Sarkin Kano Na 15, Aminu Ado Bayero Zai Naɗa Ɗan Uwansa Sanusi Ado A Matsayin Galadiman Kano
Published: 27th, April 2025 GMT
Wannan naɗi ya zama wani babban mataki a cikin mulkin Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda ke ci gaba da kiyaye al’adun masarautar tare da haɗa kan al’umma.
Sai dai kuma a cikin wannan wata ne Sarkin Kano na 16 Sanusi Lamido Sanusi II, ya fara naɗa Alhaji Mannir Sanusi (Hakimin Bichi) a wannan muƙami bayan rasuwar tsohon Galadima.
Za a iya cewa dai yanzu bayan Sarakuna biyu Kano na da Galadima biyu da aka naɗa a wata guda sakamakon Sarkuna biyun dake da’awar zama halattaccen Sarki, duk da dai Sarki Sanusi Lamido II shi yake gidan Rumfa yayin da Sarki Aminu ke gida masauƙin baƙi da na Nassarawa da ya mayar da shi sabuwar fadarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Bayero
এছাড়াও পড়ুন:
Ya kamata mulkin Najeriya ya ci gaba da zama a hannun ’yan Kudu — Hannatu Musawa
Ministar Raya Al’adu, Hannatu Musawa, ta ce ya kamata shugabancin ƙasar nan ya ci gaba da kasancewa a hannun ’yan Kudu domin a samu adalci da daidaito.
Ko da yake kundin tsarin mulkin Najeriya bai tilasta tsarin karɓa-karɓa ba, manyan jam’iyyun siyasa suna bin tsarin sauya mulki tsakanin Arewa da Kudu.
An tsare mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Filato Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – ƊangoteA wata hira da ta yi da gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, Hannatu Musawa ta ce tun da an samu Shugaba daga Arewa (Muhammadu Buhari) na tsawon shekaru takwas, to ya dace yanzu kuma a bar ’yan Kudu su yi shekaru takwas.
A shekarar 2023 ne Bola Ahmed Tinubu, wanda ɗan Kudu ne, ya gaji Buhari daga Arewa bayan kammala wa’adin mulkinsa.
Ministar ta ce: “Bayan shekara takwas na mulkin Buhari daga Arewa, ya kamata yanzu ’yan Kudu su ma su samu damar yin shekaru takwas don a samu adalci.”
A kwanakin baya, tsohon gwamnan Benuwe, Samuel Ortom, ya bayyana cewa ba zai goyi bayan ɗan takara daga Arewa ba.
Maganar karɓa-karɓa tsakanin Arewa da Kudu wani batu ne da ake ta muhawara a kai a siyasar Najeriya, kuma wasu masana na ganin yana hana dimokuraɗiyya ci gaba yadda ya kamata.