Ya kamata ’yan majalisar Najeriya su koma zaman wucin gadi – Ndume
Published: 28th, November 2025 GMT
Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ce Najeriya na iya ajiye biliyoyin naira a duk shekara idan aka rungumi tsarin majalisa ta wucin gadi.
Yayin da yake magana a gidan talabijin na Channels ranar Alhamis, Ndume ya ce kuɗin da ake kashewa wajen kula da Majalisar Dokoki a tsarin zama kodayaushe ba zai dore ba, musamman a wannan lokaci da ƙasar ke fama da matsalolin kuɗi da tsaro.
“Kudin gudanar da gwamnati ya yi yawa sosai. Idan ’yan majalisa suka zauna na wucin gadi, gwamnati za ta ajiye biliyoyi,” in ji shi.
Ya ce za a iya sauya akalar kuɗin zuwa bangaren tsaro da sauran muhimman abubuwan ƙasa.
Ndume ya danganta tsadar gudanar da gwamnati da manyan ƙalubale da ke hana ƙasar yin nasara wajen yaki da rashin tsaro.
Ya ce Najeriya ba za ta iya jure ɓarnar kashe kuɗi ba a yayin da ake fuskantar ta’addanci a Arewa maso Gabas, ’yan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, garkuwa da mutane, da kuma ƙaruwar laifuka.
A wani bangare na fafutukar rage kashe kuɗi, sanatan ya soki ci gaba da kasancewar ’yan sanda da ke tare da sanataci da sauran manyan mutane duk da umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye jami’an tsaro daga irin wannan aiki.
Aminiya ta rawaito cewa Shugaban Ƙasa ya umarci Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, da ya janye jami’an daga aikin kare manyan mutane ya kuma tura su zuwa fagen yaki da ta’addanci da samar da tsaro.
“Amma har yanzu, ’yan siyasa na tare da ’yan sanda,” in ji Ndume, yana kira ga Babban Sufeton da ya tabbatar da cikakken bin umarnin na shugaban ƙasa.
Ya bayyana cewa tura ’yan sanda daga aikin kare manyan mutane zuwa aikin al’umma da na fagen yaki zai ƙara inganta tsaron ƙasa fiye da ɗaure su ga mutum ɗaya.
Ndume ya ce tsarin tsaron ƙasa ya yi ƙunci kuma yana bukatar “haɗa hannaye wajen yin aiki,” yana mai jaddada cewa dubban jami’an suna makale wajen rakiyar ’yan siyasa da masu tasiri waɗanda za su iya rayuwa ba tare da irin wannan rakiyar ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: manyan mutane
এছাড়াও পড়ুন:
Yan Majalisar Kudu Sun Nemi Gafarar Tinubu Ga Nnamdi Kanu
’Yan Majalisar Tarayya daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.
Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci.
Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
Tuni aka tura Nnamdi Kanu zuwa gidan yari a Jihar Sakkwato inda yake zaman waƙafi.
A cikin sanarwa bayan taron gaggawa da suka gudanar a Abuja, ’yan majalisar sun ce duk da cewa suna girmama kotu da tsarin shari’a, lamarin ya rikiɗe zuwa matsalar ƙasa mai tasiri ga rayuwar jama’a, tattalin arziki da tsaro.
Da yake karanta sanarwar, Hon. Iduma Igariwey ya ce yin afuwa zai taimaka wajen rage tashin hankali da dawo da zaman lafiya a yankin.
Sun lissafa dalilai guda huɗu da suka sa suka yi wannan kira.
Dalilan da suke bayyana su ne ƙaruwa da rashin tsaro da tashin hankali da ke da alaƙa da tsare Kanu; Wahalar rayuwa da tattalin arziki da jama’a ke fuskanta da kuma buƙatar shugabanci mai tausayawa wajen shawo kan matsalolin ƙasa.