Aminiya:
2025-11-02@00:52:58 GMT

Arewa na buƙatar haɗa kai da Kudu don ceto Najeriya — El-Rufai

Published: 24th, February 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027.

El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark.

Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa

A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa.

“A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai.

“Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa domin tana buƙatar ceton gaggawa. Dole ne mu ɗauki matakin ceton ƙasar nan.”

Maganganunsa sun zo ne yayin da ake raɗe-raɗin cewa yana shirin sauya sheƙa daga jam’iyyar APC.

A makonnin da suka gabata, ya gana da ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa bayan wani saɓani tsakaninsa da jam’iyyar APC mai mulki da kuma gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

El-Rufai, wanda ya je ziyarar ta’aziyyar tare da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yaba da rawar da Atiku ya taka wajen kawo sauye-sauyen tattalin arziƙi a lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo.

Segun Showunmi, tsohon mai magana da yawun yaƙin neman zaɓen Atiku, ya tabbatar da cewa wannan ganawar tana cikin shirye-shiryen siyasa gabanin zaɓen 2027.

A watan Janairu, El-Rufai ya gana da Hamza Al-Mustapha, tsohon hadimin marigayi Janar Sani Abacha, da Shehu Gabam, shugaban jam’iyyar SDP, da wasu ’yan siyasa a Abuja.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Arewa Edwin Clark Haɗin Kai rasuwa Siyasa ta aziyya

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace A Taraba

Ana zargin mutumin da hannu wajen sace Alhaji Adamu.

Wanda ake zargin ya samu raunuka bayan jama’a sun yi masa duka kafin isowar sojoji, kuma an garzaya da shi asibiti, yayin da ake ci gaba da bincike.

Brigedi Janar Kingsley Chidiebere Uwa, kwamandan Rundunar 6, ya yaba da yadda sojoji, ‘yan sa-kai da mafarauta suka haɗa kai, yana mai cewa wannan haɗin kai ya taimaka wajen samun nasarar ceto wanda aka sace.

Ya kuma buƙaci jama’ar Taraba su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai da wuri domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisar Dokokin Kano Ta Ce An Yi Rashin Adalci Wajen Ɗaukar Aikin Kwastam A Nijeriya October 30, 2025 Manyan Labarai Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II October 30, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Sauya Sunayen Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa October 30, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 
  • Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani
  • Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?
  • Dan Majalisar Jema’a/Sanga, Daniel Amos, Ya Koma Jam’iyyar APC
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari
  • Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano Spalleti
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara 
  • Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC
  • Sojoji Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace A Taraba
  • Majalisa ta amince Tinubu ya karɓo rancen dala biliyan 2.35