An yi garkuwa da ɗan uwan Bishop Kukah da wasu 6 a Kaduna
Published: 7th, March 2025 GMT
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da mutane bakwai da suka haɗa da mata da ƙananan yara a ƙauyen Anchuna da ke masarautar Ikulu a ƙaramar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna.
An samu rahoton cewa harin wanda ya auku a daren ranar Larabar, ya jefa al’ummar yankin cikin firgici yayin da maharan suka mamaye ƙauyen da suke da yawa, inda suka yi ta harbe-harbe kafin daga bisani su tafi da su.
Wani mazaunin yankin mai suna Samuel Kukah, ɗan gidan fitaccen malamin kirista, Bishop Hassan Kukah, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa akwai ƙaninsa Ishaya Kukah na cikin waɗanda aka kama.
“Yayana Ishaya, shi kaɗai ne namiji a cikin waɗanda aka sace; sauran mata da yara ne, maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 11 na dare,” in ji shi.
Kukah ya ƙara da cewa har ya zuwa lokacin da yake zantawa da wakilinmu, babu wata tuntuɓa da masu garkuwar suka yi dangane da neman kuɗin fansa.
“Muna yi musu addu’ar Allah ya kare su yayin da muke jiran kowane kira,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don ganin an dawo da waɗanda lamarin ya rutsa da su lafiya, yana mai jaddada cewa galibin waɗanda aka sace mutane ne masu rauni.
Da aka tuntuɓi jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce zai yi wa wakilinmu ƙarin bayani kan lamarin, amma har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai yi ba.
Mazauna yankin na ci gaba da yin kira da a tsaurara matakan tsaro domin daƙile matsalar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
ZAMFARA: APC Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kawo Dauki Don Matsalar Tsaro Na Kara Tsananta
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, ta bayyana matukar damuwarta kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a jihar, inda ta bayyana hakan a matsayin abin ban tsoro da rashin fahimta.
A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar, Yusuf Idris Gusau, jam’iyyar APC ta ce yawaitar ‘yan fashi da makami, garkuwa da mutane da kashe-kashe a Zamfara ya kai matakin da ba a taba ganin irinsa ba, yayin da ta zargi gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Dauda Lawal da nuna halin ko in kula.
A cewar sanarwar, jam’iyyar ta damu matuka da wani faifan bidiyo na baya-bayan nan inda aka ga sama da mutane 200 mazauna Kaura Namoda suna rokon a taimaka musu biyo bayan sace su da wasu da ake zargin ‘yan fashi ne suka yi.
Jam’iyyar APC ta kuma soki gwamnatin kan abin da ta bayyana a matsayin rashin mayar da martani da kuma rashin cika alkawarin da ta dauka na kare rayuka da dukiyoyi a lokacin yakin neman zabe.
Jam’iyyar ta tuna cewa, Gwamna Dauda Lawal ya yi kakkausar suka ga gwamnatocin baya kan rashin tsaro, ya kuma yi alkawarin kawo karshen ‘yan fashi a cikin watanni biyun farko na mulki.
Sai dai jam’iyyar APC ta bayyana cewa a maimakon haka lamarin ya tabarbare, inda a kullum ake ta yin garkuwa da mutane da kashe-kashe a sassan jihar.
Sanarwar ta kuma bayyana wasu muhimman hanyoyi da suka hada da Gusau –Talata Mafara –Tureta, da Mayanchi –Anka –Gummi – wadanda a yanzu suke da hatsarin tafiya ba tare da rakiyar sojoji ba.
Jam’iyyar ta kara da cewa, hanyar Gusau zuwa Kaura Namoda ta zama daya daga cikin mafi hadari, inda a kullum ake samun rahotannin sace-sacen mutane da kashe-kashe.
Da take ba da misalin harin baya-bayan nan da aka ce an kashe mutane 38 da aka yi garkuwa da su daga unguwar Banga da ke karamar hukumar Kaura Namoda bayan an biya kudin fansa, jam’iyyar APC ta ce gwamnatin jihar ta yi shiru duk da cewa ana ci gaba da samun tashin hankali a tsakanin mazauna yankin.
A yayin da wasu sabbin rahotanni suka ce an sace sama da mutane 200 a cikin makon nan, jam’iyyar APC ta sake yin kira ga gwamnatin tarayya da ta kafa dokar ta-baci a Zamfara domin ba da damar aikewa da karin sojoji da kuma aiwatar da sahihin matakan tsaro.
Jam’iyyar ta zargi gwamnatin jihar da gazawa yadda ya kamata ga hukumomin tsaro na tarayya tare da zargin gwamnan da wasu mataimakansa kan harkokin yada labarai sun fito fili suna sukar ayyukan sojoji a jihar.
“Haka zalika ta yi Allah-wadai da rufe kasuwanni da hana zirga-zirgar ababen hawa, inda ta bayyana su a matsayin matakan da ba su da inganci da suka yi illa ga tattalin arzikin jihar.
Jam’iyyar APC ta kuma yi kakkausar suka kan tafiye-tafiyen da Gwamna Lawal ya yi a kasashen waje, inda ta yi zargin cewa yana halartar bukukuwan ‘yan uwa na kashin kansa yayin da mazauna gida ke kokawa da rashin tsaro.
Jam’iyyar ta yabawa bangaren Majalisar Dokokin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Bashar Aliyu Gummi bisa jajircewar da ta yi wajen ganin ta yi wa bangaren zartarwa hukunci kan al’amuran da suka shafi rashin tsaro da cin hanci da rashawa.
A karshe jam’iyyar APC ta jajantawa iyalan wadanda rikicin ya shafa tare da yin addu’ar Allah ya dawo mana da zaman lafiya a jihar Zamfara da Najeriya baki daya.
REL/AMINU DALHATU