Aminiya:
2025-08-10@11:13:18 GMT

Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino

Published: 26th, February 2025 GMT

Samar da dabino zai samu sauyi mai mahimmanci a Jihar Jigawa bayan da wani kamfani daga kasar Saudiyya mai samar da dabino da gwamnatin jihar suka ƙulla yarjejeniya domin ƙara yawan amfanin gona.

Ta wannan haɗin gwiwa za a kawo sababbin fasahohin zamani da irin dabino masu yawa don shigar da su cikin tsarin noma.

Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin Akpabio Ƙungiya ta rage farashin kayan marmari saboda Azumin Ramadan

A cewar bayanai daga Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), Saudiyya ita ce ƙasa ta biyu mafi girma wajen samar da dabino na duniya, inda take samar da tan miliyan 1.61 na dabino.

Masar ita ce ƙasa mafi girma wajen samar da dabino, inda ta noma tan miliyan 1.73 na dabino a shekarar 2022, yayin da Aljeriya ke matsayi na uku da tan miliyan 1.25.

Haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Jigawa da wannan rukunin daga Saudiyya tare da Netay Agro-Tech, wani kamfanin amfani da ke Nijeriya ma gudanar da harkokin noma, zai kawo karuwar samuwar dabino a jihar.

Kasar Nijeriya na samar da kusan tan 21,000 na dabino a kowace shekara, inda Jihar Jigawa ke cikin jihohi mafi girma wajen samar da dabino.

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, yayin da yake jawabi lokacin da ya karɓi wata tawaga daga babban kamfanin noma na Saudiyya, wanda ya ƙware wajen shuka dabino da sarrafa gonaki a ofishinsa da ke Dutse, ya ce wannan haɗin gwiwa zai kawo sabon salo ga samar da dabino a Jigawa.

Gwamnan ya bayyana goyon bayan gwamnatinsa ga wannan yunƙuri, yana mai cewa ya dace da ajandar bunkasa aikin gona ta jihar.

“Mun yi maraba da zuwanku Jihar Jigawa tare da nuna godiya ga sha’awar da kuka nuna wajen yin aiki tare da mu.

“A matsayinmu na gwamnati, mun jajirce kan wannan haɗin gwiwa saboda zai amfani al’ummarmu sosai.

“Zuwanku da sha’awar yin haɗin gwiwa da mu wajen kafa gonakin dabino a fadin jihar, da kuma inganta samar da alkama, sun yi daidai da burinmu na bunkasa aikin noma,” in ji gwamnan.

Ya sake jaddada shirinsa na samar da dukkan kayan aiki da ake bukata don tabbatar da nasarar aiwatar da wannan shiri.

Ya bayyana kwarin gwiwa cewa, haɗin gwiwar zai samar da fa’idodi masu ban mamaki tare da mayar da Jigawa ta zama jagora a masana’antar dabino ta duniya.

Shugaban tawagar, Abdul’aziz Abdurrahman-Al-Awf ya jaddada ƙudurinsu na kawo fasahohin noma na zamani zuwa Jihar Jigawa.

“Muna son tabbatar da samar da dabino a duk shekara, ba wai kawai a wasu yanayi ba, kuma haɗin gwiwarmu zai haɗa da horar da manoma da ba wa matasa dama,” in ji shi.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Jigawa Saudiyya samar da dabino Jihar Jigawa haɗin gwiwa

এছাড়াও পড়ুন:

Nijeriya Da Indiya Za Su Haɗa Kai Wajen Yaƙi Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi

Hukumar NDLEA ta Nijeriya da takwararta ta Indiya sun amince da yin aiki tare domin daƙile safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin ƙasashen biyu. Wannan yarjejeniya ta fito ne daga wata tattaunawa ta kafar intanet tsakanin Shugaban NDLEA na Nijeriya, Janar Buba Marwa (mai ritaya), da shugaban hukumar ta Indiya, Anurag Garg.

Shugabannin sun jaddada buƙatar haɗin gwuiwa, musamman wajen hana shigo da haramtattun magunguna daga Indiya zuwa Nijeriya. Marwa ya ce akwai buƙatar a ƙarfafa wannan dangantaka bisa yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu a shekarar 2023.

Bayan Shekaru 7 Yana Ɓoye, NDLEA Ta Cafke Babban Dillalin Ƙwayoyi NDLEA Ta Kai Samame Fitattun Wuraren Shaye-shaye, Ta Cafke Mutane 19 A Kano

Buba Marwa ya roƙi hukumar Indiya da ta tallafa wa NDLEA ta hanyar bai wa jami’anta horo na musamman domin inganta dabarunsu wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi.

Nijeriya na daga cikin ƙasashen da ke fama da matsalar shaye-shaye da safarar miyagun ƙwayoyi, wanda hakan ya sa aka kafa NDLEA domin daƙile wannan barazana ga lafiyar jama’a da zaman lafiya a ƙasar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Kwara Ta Yi Gargadi Ga Manoman Ruwan Malka Na Wata Agusta
  • Abubuwan Da Suka Ja Hankalin Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Tsarin Noman Waken Soya
  • Gwamnatin Jigawa Ta Raba Katin Duba Sakamakon Jarabawa Kyauta Ga Ɗalibai
  • Sai An Magance Matsalar Asusun Haɗin Gwiwa, Za A Tabbatar Da Cin Gashin Kan Ƙananan Hukumomi
  • Gwamnatin Tarayya da Ofishin Jakadancin Amurka Sun Haɗa Gwiwa Don Wayar Da Kan ‘Yan Nijeriya Kan Sababbin Ƙa’idojin Samun Biza
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Mayar Da Dalibai 184 Da Suka Zo Hutu Daga Cyprus
  • Sai Ƴan Siyasa Sun Haɗa Kansu Sannan Za Su Iya Tunkarar APC A 2027 – Lukman
  • Nijeriya Na Asarar Tiriliyan 3.2 Sanadiyyar Watsi Da Noma A Gandun Daji
  • Gwamnatin Kwara Ta Horar Da Manoma Sama Da 500 Tare Da Basu Tallafi
  • Nijeriya Da Indiya Za Su Haɗa Kai Wajen Yaƙi Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi