Palasdinu: Kwamandoji Biyu Na Rundunar “Sarayal-Quds” Sun Yi Shahada A Yammacin Kogin Jordan
Published: 28th, November 2025 GMT
Rundunar “Sarayal-Quds” ta kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da shahadar mayakanta biyu a yammacin kogin Jordan sanadiyyar harin da sojojin mamaya na Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai.
Daya daga cikin shahidan shi ne Yusuf Ali Asa-Asa, dan shekaru 37, da kuma Mahmud Abdullah dan shekaru 26, sun kuma yi shahadar ne a jiya Alhamis.
Sanarwar ta kuma ce,an yi batakashi a tsakanin shahidan biyu da kuma ‘yan mamaya gabanin su kwanta dama a unguwar Abu Dhahir dake Jenin a yammacin Kogin Jordan.
Wasu rahotanni daga yankin da lamarin ya faru sun ce, sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila sun kutsa cikin unguwar tare da shiga cikin wani gidan sannan kuma su ka kama wani saurayi Bapalasdine daya. Gabanin su yi awon gaba da shi su jikkata shi ta hanyar dukansa.
Daga lokacin da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta shelanta yaki akan Gaza, take kuma kai wa yankin yammacin Kogin Jordan dake karkashin gwamnatin kwarya-kwaryar Palasdinu hare-hare. A lokaci daya kuma yahudawa ‘yan share wuri zauna suna kai wa gonaki da dukiyar Falasdinawa hare-hare da kona su, da kuma kashe Falasdinawa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi Ta Soki Shirin Donald Trump Na Bayyanata A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda November 28, 2025 Kasashen Qatar Da Jordan Sun Yi Allawadai Da Harin “Isra’ila” A Kasar Syria November 28, 2025 Senegal: Hambararren Shugaban Kasar Guinea Bissau Ya Isa Kasar Senegal November 28, 2025 Limamin Tehran: Hadin Kai Ne Sakamakon Imani Da Ayyukan Kwarai Ne November 28, 2025 Yamen Ta Soki Kasashen Birtaniya Da Amurka Da Tsoma Baki Kan harkokin Kasarta November 28, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 10 A Wani Hari Da Ta Kai A Birinin Damaskas Na Kasar Siriya November 28, 2025 Jagoran : Amurka Tasha Kashi A Yakin Kwanaki 12 Duk Da Manyan Makamai Na Zaman Da Take Da Su. November 28, 2025 Ministocin Tarayyar Turai Sun yi Tir Da Karuwar Hare –Haren Da Yahudawa Ke Kai wa Falasdinawa November 28, 2025 An Rantsar Da Sabon Shugaban Mulkin Soja Na kasar Guinea-Bissau November 28, 2025 Isra’ila Na Barazanar Sake Shiga Wani Sabon Yaki Da Kasar Lebanon November 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza
Rahotanni sun bayyana cewa kididdigar da ma’aikatar harkokin wajen yankin falasdinu ta fitar ya nuna cewa sojojin Isra’ila sun kashe akalla yan mata 33000 a ci gaba da yakin kare dangi da take yi kan alummar Gaza.
Ma’aikatar fa fitar da wannan sanarwar ce a wajen taron ranar kawo karshen hare-hare kan mata ta duniya . kuma tayi kaca-kaca da gwamnatin sahayuniya game da irin muggan laifukan yaki da ta tafka, inda ta rika amfani da makamai na zamani kan alummar falasdinu
Kididdigar ta nuna cewa sama da mata 12500 da kuma yara 20,000 ne Isra’ila ta kashe a harin da ta kai tun daga watan oktoban shekara ta 2023.
Har ila yau ma’aikatar ta bayyana cewa lallai a kwai bukatar a dauki matakin gaggawa na matsin lamba domin kawo karshen ci gaba da mamaye yankunan falasdinawa da HKI ke yi, kuma tayi aiki da kudurin kafa kasashe guda biyu da zai bada garanti wajen kafa kasar falasdinu..
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu. November 26, 2025 Aljeriya Tayi Kira Da A Dakatar Da Israila Game Da Hare-haren Da Take Kaiwa November 26, 2025 Sojojin Sun Sanar Da Kwace Mulki A Kasar Guinea Bissau November 26, 2025 Larijani Iran Tana Maraba Da Tattaunawa Ta Gaskiya Amma Ba Tsararren Sakamako Ba November 26, 2025 November 26, 2025 Isra’ila Tana Ci Gaba Da Rushe Gidaje A Yankin Gaza November 26, 2025 Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe November 26, 2025 Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta November 26, 2025 Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki November 26, 2025 Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin November 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci