Aminiya:
2025-11-28@13:47:38 GMT

CAF Tayi Watsi Da Alƙalan Wasan Nijeriya a Kofin Afrika Na 2025

Published: 28th, November 2025 GMT

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nahiyyar Afrika (CAF) ta fitar da jerin alƙalan wasa da masu kula da na’urar VAR a gasar cin kofin Nahiyyar Afrika ta 2025, amma babu ɗan Najeriya ko ɗaya.

A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ayyana alƙalan wasa 28 da masu kula da VAR 14 daga ƙasashe daban-daban.

Ƙasar Japan ta fara sayar da injin da ke yi wa mutane wanka Hamɓararren Shugaban Guinea-Bissau ya gudu Senegal

Hukumar ta zaɓo alƙalan wasa biyu daga ƙasashen Maroko, Aljeriya, Masar, da kuma Mauritaniya.

Masana harkokin wasanni dai na ganin cewa matsalar cin hanci da rashawa ne dalilin yin shagulacin ɓangaro ga alƙalan wasan Najeriya, saboda karɓar na goro musamman a gasar Firimiya.

Kawo yanzu an shafe shekaru 19 rabon da wani alƙalin wasa daga Najeriya ya busa gasar cin kofin Nahiyyar Afrika.

Za a fara gasar daga ranar 21 ga watan Disamba 2025 zuwa 18 ga watan Janairun 2026.

Ƙasar Maroko ce za ta buɗe gasar da karɓar baƙuncin Comoros a birnin Rabat.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Alƙalin Wasa Masar Nijeriya alƙalan wasa

এছাড়াও পড়ুন:

Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai

A yammacin nan ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid za ta kece raini da Olympiacos a ci gaba da Gasar Zakarun Turai, duk da rashin wasu manyan ’yan wasanta biyu.

Babban mai tsaron ragar Madrid, Thibaut Courtois, da ɗan wasan baya Dean Huijsen, na fama da jinya, lamarin da zai hana su buga wannan muhimmin wasa.

Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu

Yanzu haka jerin ’yan wasan Madrid da ke jinya sun haɗa da: Thibaut Courtois, Dean Huijsen, Antonio Rüdiger, David Alaba, Franco Mastantuono, da Éder Militão.

Tun bayan zuwan sabon kocin Real Madrid, Xabi Alonso, Courtois ya riƙe ragamar tsaron raga a dukkan wasanni 17 da suka buga a kakar nan.

Andriy Lunin, ɗan asalin ƙasar Ukraine mai shekaru 26, shi ne mai tsaron da ya fi samun damar buga wasanni a zamanin tsohon koci Carlo Ancelotti, lokacin da Courtois ya yi jinya mai tsawo.

Gasar Zakarun Turai dai fage ne da Real Madrid ta yi fice a duniya wadda ta lashe sau 15 a tarihi.

A bana, ƙungiyar tana da maki 9 daga wasanni 4 da ta buga zuwa yanzu da ake kece raini a matakin rukuni

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ya kamata ’yan majalisar Najeriya su koma zaman wucin gadi – Ndume
  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • Mbappe ya ci ƙwallaye 4 rigis a wasan Madrid da Olympiacos
  • Super Falcons za su ƙaurace wa wasannin Nijeriya saboda riƙe musu alawus
  • Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu.
  • Aljeriya Tayi Kira Da A Dakatar Da Israila Game Da Hare-haren Da Take Kaiwa
  • Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai
  • DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
  • Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai