China Ta Gargadi Amurka Akan Batun Yakar Kasar Venezuela
Published: 28th, November 2025 GMT
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar China ta bayyana cewa: Beijing ba ta lamunta da duk wani kokarin tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gidan wannan kasar.”
Mao Ning wacce ta gabatar da taron manema labaru a brinin Beijing a kasar China ta yi kira ga kasar Amurka da ta fasa Shirin kai wa kasar Venezuela hari wanda ba ya kan doka,mai makon haka ta karfafa sulhu da zaman lafiya a cikin yankin Latin.
Kamfanin dillancin labarun Xin Hua na kasar China ya nakalto mai Mao Ning tana cewa; Kasar China ba ta kuma lamunta da kakaba wa kasar ta Venezuela takunkumi ta gefe daya wanda baya kan doka ba, kuma take dokokin kasa da kasa ne, saboda ba a yi shi a karkashin amincewar kwamitin tsaro na MDD ba.
Mao Ning ta kuma ce; Beijing tana son ganin dukkanin bangarori su girmama hurumin kasar Venezuela, su kuma kaucewa haddasa hargitsi.
A ranar 24 ga watan Nuwamba ta sanar da haramta wata kungiya wacce take mai fataucin muggan kwayoyi ce, kuma shugabanninta su ne shugaban kasar Venezuela Nicholas Maduro da kuma wasu jami’an gwamnatinsa.
Kasar Venezuela ta karyata abinda Amurkan ta riya, tare da bayyana shi a matsayin ‘karya bai sa dariya” sannan kuma tana son fakewa da haka ne domin tsama baki a harkokin cikin gidan kasar.
A cikin watannin bayan nan dai Amurkan tana kai hare-hare akan kananan jiragen ruwa a tekun Carrebea bisa riya cewa suna dauke da kwayoyi daga Venezuela zuwa Amurka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Palasdinu: Kwamandoji Biyu Na Rundunar “Sarayal-Quds” Sun Yi Shahada A Yammacin Kogin Jordan November 28, 2025 Kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi Ta Soki Shirin Donald Trump Na Bayyanata A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda November 28, 2025 Kasashen Qatar Da Jordan Sun Yi Allawadai Da Harin “Isra’ila” A Kasar Syria November 28, 2025 Senegal: Hambararren Shugaban Kasar Guinea Bissau Ya Isa Kasar Senegal November 28, 2025 Limamin Tehran: Hadin Kai Ne Sakamakon Imani Da Ayyukan Kwarai Ne November 28, 2025 Yamen Ta Soki Kasashen Birtaniya Da Amurka Da Tsoma Baki Kan harkokin Kasarta November 28, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 10 A Wani Hari Da Ta Kai A Birinin Damaskas Na Kasar Siriya November 28, 2025 Jagoran : Amurka Tasha Kashi A Yakin Kwanaki 12 Duk Da Manyan Makamai Na Zaman Da Take Da Su. November 28, 2025 Ministocin Tarayyar Turai Sun yi Tir Da Karuwar Hare –Haren Da Yahudawa Ke Kai wa Falasdinawa November 28, 2025 An Rantsar Da Sabon Shugaban Mulkin Soja Na kasar Guinea-Bissau November 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Venezuela Kasar Venezuela Kasar China kasar China
এছাড়াও পড়ুন:
An Rantsar Da Sabon Shugaban Mulkin Soja Na kasar Guinea-Bissau
An rantsar da Gen Horta N’tam a matsayin sabon shugaban mulkin sojan kasar Gunea-Bissau bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.
Gen Horta N’Tam ya zamo shugaban da zai mika mulki ga shugabannin farar hula inda zai kasance a kargar mulki na tsawon shekara guda.
An dai rantsar da shugaban ne a wani takaitacce kuma gajeren bikin da aka yi ranar Alhamis.
Wasu kungiyoyin farar hula a Guinea-Bissau sun soki shugaban da aka hambare, Umaro Sissoco Embalo da kitsa juyin mulki na wasan kwaikwayo a kansa, bisa taimakon sojoji, inda suke cewa ya shirya wasan kwaikwayon ne domin hana sakamakon zaben da aka yi ranar Lahadi fitowa idan bai yi nasara ba.
Sun ce sun kwace ikon ne domin dakile wani yunkurin ƴan siyasar kasar wadanda “ke tallafa wa wani gungu da ke ta’ammali da kwaya” sannan sojojin sun kuma rufe iyakokin Kasar tare da sanya dokar hana zirga-zirga da daddare.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila Na Barazanar Sake Shiga Wani Sabon Yaki Da Kasar Lebanon November 28, 2025 Petro: Man fetur shine burin Amurka a Venezuela ba yaki da fataucin kwayoyi ba November 28, 2025 Tarayyar Afirka ta yi Allah wadai da juyin mulkin a Guinea-Bissau November 28, 2025 Najeriya : Ana ci gaba da alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi November 27, 2025 Iran ta yi tir da Australiya kan alakanta IRGC, da mai tallafawa ta’addanci November 27, 2025 Ramaphosa ya soki Trump kan hana shi halartar taron G20 na badi November 27, 2025 ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau November 27, 2025 Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci November 27, 2025 Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci