Kwamishinan Tsaron Cikin Gida Na Kano Ya Yi Murabus Watanni 7 Bayan Naɗa Shi
Published: 26th, March 2025 GMT
Kwamishinan tsaron cikin gida da ayyuka na musamman na jihar Kano, Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya), ya yi murabus daga mukaminsa. An tabbatar da murabus din nasa ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar. Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din a hukumance, inda ya nuna jin dadinsa da irin gudunmawar da Janar din sojan ya bayar a lokacin da yake gudanar da aikinsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta raba zunzurutun kuɗi naira miliyan 63.4 ga iyalan jami’anta 84 da suka rasa rayukansu a bakin aiki.
Rundunar ta raba kudin ne a ƙarƙashin tsarin inshorar rayuwa da kuma tsarin kula da lafiyar iyali na Sufeto Janar na ’yan sanda.
An gudanar da rabon kuɗin ne a ranar Alhamis a Maiduguri babban birnin jihar kamar yadda Kakakin rundunar a jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana a cikin wata sanarwa.
A cewar sanarwar, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Naziru Abdulmajid, wanda ya wakilci Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, shi ne ya gabatar da takardun cakin kudin ga iyalan waɗanda suka ci gajiyar tallafin.
“Harkokin da suka shafi jami’anmu da iyalansu ya kasance babban fifiko ga rundunar,” in ji CP Abdulmajid yayin taron.
Ya ce wannan shiri na nuna tausayi da rikon amana, da kuma jagoranci mai nagarta daga Sufeto Janar wajen girmama jaruman da suka sadaukar da rayukansu domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasa.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga iyalan da suka amfana da tallafin da su yi amfani da kuɗaɗen yadda ya dace, musamman wajen tallafa wa ilimi, kiwon lafiya, da jin daɗin rayuwar iyalansu gaba ɗaya.
Ya yaba wa Sufeto Janar bisa ci gaba da tsare-tsaren jin daɗin jami’an rundunar, yana mai bayyana su a matsayin muhimman hanyoyin da ke samar da agaji da kwanciyar hankali ga iyalan waɗanda suka rasa masoyansu.
A nata jawabin a madadin iyalan da suka amfana, Misis Nana Goni ta nuna godiya ga Sufeto Janar bisa goyon bayan da ya bayar, tana mai tabbatar da cewa za su yi amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata don inganta rayuwar iyalansu.
Rundunar ta bayyana cewa wannan rabon tallafi ya sake tabbatar da jajircewarta wajen kula da walwala da mutuncin jami’anta da iyalansu, musamman waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen kare al’umma.