Aminiya:
2025-11-27@23:00:28 GMT

Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya

Published: 4th, March 2025 GMT

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Shamsedeen Babatunde Ogunjimi a matsayin sabon Akanta Janar na Tarayya.

Naɗin nasa, wanda aka amince da shi a yau Talata, zai fara aiki ne daga ranar 7 ga Maris 2025, ranar da Oluwatoyin Madehin zai yi ritaya.

Muhimmancin ƙamshi a rayuwar mace An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a

Ana iya tuna cewa, tun a watan Disambar da ya gabata ne aka bayyana Ogunjimi mai shekaru 57 a matsayin magajin Madehin.

Daga baya wani aka naɗa wani kwamitin ƙwararru da zai tantance wanda ya haɗa da manyan daraktocin daga a ma’aikatun gwamnatin tarayya daban-daban.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce kwamitin ya yi tantancewar bisa matakai uku masu tsauri da suka haɗa da a rubuce, gwajin ƙwarewar fasahar sadarwar da kuma hira ta baka.

Ogunjimi ya kammala karatunsa na digiri a Jami’ar Nijeriya, Nsukka, a shekarar 1990, inda ya sami digiri na farko a fannin lissafin kuɗi.

Ya kuma samu wani digiri na biyun a wannan fannin a Jami’ar Legas.

Kazalika, sabon Akanta Janar ɗin mamba ne a Cibiyar Akantoci na Nijeriya da Cibiyar Haraji ta Nijeriya.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ya taya Ogunjimi murna, ya kuma buƙaci da ya hidimta wa Nijeriya bisa gaskiya, ƙwarewa, da sadaukarwa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Akanta Janar

এছাড়াও পড়ুন:

Super Falcons za su ƙaurace wa wasannin Nijeriya saboda riƙe musu alawus

’Yan wasan tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Mata, Super Falcons, sun yi barazanar ƙaurace wa wasannin sada zumunta da Najeriya za ta buga a watan Disamba mai kamawa.

’Yan wasan sun ce za su ƙaurace wa wasannin ne idan har Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta ci gaba da jinkirta biyan kuɗaɗen alawus-alawus da suke biyo tun na Gasar Olympics da aka yi a birnin Paris a 2024.

Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro

Wasu majiyoyi daga ƙungiyar sun tabbatar cewa ’yan wasan na ci gaba da jiran a biya su haƙƙoƙinsu na wasannin da suka buga, ciki har da alawus na nasarar da suka samu a gasar Olympics, duk da cewa Najeriya ta fice tun a matakin rukuni bayan shan kashi a hannun Brazil da Spain da Japan.

Wani jami’in tawagar, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce ’yan wasan gaba ɗaya sun amince cewa ba za su halarci kowanne wasa ba muddin ba a biya su haƙƙoƙinsu ba.

Ana sa ran Najeriya za ta buga jerin wasannin sada zumunta daga ranar 2 zuwa 10 ga watan Disamba, a wani ɓangare na shirye-shiryen Super Falcons domin tunkarar gasar cin Kofin Afrika ta Mata na 2026.

A halin yanzu, NFF ba ta fitar da jerin sunayen ’yan wasan da za su wakilci Najeriya a wasannin ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu
  • Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
  • Super Falcons za su ƙaurace wa wasannin Nijeriya saboda riƙe musu alawus
  • Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Harkar Tsaro Tare da Bada Umurnin Daukar Sabbin Jami’ai
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
  • Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu
  • Faduwar Darajar Kuɗi Na Kara Tsananta Kalubale Ga Kotunan Shari’a — CJN
  • Abin da ya sa nake haxa harkar fim da harkar karatu-Nabila