Aminiya:
2025-11-28@16:24:38 GMT

Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi

Published: 28th, November 2025 GMT

Dubban mutane sun taru a Jihar Bauchi, don halartar jana’izar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa.

Gwamnatin Jihar Bauchi, ta ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu domin ba jama’a damar halartar jana’izar malamin.

Trump zai haramta wa ’yan Najeriya da wasu ƙasashe zuwa Amurka CAF Tayi Watsi Da Alƙalan Wasan Nijeriya a Kofin Afrika Na 2025

Ɗalibansa da sauran Musulmi daga Bauchi da maƙwabtan jihohi sun isa da wuri domin halartar jana’izar.

Huumomi sun tsaurara matakai a jihar don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali.

Maulud Dahiru Bauchi, wanda ya yi magana a madadin iyalan marigayin, ya ce za a yi jana’izar malamin da misalin ƙarfe 3 na rana bisa wasiyyar malamin.

Ya ƙara da cewa Sheikh Sharif Saleh ne zai jagoranci jana’izar.

Jama’a da dama sun halarta, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, gwamnoni, sarakuna, ’yan kasuwa, attajirai da sauransu.

Iyalan mamacin sun ce dandazon mutanen da suka halarci jana’izar, ya nuna tasirin da Sheikh Dahiru ya yi wajen yaɗa addini da tarbiyya tsawon rayuwarsa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: rasuwa halartar jana izar

এছাড়াও পড়ুন:

Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi

A ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamban 2025 ce Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma jigo a Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa.

Ya rasu yana da sama da shekaru 100 a duniya.

Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da zuri’arsa ta fi kowacce yawan mahaddata Alkur’ani

Baya ga tarin iliminsa da yawan shekaru, akwai wasu tarin baiwa da Allah Ya ba malamin, wadanda ba kowa ne ya san da su ba.

Aminiya ta yi nazari a kansu, inda ta zakulo muku abubuwa 18 da ya kamata ku sani a kansa.

Ga wasu daga ciki:

Ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a duniya, inda yake da ’ya’ya da jikoki da tataba-kunne kusan 300 da suka haddace Alkur’ani mai girma Kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, ya ba shi shaidar girmamawa saboda yawan zuri’a mahaddata Yana da ’ya’ya 95 Yana da jikoki 406 Yana da tattaba-kunne 100 ’Ya’yansa mahaddata Alkur’ani 77 Jikokinsa mahaddata Alkur’ani 199 Tattaba-kunnensa mahaddata Alkur’ani 12 Shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Koli da ke bayar da fatawa a addinin Musulunci a Najeriya An haife shi a watan Janairun 1927, wanda ya yi daidai da watan Muharram 1346 Bayan Hijira A ranar Laraba aka haife shi a a garin Nafada da ke Jihar Gombe a yanzu Kwararre ne a fannin Alkur’ani da Tafsiri da Ma’arifa da Hadisi da Harshen Larabci da Li’irabi da Fikihu Jami’ar Tarayya da ke Lafiya a Jihar Nasarawa ta ba shi Digirin girmamawa Gwamnatin Najeriya ta ba shi lambar girmamawa ta kasa ta OFR Ya musuluntar da dubban mutane Yakan yi saukar Alkur’ani duk bayan kwana biyu Mutane fiye da 140,924 suka haddace Alkur’ani a makarantunsa da ke fadin Najeriya Ya kafa makarantun haddar Alkur’ani sama da 1,500 a Najeriya da wasu kasashen Afirka Karkashin gidauniyasa, an gina dakunan karatu guda 133,060 a Arewacin Najeriya Ya shafe shekaru sama da 50 yana gabatar da tafsirin Alkur’ani a cikin watan Ramadan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu
  • Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi
  • Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da zuri’arsa ta fi kowacce yawan mahaddata Alkur’ani
  • Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa
  • Gwamnan Bauchi ya yi ta’aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa
  • Jihar Jigawa Za Ta Rufe Karbar Kudaden Aikin Hajjin 2026 Ranar 24 Ga Watan Disamba
  • Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran