Mutum Shida Sun Mutu A Hatsarin Jirgi Mai Saukar Ungulu A Amurka
Published: 11th, April 2025 GMT
Wani jirgi mai saukar ungulu ya faɗa cikin kogin Hudson da ke birnin New York a Amurka.
Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun bayyana cewa mutum shida da ke cikin jirgin – fasinja biyar da direban jirgi guda sun mutu.
Magajin garin New York Eric Adams ya ce jirgin na ɗauke da wani iyali su biyar daga Spain har da yara uku.
Ya ƙara da cewa tuni aka tsamo gawarwakin mutum biyar ɗin daga ruwa.
Wakilin BBC ya ce har yanzu ana aikin ceto domin koƙarin zaƙulo tarkacen jirgin da masu bincike za su buƙata don gano abin da ya haddasa haɗarin.
Shaidu sun ce jirgin ya tarwatse ne tun a sama inda kuma ya faɗa cikin kogin.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Hadari
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 3 sun mutum yayin haƙar rijiya a Kano
Wasu mutane uku sun rasu yayin da suke tsaka da aikin yasar rijiya a garin Badume da ke Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano.
A yayin da suke aikin haƙar rijiya, ɗaya daga cikinsu ya shiga domin yasowa biyu kuma na janyo ƙasar da aka haƙo.
Ana cikin haka igiyar ta tsinke, inda nan take ƙasa ta koma kan dattijon mai shekara 65 da ke haƙar rijiyar.
Hakan ya sa ɗansa mai shekara 20 shiga rijiyar domin fito da shi amma abu ya tura.
A nan ne na ukunsu mai 60 Yakubu Abdullahi shi ma ya shiga domin ceto su, amma duka dai abu ya gagara.
A ƙarshe jami’an Hukumar Kashe Gobara sun yi nasarar ceto su ukun a sume, amma daga baya likita ya tabbatar da rasuwarsu bayan kai su asibiti kamar yadda mai magana da yawun rundunar ya bayyana.