DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi
Published: 19th, February 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade.
Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma?
NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar HausaShirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikata 240 na karɓar albashi biyu, wasu 217 na amfani da lambar BVN ɗaya a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta gano ma’aikatanta 240 da ke ƙarɓar albashi sau biyu a duk wata, da wasu 217 da ke amfani da lambar tantance asusun banki (BVN) guda ɗaya.
Wani mai magana da yawun gwamnati, Dakta Sulaiman Wali Sani, ya gaya wa manema labarai a ranar Lahadi cewa an gano wannan badaƙalar ce a yayin da ake tantance tsarin biyan albashin gwamnati.
Dr. Sani ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alƙawarin biyan ma’aikata daidai kuma akan lokaci, kuma gano waɗannan matsalolin wani ɓangare ne na gyara al’amura.
Ya ce sun duba bayanan ma’aikata ta hanyar amfani da hotunan yatsa a matakin jiha da ƙananan hukumomi.
“Tsohuwar hanyar biyan mutane tana da matsaloli. Mun gano ma’aikata 240 suna karɓar albashi sau biyu kuma mutane 217 suna amfani da BVN ɗaya, wanda zai iya nufin akwai ma’aikatan bogi ko kuma mutane suna amfani da BVN na wani,” in ji Dakta Sani.
Ya kuma ce ma’aikata 1,335 ba su zo don a tantance su ba a tsawon fiye da watanni shida, wanda ya sa suke tunanin ko waɗannan mutanen da gaske suna aiki da gwamnati.
Alhaji Umar Idi, wanda ya duba biyan kuɗin ƙananan hukumomi, ya ce sun gano sunaye 247 da babu tabbaci a kansu. Waɗannan sun haɗa da mutanen da suka yi ritaya, waɗanda suka mutu, ko kuma waɗanda aka ci gaba da biyan su ba tare da izini ba bayan lokacin barinsu aiki.
“Daga cikin waɗannan ma’aikata 247, takwas ne kawai suka zo don tabbatar da cewa har yanzu suna aiki. Za a goge sauran sunaye 239, wanda zai rage wa gwamnati asarar naira miliyan 27 a duk wata,” in ji shi, yana mai cewa za a mayar da kuɗaɗen da aka samu ga asusun gwamnati.
Dakta Sani ya ce gwamnati ba ta ƙoƙarin hukunta kowa ba, kawai dai tana gyara tsarin ne don ma’aikata na gaske da ’yan fansho su ci gaba da karɓar haƙƙoƙinsu ba tare da wata matsala ko yanka ba bisa ƙa’ida ba.
“Tun lokacin da Gwamna Abba ya fara aiki, ya tabbatar da cewa ana biyan ma’aikatan gwamnati da ’yan fansho a kan lokaci, ba tare da ɓoyayyun cire-cire da aka riƙa yi a baya ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa yanzu da suke tsaftace tsarin biyan kuɗi, ma’aikata su yi tsammanin samun biyan kuɗi mafi inganci a gaba.
Gwamnati ta ce za ta ci gaba da magana da duk masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa an magance duk matsalolin kuma jama’a sun sake amincewa da ayyukan gwamnati.