An Fara Binciken Badaƙalar Haɗa NIN-SIM Ba Bisa Ƙa’ida Ba
Published: 7th, February 2025 GMT
Majalisar wakilai ta umarci kwamitocin sadarwa da harkokin cikin gida da su binciki haɗa lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) da layukan waya ba tare da izini ba da kamfanonin sadarwa ke yi.
Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da ‘yan majalisa Patrick Umoh da Julius Ihonvbere suka gabatar, inda aka buƙaci hukumar NCC ta ɗauki mataki kan duk wani kamfanin sadarwa da aka samu da laifi, tare da NIMC ta tabbatar da sahihancin haɗa bayanan NIN.
Umoh ya ce wannan mataki na iya haifar da damuwa ga ‘yan ƙasa, tare da jefa su cikin hatsarin satar bayanai, da damfara, da wasu laifukan intanet. Kwamitin binciken na da makonni huɗu domin kammala aikinsa.
এছাড়াও পড়ুন:
MDD ta yi gargadin cewa jarirai 14,000 a Gaza kan iya mutuwa idan an ci gaba da killace Zirin
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa jarirai dubu 14 a Gaza kan iya rasa rayukansu muddin Irsa’ila ta ci gaba da killace Zirin da hana shigar da kayan agaji.
Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher na maida martini ne kan matakin gwmanatin Isra’ila na kyale manyan motoci hudu na agaji su shiga Gaza inda ya ce wannan tamkar”digo ne a cikin teku.”
“Akwai jarirai 14,000 da za su mutu a cikin sa’o’i masu zuwa idan ba za mu iya kaiwa gare su ba inji shi.
Ya ce motocin agajin da ke dauke da kayan abinci na jarirai da abinci mai gina jiki, suna cikin Gaza amma ba su kai ga farar hula ba saboda gwamnatin Isra’ila ba ta yarda da hakan ba.
Halin jin kai a Gaza ya ta’azzara sosai tun daga ranar 18 ga Maris saboda yadda gwamnatin Isra’ila ta takaita shigar abinci, man fetur, magunguna, da ruwa cikin Zirin na Gaza.
A cewar hukumar Integrated Food Security Phase Classification (IPC), kusan yara 71,000 ‘yan kasa da shekaru biyar suna fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki.