Jonathan ya dawo Najeriya bayan juyin mulki ya ritsa da shi a Guinea-Bissau
Published: 28th, November 2025 GMT
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dawo Najeriya bayan juyin mulkin sojoji ya ritsa da shi a ƙasar Guinea-Bissau inda ya je sa ido kan zaben ƙasar.
Jonathan ya isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da yammacin Alhamis, kusan kwana biyu bayan sojoji sun karɓi mulki a ƙasar da ke yammacin Afirka.
Ya isa filin jirgin sama na Abuja a cikin jirgin gwamnatin Guinea-Bissau, inda tawagar magoya baya da jami’an gwamnati suka tarbe shi.
Tsohon shugaban kasar ya je Guinea-Bissau ne don sa ido kan zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki a matsayin shugaban tawagar sa ido ta dattawan Afirka ta Yamma.
Tawagarsa, tare da ta Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) da Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), suna ci gaba da aikinsu lokacin da sojoji suka yi juyin mulki a Guinea-Bissau.
Wannan lamari ya bar tsohon shugaban kasar tare da sauran mambobin tawagar masu sa ido cikin rashin tabbas da damuwa kan lafiyar su.
Sai dai ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta bayyana cewa tsohon shugaban kasa yana cikin koshin lafiya kuma ya bar Guinea-Bissau.
“Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan yana cikin koshin lafiya kuma ya fita daga Guinea-Bissau,” in ji mai magana da yawun ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa.
“Ya tafi ne da jirgi na musamman tare da mambobin tawagarsa, ciki har da Ibn Chambas.”
Sojojin Guinea-Bissau sun ƙwace iko da ƙasar a ranar Laraba, inda suka dakatar da tsarin zaben ƙasar tare da rufe iyakokinta, kwanaki bayan gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki.
Bayan juyin mulkin, shugaban ofishin soja na fadar shugaban kasa, Janar Denis N’Canha, ya ce kwamitin da ya ƙunshi dukkan sassan sojoji, ya karɓi jagorancin ƙasar har zuwa lokacin da za a bayar da sanarwa ta gaba.
Sojojin sun kuma kama shugaban kasar Umaro Embalo, wanda ake ganin zai iya lashe zaben na ranar Lahadi.
Kwana ɗaya bayan juyin mulkin, sojojin sun nada shugaban hafsoshin rundunar sojoji, Janar Horta N’Tam, a matsayin sabon shugaban ƙasar na na riƙon ƙwarya.
Zai jagoranci ƙasar na tsawon shekara guda.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: bayan juyin Jonathan ya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Sun Sanar Da Kwace Mulki A Kasar Guinea Bissau
Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu dauke da makamai sun kama shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo a yau Laraba, kwanaki uku bayan da aka yi zaben shugaban kasa.
Rahotannin sun ce an yi ta harbe harbe a babban birnin kasar, a yayin da Alummar kasar ke zaman jiran sakamako zagaye na farko na zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Lahadi.
Zuwa yanzu ba a tabbatar da ko su wane ne suka yi harbin ba.
Rahotannin sun kuma ce an yi ta harbe harben a kusa da fadar shugaban kasar da ofishin hukumar zabe a yau Laraba, inda mutane suka tarwatse suna neman mafaka.
A jiya Talata ne dai shugaban mai ci Umaro Sissoco Embalo, da babban abokin hamayyarsa Fernando Dias, suka yi ta ikirarin yin nasara a zaben wanda ya kamata a yi tun a shekarar da ta gabata.
Guinea Bissau dai ta fuskanci juyin mulki har karo hudu da rashin zaman lafiya tun bayan samun ƴancin kai daga Portugal a 1974.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Larijani Iran Tana Maraba Da Tattaunawa Ta Gaskiya Amma Ba Tsararren Sakamako Ba November 26, 2025 November 26, 2025 Isra’ila Tana Ci Gaba Da Rushe Gidaje A Yankin Gaza November 26, 2025 Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe November 26, 2025 Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta November 26, 2025 Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki November 26, 2025 Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin November 26, 2025 Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin Lebanon November 26, 2025 Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci