Aminiya:
2025-12-02@20:43:57 GMT

Tsohon shugaban Philippines ya faɗa komar ’yan sanda

Published: 11th, March 2025 GMT

’Yan sanda sun cafke tsohon shugaban ƙasar Philippines,  Rodrigo Duterte a filin jirgin saman birnin Manila a wannan Talatar.

Mista Duterte ya faɗa komar ’yan sandan ne bisa sammacin Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, jim kaɗan da saukarsa daga birnin Hong Kong.

Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet Ainihin abin da ke kawo wa Manchester United koma baya

Hatsaniya ta ɓarke a filin jirgin saman lokacin da ’yan sanda suka kama Mista Duterte, sakamakon tirjiya daga masu tsaron lafiyarsa da likitansa da kuma lauyoyinsa, wadanda ke zargin cewa an take masa haƙƙinsa da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi.

Fadar shugaban ƙasar Ferdinand Marcos ta ce tsohon shugaban na fuskantar tuhumar kisan ɗimbin jama’a a lokacin mulkinsa, wanda ya fake da yaƙi da masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

A lokacin dai ya sha alwashin kawar da fataucin miyagun ƙwayoyi, amma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’dama sun ce lamarin ya rikiɗe zuwa wani abu daban, inda ake zargin ’yan sanda da kashe dubban mutane, ciki har da waɗanda da ba su ji ba ba su gani ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kotun Duniya

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 12 da ɓacewarsu a Borno

’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinwu ta kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 12 da suka gabata a Jihar Borno.

Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam.

Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida.

Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game da gano tsabar zinare na masu daraja da suka ɓace tun 2012, lokacin da ’yan Boko Haram suka ƙona gidaje da shaguna da yawa a cikin al’ummarmu.”

Ta jaddada cewa, “babu daga cikin zinare da aka samu ya ɓace ko ya lalace a lokacin mamayar Malam Fatori da ’yan ta’adda suka yi fiye da nawa.”

Wani babban jami’in Majalisar Ƙaramar Hukumar Abadam da ya sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya yaba wa ’yan sandan da aka tura don kare rayukan mutane da kadarorinsu a yankin Tafkin Chadi.

Bayan gano tsabar zinare na naira miliyan 23, jami’in ya lura cewa martanin ’yan sanda a ayyukan yaƙi da ta’addanci da ake ci gaba da yi wani abin karfafa gwiwa ne ga sojoji da sauran hukumomin tsaro a yankin Tafkin Chadi, wanda ya ƙunshi qananan hukumomi takwas da ke yankin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An aiwatar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocin Majalisar Dattawa
  • Shugaba Tinubu Ya Nada Janar Christopher Musa Sabon Ministan Tsaro
  • Tinubu ya naɗa Janar CG Musa sabon Ministan Tsaron Nijeriya
  • ’Yan ta’adda sun kashe ɗan sanda a gidan DPO a Jigawa
  • An kama ’yan bindiga 4 a Kano
  • Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100%
  • MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar
  • ’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 13 da ɓacewarsu a Borno
  • ’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 12 da ɓacewarsu a Borno
  • ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi