Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali
Published: 28th, November 2025 GMT
Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta nemi hukumomin tsaro su gaggauta bincikar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, kan zarginsa da kalaman tayar da hankali.
Wannan na zuwa ne bayan kammala zaman majalisar zartarwa na 34 da aka yi ranar Alhamis a Fadar Gwamnatin Kano.
Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi CAF Tayi Watsi Da Alƙalan Wasan Nijeriya a Kofin Afrika Na 2025Zaman ya mayar da hankali kan maganganun da Ganduje da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin suka yi, inda suka ce Kano na ƙara fuskantar barazanar hare-haren ’yan bindiga.
Ganduje ya bayyana aniyar ɗaukar mutum 12,000 aiki wanda hukumar Hisbah ta sallama daga aiki, a wata ƙungiya mai alaka da ake kira da “Khairul Nas”.
Da yake zantawa da manema labarai ranar Juma’a, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce waɗannan maganganu na iya kawo koma baya ga harkar tsaro da ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi.
Majalisar ta kuma nuna damuwarta cewa ƙasa da awanni 48 bayan yin waɗannan maganganu, aka sake kai hari wasu yankuna na jihar.
Gwamnatin jihar ta sake godewa Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro kan goyon bayan da suke bayarwa wajen yaƙi da matsalolin tsaro.
Haka kuma ta yi gargaɗin cewa ba za ta bari wani ko wata ƙungiya ta kafa haramtacciyar rundunar tsaro ba a Jihar Kano.
A ƙarshe, gwamnatin ta roƙi jami’an gwamnati da’yan siyasa su guji yin maganganun da ka iya tayar da hankali.
Ta kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da doka a faɗin Kano.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnati Majalisar Zartarwa Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Radda Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Ya Zama Doka
Daga Isma’il Adamu
Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya sanya hannu kan kudirin kasafin kudin jihar na 2026 na Naira Biliyan 897, makonni uku bayan gabatar da shi a gaban majalisar dokokin jihar.
Yayin rattaba hannu a Fadar Gwamnati da ke Katsina, a gaban ‘yan majalisar dokokin jihar, gwamnan ya jinjinawa majalisar bisa gaggawar amincewa da kasafin, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da shi yadda ya dace.
Ya bayyana cewa kashi 82 cikin ɗari na kasafin an ware shi ne ga manyon ayyuka(capital expenditure), yayin da kashi 18 cikin ɗari aka ware ga ayyukan yau da kullum(recurrent expenditure), rabo wanda ya ce ya fi abin da doka ta baya ta tanada, wadda ke bukatar kada kudaden gudanarwa su haura kashi 30 cikin ɗari.
Gwamna Radda, wanda ya bayyana kasafin a matsayin “kasafin jama’a,” ya ce an tsara shi ne daga shawarwarin da aka tattara a tarukan jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a fadin kananan hukumomi 34 na jihar.
Yayin da yake jinjinawa ‘yan majalisar dokokin jihar bisa kyakkyawar alakar aiki da suke da ita da bangaren zartarwa, gwamnan ya bukaci kwamitocin majalisar su gudanar da aikinsu na sa ido don tabbatar da cewa an aiwatar da kasafin yadda ya kamata.
Tun da farko, yayin mika kudirin kasafin domin rattaba hannu, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Nasir Yahaya, ya ce ‘yan majalisar sun duba tare da amince da kasafin cikin makonni uku, lamarin da ya sanya Katsina ta zama jihar farko da ta samu dokar kasafin kudin shekara ta 2026.