HausaTv:
2025-11-28@17:53:01 GMT

Kasashen Qatar Da Jordan Sun Yi Allawadai Da Harin “Isra’ila” A Kasar Syria

Published: 28th, November 2025 GMT

A bayanin da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar a yau, ta yi tir da harin da sojojin na “Isra’ila” su ka kai wa kauyen Beit-Jin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13.

Bayanin ya kara da cewa; Harin, yana a matsayin keta hurumin shugabancin kasar Syrai da kuma dokokin kasa da kasa.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Qatar ya kuma ce, abinda “Isra’ila” take yi a wannan yankin yana kara yawan zaman dar-dar din da ake ciki a wannan yankin.

Da safiyar yau Juma’a ne dai sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kutsa cikin garin Beit-Jin a gefen birnin Damascuss, inda ta bude wuta akan mutanen kauyen da ya kai ga kashe 13 daga cikinsu da jikkata wasu.

Ita kuwa ma’aikatar harkokin wajen kasar Jordan ta bayyana cewa; Abinda ya faru keta hurumin kasar Syria ne da kuma dokokin duniya.

 Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Jordan, Fu’ad al-majali ya ce, harin na Isra’ila wata tsokana cem ai hatsarin gaske da zai kara matsala akan wacce ake da ita a wannan yankin.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Jordan ta bayyana cewa, dole ne a kawo karshen hare-haren da Isra’ilan take kai wa akan kasar Syria, da komawa aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta ta 1974.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Senegal: Hambararren Shugaban Kasar Guinea Bissau Ya Isa Kasar Senegal November 28, 2025 Limamin Tehran: Hadin Kai Ne Sakamakon Imani Da Ayyukan Kwarai Ne November 28, 2025 Yamen Ta Soki Kasashen Birtaniya Da Amurka Da Tsoma Baki Kan harkokin Kasarta November 28, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 10 A Wani Hari Da Ta Kai A Birinin Damaskas Na Kasar Siriya November 28, 2025 Jagoran : Amurka Tasha Kashi A Yakin Kwanaki 12 Duk Da Manyan Makamai Na Zaman Da Take Da Su. November 28, 2025 Ministocin Tarayyar Turai Sun yi Tir Da Karuwar Hare –Haren Da Yahudawa Ke Kai wa Falasdinawa November 28, 2025 An Rantsar Da Sabon Shugaban Mulkin Soja Na kasar Guinea-Bissau November 28, 2025 Isra’ila Na Barazanar Sake Shiga Wani Sabon Yaki Da Kasar Lebanon November 28, 2025 Petro: Man fetur shine burin Amurka a Venezuela ba yaki da fataucin kwayoyi ba November 28, 2025 Tarayyar Afirka ta yi Allah wadai da juyin mulkin a Guinea-Bissau November 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: aikatar harkokin wajen

এছাড়াও পড়ুন:

UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin  Lebanon

Wani mai magana da yawun rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIFIL) ya tabbatar da cewa Isra’ila ta gina katanga kan iyakar da ta ratsa zuwa cikin yankin kasar Lebanon kusa da garin Yaroun, abin da tawagar ta bayyana a matsayin keta kudurin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701.

“Isra’ila ta shafe shekaru da dama tana gina katanga a gefen Layin da aka Shata da ya raba yankunan Falastinu da Isra’ila ta mamaye da Lebanon, amma a cikin wannan yanayi katangar Isra’ila ta ratsa layin da ya raba bangarorin biyu,” in ji mai magana da yawun UNIFIL. “Don haka muna nuna rashin amincewa da wannan mataki, Wannan, a bayyane ya keta kuduri mai lamba 1701 da kuma hurumin kasar  Lebanon.” Inji shi.

Dakarun Masu Sanya ido kan zaman lafiya a kudancin kasar Lebanon UNIFIL  sun yi nazarin wurin kuma kuma tabbatar da cewa katangar ta ketare Layin da aka shata.

A cewar UNIFIL,  sun gano cewa katangar tana cikin kasar Lebanon kuma ta  kai  kimanin mita murabba’i 4,000 a cikin kasar Lebanon”.  Mai magana da yawun rundunar ya kara da cewa, tawagar ta sanar da sojojin na Isra’ila a hukumance  game da keta dokar da suka yi, inda suka mayar da martanin cewa za su dubi lamarin.

UNIFIL ta jaddada cewa za ta ci gaba da bin diddigin lamarin, da kuma ci gaba da Magana tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa don tabbatar da cewa an kiyaye doka da kuma yin aiki da kudiri mai lamba 1701.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru  Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • China Ta Gargadi Amurka Akan Batun Yakar Kasar Venezuela
  • Palasdinu: Kwamandoji Biyu Na Rundunar “Sarayal-Quds” Sun Yi Shahada A Yammacin Kogin Jordan
  • Senegal: Hambararren Shugaban Kasar Guinea Bissau Ya Isa Kasar Senegal
  • Isra’ila Ta Kashe Mutane 10 A Wani Hari Da Ta Kai A Birinin Damaskas Na Kasar Siriya
  • Isra’ila Na Barazanar Sake Shiga Wani Sabon Yaki Da Kasar Lebanon
  • Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan
  • An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
  • UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin  Lebanon
  • Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu