓɓun kwamishinoni 16 domin tabbatarwa. Shugaban Majalisar, Danladi Jatau ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar da ya gudana ranar Litinin a birnin Lafiya. Atiku da Obasanjo suna ganawar sirri Ɗalibi ya kashe abokin karatunsu da gatari a Nasarawa Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin sabbin kwamishinonin da gwamnan ya zaɓa har da tsohon Shugaban Masu Rinjayen a majalisar dokokin jihar, Umar Tanko-Tunga da wani tsohon mamba a majalisar, Mohammed Agah-Muluku. Kakakin Majalisar ya buƙaci kowane ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun kwamishinonin da su gabatar da kwafi 30 na duk bayanansu daga yanzu zuwa ranar Alhamis tare neman su hallara a gaban majalsiar a ranar Litinin ta makon...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Kano. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yammacin ranar Asabar. Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja Ya yi wa kansa keji don daina shan sigari Sanarwar ta ce naɗin sabon Sakataren Gwamnatin zai fara aiki ne a hukumance daga ranar Litinin mai zuwa 10, ga Fabarairun 2025. Sanarwar ta ce an naɗa sabon Sakataren Gwamnatin wanda ya shafe sama da shekaru talatin yana aikin gwamnati la’akari da ƙwarewar aiki da yake da ita a hukumomi da ma’aikatu daban-daban na wajen ganin an cimma muradin gwamnati mai ci na ciyar da Jihar...
    Majalisar wakilai ta umarci kwamitocin sadarwa da harkokin cikin gida da su binciki haɗa lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) da layukan waya ba tare da izini ba da kamfanonin sadarwa ke yi. Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da ‘yan majalisa Patrick Umoh da Julius Ihonvbere suka gabatar, inda aka buƙaci hukumar NCC ta ɗauki mataki kan duk wani kamfanin sadarwa da aka samu da laifi, tare da NIMC ta tabbatar da sahihancin haɗa bayanan NIN. Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya Trump Ya Hana Maza Masu Sauyin Jinsi Shiga Wasannin Mata Umoh ya ce wannan mataki na iya haifar da damuwa ga ‘yan ƙasa, tare da jefa su cikin hatsarin satar bayanai, da damfara,...
    Masarautar Fika da ke Jihar Yobe ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a filin wasa na Dabo Aliyu da ke garin Potiskum. An buɗe gasar ƙarƙashin jagorancin mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Dr. Muhammad Ibn Abali Muhammad Idris wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe. Ya je Maiduguri daga Legas a kan keke Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a Kano Gasar wacce aka fara a shekarar 2011 ta bunƙasa zuwa wani gagarumin taron wasanni a yankin, wadda ke haɗa ƙungiyoyi daga ƙananan hukumomi huɗu na yankin da suka haɗa da Fune, Potiskum, Fika, da Nangere. A shekarar 2017 aka gudanar da gasar karo  na biyu, lamarin da ya ƙara tabbatar da gasar a matsayin...
    Gwamnati Ta Sake Haɗa Tubabbun Mayaƙan Boko Haram 5,000 Da Iyalansu
    Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami’an hukumar tsaron farin kaya daga jamhuriyar Nijar ne suka biyo wanda ake zargin ɗan bindigar ne a kan babbar hanyar Zurmi/Kauran Namoda a jihar Zamfara.   Da yake duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin sojojin da gwamnatin jihar Zamfara wajen yaƙi da ‘yan bindiga.   “Dole ne in yaba wa sojoji, DSS, da ‘yan sanda, musamman ma Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, bisa nasarar aiwatar da wannan gagarumin kame.   “Ina so in jaddada cewa waɗannan nasarori da aka samu tare da wasu na daƙile ‘yan bindiga a jihar, sun samo asali ne daga haɗin kai da goyon bayan da gwamnatin jihar Zamfara ke baiwa ɗaukacin...
    Ya ƙara da cewa, “Da har yanzu ina cikin wannan gwamnati, zan fadi gaskiya a cikin tarurruka na sirri, kuma idan ba a ɗauki mataki ba, zan yi magana a fili. Duk wanda ke shakkar haka, ya duba tarihin aikin gwamnati na tun daga 1998.” El-Rufai ya kuma soki wasu da ya kira “’yan amshin shata” a gwamnatin Tinubu, yana mai cewa suna amfani da kuɗaɗen tsaro don kare duk wani abu da gwamnati ke yi, ko da kuwa ba abin karewa bane. Ya buƙaci Bwala da ya tuna cewa “Alkawari na farko shi ne ga Allah da ƙasa, kafin wani mutum ko hukuma.”
    Haka kuma, an naɗa Muhammad Yahaya Liman a matsayin sabon Daraktan Akanta. Ya samu ƙwarewa a fannonin rahoton kuɗi da sarrafa kuɗi, ana sa ran zai taimaka wajen ƙara ƙarfin tsarin kuɗi na jihar. An kuma naɗa Akibu Isa Murtala, wanda a baya ya kasance Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ma’aikata, a matsayin Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Gudanarwa. Aikin sa shi ne kula da gudanar da ayyukan ma’aikatu. Injiniya Abubakar Sadiq kuma an naɗa a matsayin Mataimakin Manajan Darakta na Hukumar Samar da Ruwa da Tsabtace Muhalli a Ƙauyuka (RUWASA). An ɗora masa alhakin inganta samar da ruwa da tsabtace muhalli a yankunan karkara. Haka kuma, an kafa kwamiti na musamman domin farfaɗo da Hukumar Sufuri...