CAF ta ƙara yawan ’yan wasan ƙasashe zuwa 28 a gasar nahiyar Afrika
Published: 28th, November 2025 GMT
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika (CAF), ta sanar da cewa daga yanzu kowace ƙasa da za ta taka leda a Gasar Cin Kofin Afrika za ta je da ’yan wasa 28, maimakon 23 da ake amfani da su a baya.
CAF, ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin rage matsalar samun raunin da ’yan wasa ke samu a lokacin gasar, tare da bai wa masu horaswa damar samun zaɓin ’yan wasa.
Haka kuma, an amincewa kowace ƙasa za ta je gasar da mutum 17 daga cikin masu horaswa da likitoci.
Hukumar ta bayyana cewa zuwa ranar 11 ga watan Disamba, dole a turo mata da cikakken jerin sunayen ’yan wasa, wato kwana 10 kafin a fara gasar.
Gasar za ta gudana daga 21 ga Disamba zuwa 18 ga watan Janairu, wanda ƙasar Maroko za ta kasance mai masaukin baƙi, inda ƙasashe 24 za su fafata a gasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gasar Nahiyar Afirka Ƙasashe Ƙwallo
এছাড়াও পড়ুন:
An janye ’yan sanda 11,566 daga yi wa manyan mutane rakiya – Egbetokun
Babban Sufeton ’yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ce sun janye ’yan sanda 11,566 da ke rakiyar manyan mutane kamar yadda Shugaban Ƙasa ya ba da umarni a kwanakin baya.
Ya kuma ce an sake tura waɗannan jami’an zuwa muhimman wuraren da aka fi buƙatars su don kare al’ummomi masu rauni a fadin ƙasa.
NAJERIYA A YAU:Waiwaye Kan Irin Gudunmawar Da Sheikh Dahiru Bauci Ya Bayar Ga Cigaban Addini An gano gawawwakin mata uku ’yan Kamaru da aka sace a AnambraAminiya ta rawaito cewa Shugaba Bola Tinubu, a ranar Lahadi, ya bayar da umarnin janye jami’an ‘yan sanda daga aikin tsaron manyan mutane tare da umartar a sake tura su zuwa ayyukan tsaro na asali.
Umarnin ya biyo bayan taron tsaro da aka gudanar a Abuja tare da shugabannin rundunonin tsaro da shugaban hukumar tsaro ta DSS.
Yayin da yake jawabi a hedikwatar ’yan sanda da ke Abuja, ranar Alhamis, lokacin da ya gana da manyan jami’an ‘yan sanda masu mukamin kwamishina, Egbetokun ya ce jami’an da aka janye za a mayar da su ga ayyukan tsaro na asali.
Ya ce shawarar janye jami’an daga aikin tsaron mutanen ba ta samo asali daga son rai ba, sai dai daga bukatar gaggawa ta karkatar da ma’aikata zuwa wuraren da tsaron jama’a ya fi bukata.
A cewarsa, wannan mataki ya yi daidai da babban aikin Hukumar ‘Yan Sanda ta Najeriya, wato kare ‘yan ƙasa, al’ummomi da kuma tabbatar da zaman lafiya, yana mai jaddada cewa dukkan jami’an 11,566 da aka janye an sake tura su wuraren aiki.
“A bisa umarnin Shugaban Ƙasa, mun janye jami’an 11,566 daga aikin tsaron manyan mutane. Waɗannan jami’an za a sake tura su zuwa muhimman ayyukan tsaro nan take,” in ji shi.
Babban Sufeton ya ce janyewar za ta bai wa ‘yan sanda damar ƙara yawan jami’an da za su yi aiki wajen tsaron ƙauyuka da birane, kare jama’a da yawa, ƙarfafa sintiri, ayyukan tsaro bisa bayanan sirri, da kuma daƙile barazanar tsaro cikin gaggawa.