Jagoran : Amurka Tasha Kashi A Yakin Kwanaki 12 Duk Da Manyan Makamai Na Zaman Da Take Da Su.
Published: 28th, November 2025 GMT
Jagoran juyin musulunci na kar iran Ayatullah sayyid Ali Khamna’i ya bayyana cewa kasar Amurka bata ji da dadi ba a yakin kwanaki 12 da ta kaddamar a kan kasar iran a watan yuni, duk da amafani da ta yi da manyan makaman yaki na zamani da suka hada da jiragen yaki da kuma makaman kariya .
Har ila yau jagoran yace Amurka da isra’ila sun sha kashi a yakin kwanaki 12 da suka kaddamar kan kasar iran, sun kai harin ne don su ci blus, sai suka koma da borin kunya, basu iya tabuka komai ba, wannan babban shan kashi ne a garesu,
Yace wasu rahotanni sun nuna cewa gwamnatin sahyuniya ta shirya yakin shekaru 20, ta shirya tunzura mutane su juyawa tsarin musulunci na kasar baya, amma sai lamarin ya juya sabanin yadda suka yi tsammani, inda haka ya kara hadin kai tsakanin alummar kasar kuma reshe ya juye da mujiya.
Yace a ranar 13 ga watan yuni Amurka ta kaddamar da harin tsokana kan kasar iran inda ta kashe manyan jami’an sojin kasar da masana fasahar nukiliya da ma sauran fararen hula. Sai dai iran ta mayar da martani kan wasu sansanoninta dake yankin da suka hada da sansaninta na Al-udeida na kasar Qatar wanda shi ne mafi girma a yammacin asiya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministocin Tarayyar Turai Sun yi Tir Da Karuwar Hare –Haren Da Yahudawa Ke Kai wa Falasdinawa November 28, 2025 An Rantsar Da Sabon Shugaban Mulkin Soja Na kasar Guinea-Bissau November 28, 2025 Isra’ila Na Barazanar Sake Shiga Wani Sabon Yaki Da Kasar Lebanon November 28, 2025 Petro: Man fetur shine burin Amurka a Venezuela ba yaki da fataucin kwayoyi ba November 28, 2025 Tarayyar Afirka ta yi Allah wadai da juyin mulkin a Guinea-Bissau November 28, 2025 Najeriya : Ana ci gaba da alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi November 27, 2025 Iran ta yi tir da Australiya kan alakanta IRGC, da mai tallafawa ta’addanci November 27, 2025 Ramaphosa ya soki Trump kan hana shi halartar taron G20 na badi November 27, 2025 ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau November 27, 2025 Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Rantsar Da Sabon Shugaban Mulkin Soja Na kasar Guinea-Bissau
An rantsar da Gen Horta N’tam a matsayin sabon shugaban mulkin sojan kasar Gunea-Bissau bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.
Gen Horta N’Tam ya zamo shugaban da zai mika mulki ga shugabannin farar hula inda zai kasance a kargar mulki na tsawon shekara guda.
An dai rantsar da shugaban ne a wani takaitacce kuma gajeren bikin da aka yi ranar Alhamis.
Wasu kungiyoyin farar hula a Guinea-Bissau sun soki shugaban da aka hambare, Umaro Sissoco Embalo da kitsa juyin mulki na wasan kwaikwayo a kansa, bisa taimakon sojoji, inda suke cewa ya shirya wasan kwaikwayon ne domin hana sakamakon zaben da aka yi ranar Lahadi fitowa idan bai yi nasara ba.
Sun ce sun kwace ikon ne domin dakile wani yunkurin ƴan siyasar kasar wadanda “ke tallafa wa wani gungu da ke ta’ammali da kwaya” sannan sojojin sun kuma rufe iyakokin Kasar tare da sanya dokar hana zirga-zirga da daddare.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila Na Barazanar Sake Shiga Wani Sabon Yaki Da Kasar Lebanon November 28, 2025 Petro: Man fetur shine burin Amurka a Venezuela ba yaki da fataucin kwayoyi ba November 28, 2025 Tarayyar Afirka ta yi Allah wadai da juyin mulkin a Guinea-Bissau November 28, 2025 Najeriya : Ana ci gaba da alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi November 27, 2025 Iran ta yi tir da Australiya kan alakanta IRGC, da mai tallafawa ta’addanci November 27, 2025 Ramaphosa ya soki Trump kan hana shi halartar taron G20 na badi November 27, 2025 ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau November 27, 2025 Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci November 27, 2025 Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci