HausaTv:
2025-11-28@06:24:14 GMT

Tarayyar Afirka ta yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a Guinea-Bissau

Published: 28th, November 2025 GMT

Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahmoud Ali Youssouf, ya yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Guinea-Bissau a ranar Alhamis, inda ya yi kira da a gaggauta sakin hambararren shugaban kasar Umaro Sissoco Embaló da sauran jami’an da ake tsare da su.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta sake nanata cewa kungiyar Tarayyar Afirka ba za ta amince da duk wani sauyi na gwamnati da ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar ba.

Ya jaddada muhimmancin mutunta tsarin zabe da ake gudanarwa da kuma tabbatar da tsarin mulkin kasar, kamar yadda hukumar zabe ta kasar ta tanada.

Youssouf ya yi kira ga dukkan bangarorin da su yi taka tsantsan don hana ci gaba da tabarbarewar lamarin, yana mai jaddada shirin kungiyar na yin aiki kafada da kafada da ECOWAS da abokan huldar kasa da kasa don maido da kwanciyar hankali da kiyaye tsarin dimokuradiyya a Guinea-Bissau.

Tarayyar Afirka ta tabbatar da goyon baya da hadin kai ga al’ummar Guinea-Bissau kan hanyar samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da tabbatar da mulkin dimokuradiyya.

Kasashe da kungiyoyi da hukumomi da dama sun yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a kasar Guinea Bissau da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya, da Portugal, da Ghana, da Najeriya, da shugabannin hukumar zabe da dai sauransu, inda suka yi kira da a gaggauta maido da tsarin mulkin kasar Guinea-Bissau, mutunta tsarin dimokuradiyya da warware duk wasu korafe-korafe na zabe ta hanyar lumana, gaskiya, kuma bin doka da oda.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya : Ana ci gaba da alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi November 27, 2025 Iran ta yi tir da Australiya kan alakanta IRGC, da mai tallafawa ta’addanci November 27, 2025 Ramaphosa ya soki Trump kan hana shi halartar taron G20 na badi November 27, 2025 ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau November 27, 2025 Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci November 27, 2025 Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon  Dake Takawa Makiya Birki November 27, 2025 Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa November 27, 2025 An Zabi Iran A Cikin Majalisar Zartarwa Ta Hukumar Yaki Da Makamai Masu Guba Ta Duniya CWC November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: yi Allah wadai da juyin Tarayyar Afirka

এছাড়াও পড়ুন:

EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi

Taron koli karo na 7 na tarrayar Turai da tarayyar Afrika, wanda aka bude a Luanda, na maida hankali kan batun diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi a karon farko.  

A cewar ajandar taron, daya daga cikin manyan jigogi zai mayar da hankali kan diyya ta kudi da siyasa da ta shafi zaluncin mulkin mallaka da cinikin bayi, gami da lalacewar tattalin arziki, da al’adu da aka tara tsawon shekaru da dama.

Wannan lokaci ne da ba a taba ganin irinsa ba a wannan matakin siyasa: ba a taba sanya irin wannan batu a cikin ajandar taron da ya hada shugabannin kasashen Turai da Afirka ba.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta ware shekarar 2025 a matsayin shekarar “Adalci ga ‘Yan Afirka da kuma Mutanen da suka fito daga zuriyar Afirka ta hanyar diyya.

A cewar AllAfrica, kawai shigar da batun a cikin ajandar ya zama babban ci gaba, domin manyan biranen Turai sun dade suna guje wa batun.

Baya ga batun diyya, taron kolin ya yi magana kan batutuwa daban-daban: ci gaba mai dorewa, zuba jari, gyare-gyare ga tsarin kuɗi na duniya, rage raunin bashi, kirkire-kirkire, tsaro, da yanayi.

Kusan shugabanni 80 ne ke halartar taron, wanda João Lourenço, Shugaban Angola kuma Shugaban Tarayyar Afirka na yanzu, da António Costa, Shugaban Majalisar Turai, tare da Ursula von der Leyen suke jagoranta.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Talabijin ta Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru  Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin November 25, 2025 An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau
  • An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji
  • Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau
  • Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa
  • An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
  • Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
  • Sojojin Sun Sanar Da Kwace Mulki A Kasar  Guinea Bissau
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
  • EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi