Ƙasar Japan ta fara sayar da injin da ke yi wa mutane wanka
Published: 28th, November 2025 GMT
An fara sayar da wani inji da ke yi wa mutum wanka bayan ya burge baƙi a lokacin bajekolin duniya a Japan, in ji wata mai magana da yawun kamfanin da ya ƙera injin, a ranar Juma’a.
Masu amfani za su kwanta su rufe kansu a cikin injin da wani murfi, sannan ya wanke su kamar yadda ake wanke kaya a injin wanki, amma ba tare da ya jujjuya su ba, yayin da kiɗa ke tashi a ciki.
An gabatar da samfurin na’urar, mai suna “injin wankin ɗan adam”, kuma an sami dogayen layuka a baje kolin watanni shida da aka kammala a Osaka a watan Oktoba bayan ya sami halartar fiye da mutum miliyan 27.
Kamfanin Japan mai suna Science ne ya ƙera shi, kuma wannan na’urar sabuwa ce a kan irin ta da aka nuna a Osaka, a shekarar 1970.
“Injiniyanmu shugaban kamfani ya samu wahayi daga wannan tun yana ƙaramin yaro mai shekaru 10 a lokacin,” in ji mai magana da yawun Science, Sachiko Maekura, ga AFP.
Na’urar “ba wai tana wanke jiki kaɗai ba, har ma da ruhinka,” in ji ta, tare da lura da bugun zuciya da sauran muhimman alamomin lafiyar masu anfani da shi.
Bayan wani kamfanin shakatawa daga Amurka ya tuntubi Science don ganin ko za a shigar da samfurin fasahar kasuwa, sai kamfanin ya yanke shawarar samar da shi a zahiri.
Wani otal a Osaka ya sayi na’urar ta farko kuma yana shirin fara amfani da ita ga baƙin otal ɗin, in ji mai magana da yawun kamfanin.
Sauran abokan cinikin na’urar sun haɗa da Yamada Denki, babban kamfanin dillancin kayan lantarki a Japan, wanda ke fatan na’urar za ta jawo mutane zuwa shagunan su, in ji ta.
“Saboda wani bangare na jan hankalin wannan na’ura shi ne ƙarancinta, muna shirin samar da kusan guda 50 ne kawai,” in ji Maekura.
Jaridun ƙasar ta Japan sun rawaito cewa farashin siyarwa zai kasance yen miliyan 60, kwatankwacin sama da Naira miliyan 500.
AFP
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Injin wanka
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila Na Barazanar Sake Shiga Wani Sabon Yaki Da Kasar Lebanon
Ministan yakin Isra’ila ya yi barazanar kai wa kasar Lebanon hari gadan-gadan, inda ya bukaci kungiyar Hizbullah ta kwace damarar makamai.
Ministan yakin Isra’ila, Isra’ila Katz, ya yi gargadin cewa Tel Aviv a shirye take ta kaddamar da wani sabon yaki kan kasar Labanon matukar kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta ki mika makamanta zuwa karshen shekarar 2025.
Da yake jawabi ga Knesset na Isra’ila, Katz ya yi ikirarin cewa Washington ta ba Beirut wa’adin kwance damarar Hezbollah zuwa karshen shekara, amma ya ce ba ya tsammanin kungiyar za ta mika makamanta.
“Ban yi imani cewa Hizbullah za ta mika makamanta bisa radin kanta ba,” kamar yadda ya shaida wa ‘yan majalisar. “Idan Hezbollah ba ta yi watsi da makamanta a karshen shekara ba, za mu sake yin aiki da karfi a Lebanon, za mu kwance damarar su.”in ji shi.
Katz ya kara da cewa gwamnatin Isra’ila ba za ta lamunci abin da ya kira barazana ga matsugunan da ke kan iyakar Lebanon ba.
“Ba za mu yarda da duk wata barazana ga mazauna arewa ba, kuma za a ci gaba da aiwatar da doka har ma da kara yin amfani da karfi.”
A halin da ake ciki dai Washington na matsawa kasar Lebanon lamba kan ta tilastawa kungiyar Hizbullah ta kwace damarar makamai, ko da kuwa hakan yana tattare da hadarin fadawar kasar a cikin yakin basasa, kuma ta fito fili ta goyi bayan barazanar da Isra’ila ke yi, tana mai gargadin cewa Lebanon na fuskantar wani babban hari idan har Hizbullah ba ta mika makamanta ba.
A yayin da yake mayar da martani game da batun da ake yi, dan majalisar dokokin Lebanon Hassan Fadlallah ya jaddada cewa, babu inda za a yi wata tattaunawa ta siyasa da Isra’ila yayin da take ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Fadlallah ya ce, har yanzu ba a gabatar da wata shawara ta siyasa ga kasar Labanon da za ta iya dakatar da kai hare-haren ‘yan mamaya yadda ya kamata ba, yana mai yin Allah wadai da tsoma bakin kasashen yammacin duniya da kuma Amurka suke yi a cikin harkokin cikin gidan kasar ta Lebanon.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Petro: Man fetur shine burin Amurka a Venezuela ba yaki da fataucin kwayoyi ba November 28, 2025 Tarayyar Afirka ta yi Allah wadai da juyin mulkin a Guinea-Bissau November 28, 2025 Najeriya : Ana ci gaba da alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi November 27, 2025 Iran ta yi tir da Australiya kan alakanta IRGC, da mai tallafawa ta’addanci November 27, 2025 Ramaphosa ya soki Trump kan hana shi halartar taron G20 na badi November 27, 2025 ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau November 27, 2025 Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci November 27, 2025 Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon Dake Takawa Makiya Birki November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci