Kamfanin Harhaɗa Mota Na Dangote Ya Kera Peugeot 3008 GT A Kaduna
Published: 11th, February 2025 GMT
Kamfanin Dangote na Peugeot Automobiles Nigeria Limited (DPAN), wanda ke kera wa da tallata motocin Peugeot a Nijeriya, ya fara tarawa da haɗa sabuwar Peugeot 3008 GT a masana’antarsa da ke Kaduna.
Peugeot 3008 GT, mai injin 1.6-lita turbo mai ƙarfi, ya ƙara yawan jerin motocin da ake haɗawa a masana’antar DPAN, wanda ya ya ke samar da 301 sedan da Peugeot 5008 mai kujeru bakwai.
Hakanan, an samar da fasahar ABS don hana birki shanye wa, ESP don hana zamewa, da EBFD don daidaita birki bisa nauyin mota.
Motar na kuma ɗauke da fasahar Peugeot I-Cockpit, wacce ke da allon 12.3-inch mai nuna bayanai, touchscreen mai girman 8-inch, da kuma madannin tuƙi mai ayyuka da dama. Wannan ci gaba yana tabbatar da cewa DPAN na ci gaba da samar da motocin zamani masu inganci ga kasuwar Nijeriya.
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban SUBEB Yayi Alkawarin Bayar Da Tallafin Ilimi A Jihar Nasarawa
A wani gagarumin ci gaba na inganta walwala da ci gaban yara da matasa wadanda suka isa makaranta, Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Farko ta Jihar Nasarawa NSUBEB, Dokta Kasim Mohammed Kasim ya karbi tawagar Kids & Teens Resource Center K&TRC a wani taron bayar da shawarwari da aka mayar da hankali kan shirin Ilimi don Lafiya da walwala, wanda UNESCO ke tallafawa.
An gudanar da babban taron ne a hedkwatar Hukumar NSUBEB, inda ya samu halartar kwamishinonin hukumar su uku, da Daraktoci da dama, da kuma tawagar K&TRC karkashin jagorancin wanda ya kafa kuma Shugaba, Mista Martin-Mary Falana.
Tattaunawar a yayin zaman ta tabo batutuwan da suka shafi rayuwar yara da matasa a jihar, wadanda suka hada da yawaitar cin zarafin mata kamar lalata da fyade, cin zarafi a makarantu, kananan yara da auren dole, kaciyar mata, da kuma yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.
Mahalarta taron sun amince da bukatar gaggawar samar da cikakken martani ta bangaren ilimi domin tunkarar wadannan kalubale.
Shugaban hukumar ya yi alkawarin ba da cikakken kudurin siyasa na hukumar tare da ba da tabbacin baiwa kungiyar K&TRC na NSUBEB goyon baya wajen samar da yanayi mai dacewa don samun nasarar aiwatar da aikin.
COV/Aliyu Muraki/Lafia.