Portugal ta lashe Kofin Duniya na ’yan ƙasa da shekaru 17 a karon farko
Published: 28th, November 2025 GMT
Kasar Portugal ta kafa tarihi a birnin Doha na Qatar bayan da ta lashe Kofin Duniya na ’yan ƙasa da shekaru 17 (U-17) a karon farko, inda ta doke Austria da ci 1-0 a wasan ƙarshe.
An jefa ƙwallon da ta bai wa Portugal nasara ne ta hannun Anisio Cabral, wanda ya ci a minti na 32 da fara buga wasan a filin wasa na Khalifa.
A hanyarta ta kaiwa wasan ƙarshen, Portugal ta doke Brazil a wasan kusa da na ƙarshe, yayin da Austria ta fitar da Italiya bayan lallasa ta da ci 2-0.
Wannan nasara ita ce ta farko a tarihin Portugal tun da aka fara gasar, wanda hakan ya sanya sunanta cikin jerin ƙasashen da suka taɓa ɗaga kofin.
Nijeriya ce ƙasa mafi nasara a gasar U-17, inda ta lashe ta sau biyar. Sai Brazil wacce ta lashe sau uku, Ghana da Mexico wadanda suka lashe sau biyu-biyu.
Akwa kuma Jamus, Ingila, Switzerland, Faransa da Saudiyya kuwa kowacce ta lashe sau daya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kofin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta samu nasara a wasan mako na 14 na Nigeria Premier Football League (NPFL), bayan da ta doke Ikorodu City da ci 2–1 a filin wasa na Muhammad Dikko, da ke birnin Katsina.
Wannan ita ce nasara ta uku da Pillars ta samu a kakar bana, cikin wasanninta 14, inda ta yi kunnen doki uku, sannan ta sha kashi shida.
’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun TuraiKafin wannan wasan, Kano Pillars ta yi wasanni takwas a jere ba tare da samun nasara ba.
Pillars ta zura kwallayenta ne ta hannun Rabiu Ali, wanda ya zura ta farko a minti na 3, sai Olakunle Alaka ya kara ta biyu a minti na 30.
A daidai minti na 45, kafin a je hutun rabin lokaci, Joseph Arumala ya rage tazara ga Ikorodu City.
Duk da wannan nasarar, Kano Pillars ta ci gaba da zama a matsayi na 20, inda take da maki 9 a ƙasan teburin gasar.
A wani labarin, ƙungiyar Katsina United ta samu nasarar doke Enyimba da ci 3–2 a birnin Ilorin, inda take buga wasanninta na gida bayan dakatar da ita daga yin wasa a filin gidan ta a Katsina.